← Book details Imaan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 142 OF 292

Sashe 142

Imaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sunkuyar da kai tace "Toh ke baxa ki ma yayan naki fatan xaman lafiya da matarsa ba Imaan" Shi dai Mujaheed bai tsaya ba har ya fita, bin sa da kallo imaan tayi sai kuma ta mike ta bi bayansa da sauri, Maryam ta xaro ido tana kallon Inna tace "Wai kuka fa take yi..." Inna ta kara rushewa da kuka tace "Ka ji ki da wata magana, baxa ta yi kuka ba?? ke kinsan wahalan da Mujaheed yyi da ita tun tana tsumma, ke kinsan irin fadi tashin da yayi a kanta tana karama, to ko ubanta bai yi wahalar da Mujaheed yyi a kanta ba, kullum a makale da shi xa ki ganta duk ta takura bawan Allahn duk inda xa shi tana hannunsa, tayi ta basa wahala, har goyata ya sha yi, ta xo ta fara ciwace ciwacen da ba a san kansa ba nan ma babu irin wahalan da bai yi da ita na ganin ya nema mata lafiya ba, ai shakuwar dake tsakaninsu ko d'a da uwa sai haka, kuma kice baxata yi kuka ba yau xa su rabu na har abada" tana kai wa nan ta fashe da matsanancin kuka ta xamo daga kan kujera tayi xaman dirshan a kasa, Maryam dai sai dariya take kasa kasa. Imaan na fita parlon Inna taga har yayi nisa, ta bi bayansa da sauri tace "Yaya" tsayawa yayi ya juya yana kallonta, Bata san lokacin da ta fashe da kuka ba ta nufesa da gudu ta rungume sa cikin rawar murya tace "Xan yi missing din ka Yaya" kasa cewa komai yayi, lkci daya idonsa ya canxa launi, rungume ta yyi shi ma yyi ya lumshe ido, kuka ta dinga yi a kirjinsa, cike da karfin hali yace "Ae xa ki dinga xuwa gidana in sha Allah..." Ta gyada masa kai kawai hawaye na sauka idonta, cikin sanyin murya tace "Kayi hakuri da abinda nayi daxu, ban san it's wrong ba I wouldn't have done that, kayi hakuri plss...." A hankali yace "Na hakura" gently ya janyeta jikinsa ganin hawaye take har sannan yace "Toh ya isa haka mu je ki rakani gun mota" Bata iya ta ce komai ba ya kama hannunta suka nufi gate. Tafiya kawai suke kamar ba su son tafiyar har suka fita gate din gidan, suna isa motarsa ya juya yana kallonta har idanuwanta sun yi jajir, sunkuyar da kanta tayi a hankali tace "Sai da safe, I am wishing you a happy married life...." Yayi murmushin karfin hali yace "Thanks imaan" Juyawa tayi ta fara tafiya yace "Imaan" ta tsaya sannan ta juyo jin bai ce komai ba ta dawo inda yake tana kallonsa, yace "Shiga mu je xan siyo ma Inna abu ki kawo mata ynxu" a hankali tace "Toh" sannan ta xaga ta bude front seat ta shiga, ya shiga driver seat ya tada motar, the journey was silent har suka iso gun masu gashin kaji, yayi parking ya kashe motar, ya sauka, ba a dau lkci sosai ba ya dawo rike da leda uku na kaji da fresh milk, ya bude back seat ya ajiye leda guda sannan ya bude side dinta ya mika mata leda biyu ta amsa ya xaga ya shiga driver seat, gida ya koma bayan yyi parking ya juya yana kallonta yace "Sai da safe" ta sauke idonta kasa tace "Allah ya kai mu..." Yace "Ameen, ki dau daya sai ki kai ma Inna daya" D'an murmushi tayi ta bude motar ta fita, ta nufi gate ya bi ta da kallo har ta shiga sannan yayi reverse ya bar layin. Washegari asabar tun da wayewar gari Ammi da Aunty, Mama Hansai da matan kawu Bala suka dinga aiki a gidan trying to make sure everywhere was neat, masu kujeru dama su ma sun xo sun dau kayansu, su Maimoon, Ummi da Maryam kadai ke taya su aikin, Imaan kuwa na kwance dakinta wai kai na ciwo, Rahma dama tare da ita Umma ta bar gidan da yammacin jiya.... Bayan azahar Imaan na part din Inna tare da Maryam, Inna na kan darduma tana bada labarin nan dai na irin yanda aka haifi Mujaheed tana tsaye bakin kofar asibiti tun safe har dare, wahalan da tayi da shi tun yana tsumma, yanda ya girma a wajenta da fadan da yasa ta dinga yi da jama'ah a anguwa, har lkcn da ya tafi kasar waje karatu.... Imaan dai na kwance sai game take a wayarta tana tabe baki don ita dai har ta haddace labarin nan layi layi, Maryam sai dariya take ita da ba a ta6a ba ma labarin ba, Inna na matsar kwalla tace "Har xuwa jiya da aka daura masa aure, Allah sarki Mujaheed dina" Dariya kawai Maryam take har da kwanciya, Inna dai sai matsar kwalla take tace "Duk cikin 'ya yan Ahmadu babu ya shi, gashi duk ya fi su kyau wllh, ga tsafta ga mutunta na gaba da shi, sam Mujaheed bai san wani abu wai rashin kunya ba, bai taba mayar min da magana ba, wllh jiya ban yi baccin kirki ba da tunaninsa na kwana..." Sai kuma ta fashe da kuka sosai, sai a sannan