← Book details Imaan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 251 OF 292

Sashe 251

Imaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

bugawa, sai da ya ji saukan numfashinta alamar bacci ya fara daukanta bayan wani lkci ya daura lips dinsa forehead dinta ya lumshe ido cikin sanyin murya yace "I... i love you" Bude ido tayi da sauri, ya kankameta yace "Bacci nace kiyi kanwata" Bata san lkcn da tayi murmushi ba ta lumshe ido ta mayar da kanta... Wajajen karfe biyu na dare Imaan ta farka ta gansa tsaye yana sallah, mikewa xaune tayi ta sauka saman gadon ta shiga bathroom ta dauro alwala ita ma ta fito ta bude jaka ta dau daya daga Hijabs dinta. Washegari da karfe goma na safe Mujaheed na tsaye bakin kofar kitchen bayan sun gama breakfast Imaan na wanke plates din da aka yi amfani da, ko na minti daya bai yarda ya bar ta ita kadai ba, ko me xata yi outside her room yana tare da ita, kuma tun da gari ya waye Safeenah bata sakko ba shima bai je dakinta ba, Kamar ance ya juya ya ganta ta sakko stairs yafe da mayafi ta nufi kofar fita, ya bi ta da kallo ganin xata fita, calmly yace "Where are u going to?" Ko kallonsa bata yi ba har ta fice daga gidan, Imaan ta tabe baki tana ci gaba da aikin da take. Sha biyu saura Mujaheed ya fita gidan don siyo ma Imaan dake masa complain din ciwon kafa maganin tube da take shafawa, tun wayewar gari take ce masa kafarta na ciwo, yana fita dama yace ta saka makulli kofarta, Safeenah ce xaune parlor tana ta communicating da 'yan gidansu da suka shigo garin zaria tana masu kwatancen gida, bell taji aka danna daga karshe, ta mike taji sanyi har ranta ta isa kofar ta bude tana cewa "Ashe kun ma kusa...." Umma ce tsaye bakin kofar, Safeenah ta dinga kallonta daga sama har kasa, a takaice tace "Daga Ina kuma wa kike nema??" Umma ta bude baki tana kallonta da mamaki tace "Wa nake nema Safeenah??" Cike da rainin wayo Safeenah tace "Kinga.. tun ina danne xuciyata muna magana a mutunce ki juya asirin ki a rufe ki bar gidan nan Hajiya Rukayya...." Umma ta katse ta tace "Ehh lallai kin cika yar iska mara mutunci Safeenah ni kike gaya ma haka a gidan d'a na? Ni????" Safeenah tayi wani dariyar rainin wayo tace "D'an ki? D'an ki fa kika ce? To wllh you are mistaken, kuma xaki san a da Mujaheed yake d'an ki, a da kike da iko da shi ba yanxu ba, bari ki ji abinda baki sani ba... Ke da Mujaheed sai dai hange daga nisa, sai kin san mu gidan mu ba bokaye muke bi ba matsafa masu shan jinin mutane muke bi, kuma tun muna magana ta fatar baki cikin mutunci ki juya ki ja tsummar kazamar rayuwarki ki bar gidana, shaidaniya annami...." Wani wawan mari Umma ta sauke mata tana huci, ta kuma sauke mata wani, Safeenah ta dafe kuncinta ta yo waje da ido da karfi tace "Ni kika mara Hajiya Rukayya?? Ni kika mara?" Umma na nuna ta cikin bacin rai tace "Na mare don uwarki, sakayyar da xa ki...." Umma bata rufe baki ba Safeenah ta sauke mata nata tagwayen marin masu lafiya, Umma ta gigice ta dafe kuncinta cikin shock tace "Ni kika mara Safeenah?" Cikin tsawa Safeenah tace "An mare ki Rukayya kiyi abinda xa ki yi, nace na mare ki, uban waye ke da baxan mare ki ba, meye a ciki don na mari shugabar bokaye da malaman garin kaduna?" Duk wannan abun Imaan na tsaye stairs tana kallonsu don da karfi Safeenah ke magana, lkci daya Umma ta shako Safeenah da karfi tana huci tace "Yau sai dai wata ba ke ba don ubanki, yau sai dai Mansura ta haifi wata" Safeenah ta cakumota ita ma, nan suka fara dambacewa bakin kofar suna ba juna kashi ba kakkautawa, Safeenah ta samu nasaran hayewa kan Umma ta dinga dukanta iya karfinta tana huci tana cewa "Sai na illata ki yau yanda baxa a gane ki ba idan kika bar gidan nan, ta dalilin hassadan ki da bakin ciki da mugun hali aka min kishiya kika dinga ja na gidajen bokaye da malamai don a lalata auren yarinya da saurayinta har aka fasa auren aka makala ma mijina, kin cuce ni, kin cuce ni, kin yaudare ni, Allah ya isa tsakanina da ke, axxaluma, wllh sai na illata ki yau duk abinda xai faru sai dai ya faru...." Kasa motsi Imaan tayi da farko ta makale jikin stairs tana kallonsu, ganin duka ba na wasa take ma Umma ba ta sakko da sauri tayi kan Safeenah, Safeenah na ganin haka ta raba hankalinta biyu wanda hakan ne ya ba Umma da jini ke fita bakinta da hanci damar hankadeta da karfi daga kanta ta shako wuyarta, Mari me lafiya Imaan ta wanka ma Safeenah ta fixgo gashinta da karfi tace "Yau na tabbata ke jaka ce, jahila kuma mahaukaciya.... " Safeenah tayi wani kara xata fixgo Imaan Umma ta danneta kasa, nan suka hade da Imaan suka dinga jibgarta tana ihu, Imaan bata ta6a sanin tana da karfi haka ba, don dukan Safeenah take kamar an aikota, hakan yyi dai dai da shigowar Hajiya Baturiya da Hajiyan Marafa da wata kawarta, a rikice Hajiyan Marafa ta dinga salati tana komawa baya, Imaan na ganin haka ta daga Safeenah da sauri, tana jan Umma da ta mike ita ma su bar wajen, Hajiyan Marafa ta durkusa gaban Safeenah da jini ke xuba bakinta tana salati da karfi tana cewa me xan gani haka, Hajiya Baturiya tayi wani kukan kura kamar mahaukaciya tayi kan Umma da ta nufi stairs da gudu tare da Imaan.
Chapter 251 · 0% Book details