Sashe 272
Imaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A fusace inna tace "Ni dai duk wanda ya walakanta ni kansa ya walakanta duniya da lahira, don ba banxa nake ba, ta yaya xa a barni a gantale bakin shegen kofa daga xuwa abun arxiki?" Mujaheed na murmushi ya bude kofar yace "Toh mu munce ki xo mana da sassafe ne balle a bar ki a gantale" Bangajesa ta kusa yi ta shige parlon fuska daure, ya bi ta da kallo yana dariya, ta cire Hijab din jikinta ta linke ta ajiye tana kare ma parlon kallo tace "Idan ba dai ya xamar min dole in duba jikata ba uwar me xai kawo ni gantalallen gidanka Mujaheed, me kake bani? wllh albarkacin Imaan na xo gidan nan yau, don ubanta ya min abinda har in mutu baxan manta ba ya rike ni da kyau, ka tafi ka kira min ita in ga jikata in kama hanya inyi wucewata..." Ya dawo kusa da ita ya xauna yana murmushi yace "Oh ni ba jikan ki bane?" Ta daga hannu sama da sauri tace "A'a ba ruwana da wannan xancen, uban me dama na hada da kai?" Ya mike yace "Toh bari in kira maki ita, kina ganinta ki tashi ki bar min gidana dama kar in sa mai gadi ya fitar da ke" Bai jira cewarta ba ya wuce sama, xaune ya tadda Imaan gefen gado tana kallon door din dakin, ita kanta bata san irin kwanciyar da hankalinta yyi ba jin muryar Inna, don gaba daya tunaninta Safeenah ce kamar yanda yace mata, ya karasa dakin ya xauna gefenta ta dauke kai, murmushi yayi ya juyo da fuskarta a hankali yace "Ki sakko ku gaisa da kishiyar ki" Yana fadin haka ya mike ya kama hannunta suna isa kofar dakin yace "Ko in dauke ki?" Ta hade rai tace "Saboda me?" Daukarta yyi kamar jiya, ta xaro ido ta rikesa tace "Yaya bana so da gaske ka ajiye ni plss" bai saurareta ba har suka sauka downstairs, Inna na ganinsu ta yo waje da ido ta mike da sauru tace "Nashiga uku, me ya sameta Mujaheed??" Imaan na kokarin sauka tace "Don Allah Yaya ka ajiye ni plss" ajiye ta yyi bayan sun shigo parlon yana kallon eye balls dinta, turo baki tayi tana sauke rigarta da ya tattare, Inna ta koma ta xauna tayi tagumi, Imaan ta karasa gunta tana murmushi ta xauna kusa da ita ta shige jikinta tace "Sannu da xuwa Inna" Inna ta turata daga jikinta tace "A gaskiya Imaan ba ki yi halina ba ko kadan, kwata kwata baki da jan aji, haka kawai mutumi bai maki lefe ba ki dinga shigewa jikinsa salon ya cuce ki ya kai ki ya baro ki, meye amfanin daukan ki da yayi ynxu?" Sosai ta ba Mujaheed da ya xauna yana kallonta dariya, Imaan dai bata ce komai ba, Inna na nuna ta da yatsa tace "Wato duk abubuwan da nake gaya maki baki ji ba kenan koh?" Imaan ta turo baki tace "Ni nace maki ban ji ba?" Inna ta matsa daga kusa da ita tace "Ba ruwana wllh, idan ba ni din ba dama waye xai gaya maki gaskiyar da xai maki amfani, Bukar da Ahmadu da matansu duk sun lalace babu tsoron Allah, kuma a gaskiya ni dai ban karya ba na fito gida yunwa nake ji" Mikewa Imaan tayi ta nufi kitchen tana tafiya a hankali, Inna tayi mitsi mitsi da ido tana bin ta da kallo tace "Me ya sami kafar kuma?" Mujaheed ya mike ya isa kusa da ita ya duka dai dai gabanta yace "Ke dai kin fiye sa ido, Ina ruwan ki da abinda ya samu kafarta" sake baki tayi tana bin Imaan da kallo har ta shige kitchen, ya mike yana murmushi ya bi bayanta xuwa kitchen din, tsaye ya ganta tana taran ruwa a bowl, ya isa kusa da ita yace "Me xa ki yi?" Bata juyo ba tace "Tace bata yi breakfast ba" Ya jawota jikinsa murya can kasa yace "Xa ki iya?" Tana shakan kamshin sa tayi shiru, sai kuma ta gyada masa kai tace "Uhm" daga haka ta janye jikinta ta debo Irish ta dau peeler ta fara peeling dinsu, ya duka yana kallonta, shi ya taimaka mata ta gama soye soyen just to keep and eye on her to make sure is fine, tana daura su kan tray ya rungumeta ta baya, sosai gabanta ya fadi, tana kokarin barin wajen tace "Bana so Yaya" murya can kasa yace "Baki son me?" matsawa tayi daga kusa da shi ta hade rai, ya dinga kallonta yana murmushi, shi ya dau breakfast din ya fita parlor, xaune ya tadda Inna kana kujera tana ta xuba gyangyadi, yyi dariya ya isa kusa da ita ya ajiye tray din hannunsa yace "Mutum baxai tsaya gidan yyi bacci ba kawai ya xo gidan mutane da sassafe yayi ta gyangyadi...." da sauri ta bude ido bai jira cewarta ba ya koma kitchen, tare da Imaan da taki fitowa suka dawo parlon, gaba daya taki yarda ta kalli Inna, Inna dai sai kallonsu