Imaan tayi murmushi bata dai ce komai ba, cikin rawar murya Inna tace "Da dakunan bangaren nan nawa sun kai uku sai in ce su dawo nan da matar kawai ni dai in dinga ganin sa kullum" Maryam dai sai dariya take, Imaan ta mike ta wuce daki ta dalilin kiranta da ake a waya, Daga kiran tayi ta xauna gefen gado ta kai kunne hade da yin sallama, ya amsa yace "How are you dear?" Tace "Alhmdllh" yace "Hope kin ji sauki sosai" tana murmushi tace "Sure, sosai" yace "Ohk to ki dan fito ki amshi sako" ta xaro ido tace "Na me?" A hankali yace "C'mon dear" tana murmushi tace "Toh bari in fito" daga haka ta katse wayar ta fito parlor tana kallon Maryam tace "Mu je ki rakani" Inna na goge hawayen idonta tace "Ina??" Imaan ta turo baki tace "Ae yanxu xa mu dawo" Inna ta marairaice tace "Tou ni dai kar ku dade, mai tayani xaman gashi yayi aure ya tafi..." Dariya imaan tayi ta fita Maryam ta bi bayanta, har suka isa gate Maryam tambayarta inda xa su take yi amma ta ki gaya mata, suna fita gate din Maryam tayi shiru ganin Sadeeq tsaye kusa da motarsa, murmushi yayi ganinsu, Maryam tace "Hi...." Yace "Hello Maryam" tana murmushi tace "Happy Belated birthday Sadeeq" yace "Thanks much... Hope an gama biki lafiya?" Tace "alhmdllh" yace "Maa Sha Allah, Allah ya basu xaman lafiya" Maryam tace "Ameen" kallon Imaan da ta jingina da motar ta rungume hannu yayi a hankali yace "Hello princess..." Ta d'an yi murmushi tace "Ya gida" yace "Alhmdllh, ya Kaka?" Imaan ta langwabar da kai tace "tana ciki tana ta missing ya Mujaheed" Yace "Allah sarki, ta kwantar da hankalinta after a month sai ta koma gidan gaba daya koh" Yar dariya kawai imaan tayi tace "Gaskiya ne" yyi murmushi ya bude back seat ya fiddo da wani kwali dake a rufe amma ko bai fadi meye a ciki ba kowa ya sani, yana kallonta yace "Here..." Ta xaro ido tace "Haba wannan ai yayi yawa" yace "Ni ma sun min yawa, take plss baby" Imaan tayi murmushi ta d'an risina ta amsa tace "Toh Allah saka da alkhairi" hararanta yyi tayi dariya bata ce komai ba, wani box mai kyau ya fiddo ya mika mata ta make kafada tace "Bana so" hade rai yayi ya kalli Maryam dake murmushi yace "Kin ganta koh?" Maryam tayi dariya ta mika masa hannunta tace "Bani in rike mata" Mika ma Maryam box din yyi, Maryam tace "Allah ya saka da alkhairi" Yana murmushi yace "And ban mance promise da na maki ba, kin bar min xabi or you want anything?" Yar dariya Maryam tayi tace "Ehh na bar maka" yace "Toh shikenan, thank you" Kallon imaan yayi yace "Dear, we will talk later ki gaida kaka" Imaan tace "Toh xata ji nagode" Sallama yayi ma Maryam ma suka nufi gate, ya bude maxaunin driver ya shiga ya tada motar, suna shiga gida Maryam ta kashe ma imaan ido tace "Yau xa mu ci cake mu yi dam, amma me xa ki ce ma Ammi?" Imaan ta xaro ido tace "Part din Inna xan kai ai" Maryam tace "That will save u long explanation" Washegari Sunday tun da sassafe Inna ta gama shiryawa wai xa su gidan Mujaheed da Imaan, Daddy dake parlor xaune yana kallon news yace "Toh ai kila ma basu tashi ba da sassafe xa ki je masu Inna" Inna ta xaro ido tace "Sai kace rubabbu Bukar kace min basu tashi ba, Toh ni dai gaskiya na shirya kuma yanxu xan tafi ina imaan din?" Daddy yace "Bata tashi ba" Inna ta xauna saman kujera tayi tagumi tace "Naga abinda ya isheni.... baccin safe ko baccin asara ni Asabe, karfe takwas ace mutum mai rai bai tashi yyi wanka ya kintsa ya karya ya gyara gidansa ba? Kuma tun jiya nace mata ta shirya da safe xa mu tafi tare tunda wannan yarinya Maryam dangin ubanta sun xo sun tafi da ita jiya da magariba... Kai ku dai baku da tsari gaskiya... Meye kuma baccin safe??" Shi dai Daddy bai ce komai ba, Ammi ta fito daga kitchen ta gaida Inna sannan ta tafi dakin Imaan ta tasheta... Inna na ta xaune parlor ta tsuke fuska har imaan ta fito bayan kusan minti talatin cikin atamfa riga da skirt na biki da aka masu bata sa ba, sosai kayan suka amsheta, Inna tace "Ki dauko mayafi mu tafi idan munje can kya karya gaskiya...." Ammi da Daddy suka kalleta, can Ammi tace "A'a inna da dai ta karya ai bata da 6ata lkci wajen cin abinci, ta je gidan mutane da sassafe...." A fusace Inna tace "Ke dai Aisha ki daina haka, ki dinga jin tsoron Allah, Gidan Mujaheed din ne gidan mutane idan ba walakanci ba, gidan Mujaheed ne fa, ni dai ku dinga tsoron Allah sai kace wanda xata gidan 6are? Ke dauko hijabinki mu tafi, shi gidan yayan nata xaki ce ma gidan mutane saboda baki da mutunci..." Tana
Chapter 142 · 0% Book details