take ta gefen ido tana bude Madara har suka wuce sama, sannan ta gyada kai tace "Ikon Allah, da kyar idan 'yar nan ta Bukar ba jarababbiya bace" gefen gado Mujaheed ya sa imaan ta xauna ya duka gabanta yana kallonta yace "Toh ke me xa ki ci wife?" Ta dauke kai tace "Sai anjima" ya mike yace "Ohk Ina xuwa" fita yayi dakin ta bi sa da kallo, ba a dau lkci ba ya dawo da laptop dinsa da waya ya xauna gefenta ya jawota jikinsa yace "Hope ba ki jin ciwo ko Ina yanxu?" Kai kawai ta gyada masa, ya ci gaba da abinda yake a laptop din idonta na kan laptop din, sun fi 20 mins a haka wayarsa ya fara ring, a tare suka kalli wayar, Sunan Safeenah ne ya fito a screen din, imaan ta dinga kallon wayar bbu ko kiftawa, shi kansa Mujaheed kallon wayar yake, can yyi silencing kiran ya maida idonsa kan laptop, kira ya fi uku ya shigo wayarsa na Safeenah bayan first kiran, daga karshe ya kife wayar Mujaheed still operating his laptop, can kuma ya mike ya dau laptop din da wayarsa yana kallon Imaan da ta yi kwanciyar ta yace "Bari in tafi wajen Inna" Bata ce komai ba ya nufi kofa ya fita, mikewa xaune tayi ta bi sa da kallo haka nan taji gabanta na faduwa, Yana fita da kusan minti goma sai ga Inna ta shigo dakin ta rike ha6a tace "Shi Mujaheed din yace maki kar ku sakko kasa ku barni ni daya a parlor kamar shegiyar mayya?" Imaan tace "Ba ya sauka ba shi inna" cike da masifa Inna tace "Ya sauka ina? Ni kadai raina a parlor kamar tsohuwar mayya, dama wllh sai da Ahmadu yace kada in je naki ji to gashi dai an walakanta masu ni, dama abinda ya guda kenan ni ce bana jin magana" Imaan ta sauko saman gadon ta marairaice tace "Inna ni fa kaina ne ke ciwo shi sa na xo na kwanta, wllh na xata Yaya yana parlor" Inna ta kulle kofar ta karaso kan gadon murya can kasa tace "Amma dai duk abubuwan da na gaya maki a gida kina aiki da su kuwa Imaan??" Imaan tace "Na me kenan?" Inna tace "A dakin nan Mujaheed ke kwana?" Imaan bata san lkcn da tayi murmushi ba ta girgixa kai tace "Aa ba nan yake kwana ba" Inna tace "Toh kar ki kuskura sai kin ga akwatuna kin ji?" Imaan tace "Toh" Inna tace "Atoh, ko min dadin bakin da xai maki kuwa" Imaan ta gyada mata kai tana murmushi, Inna tace "Kuma kina dai cin abinci koh naga duk kin fige?" Imaan tace "Ehh Ina ci" Bude kofar dakin aka yi Mujaheed ya shigo, Inna tace "Toh Ahmadu dai yace kada in dade, haka kawai kada in bata ran d'a na, bari in je Imaan, in sha Allahu jibi xan xo..." A hankali Imaan tace "Inna ki bari da yamma mana" Inna tace "A'a haka kawai, wa gareni da xai gaya min gaskiya banda Ahmadun, ga Bukar ya xama abinda ya xama" daga haka ta nufi kofa Imaan ta mike ta ki yarda ta kalli Mujaheed dake kallonsu ta bi bayan Inna. Murmushi Mujaheed yyi ya bi bayansu yace "Toh ni ne baxa ki ma sallama ba Inna?" Inna na sauka stairs tayi kamar bata ji sa ba Imaan na biye da ita, tsaye ya gansu balcony Inna na mata magana kasa kasa, tana ganinsa tayi shiru ta fara tafiya tana cewa "Toh ni na tafi Imaan, Allah ubangiji yyi maki albarka, ai kin cika min ciki...." dariya ta basa sosai ya bi ta ya kamo hannunta yace "Toh mu je in ajiye ki a gida inna sai nima ki sa min albarkan" ta tabe baki bata dai ce komai ba, imaan dai na tsaye har ya bude mata back seat, Inna ta kalli Imaan tace "Fatan dai duk kin ji abubuwan da na gaya maki koh?" Imaan ta gyada mata kai a hankali, Mujaheed yace "Dauko Hijab dinki mu je mu yi dropping dinta" yi tayi kamar bata ji sa ba ta juya ta koma ciki, tana tsaye parlor har ta ji fitar motarsa a compound din, sai da taji Mai gadi ya kulle gate sannan ta wuce sama ta shiga parlonsa da sauri, tun da suka xo gidan ranan ne ta fara shiga parlon, duk iya dubanta bata ga wayarsa ba, hakan yasa ta karasa cikin bedroom dinsa, daddadan kamshi ke tashi dakin nasa dake very neat, ta nufi saman gado ganin wayarsa ta dauka ta bude, call logs ta shiga, sosai gabanta ya fadi tana kallon kiran safeenah da yayi picking, ta shiga details don duba minutes din kiran aka bude kofar dakin, da sauri ta juya xuciyarta na bugawa, kallonta ya tsaya yi sannan ya mika mata hannu alamar ta basa wayar, sauke kanta tayi kasa bata motsa daga inda take ba, ya karasa ya karbi wayar a hannunta sannan ya juya ya fita, Bata san lkcn da ta durkusa kasan dakin ba ta hade kai da gwiwa sai dai taji kukan ma ya ki xuwa, ta fi minti