Sashe 61
Imaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Umma na komawa bangarensu kallo daya tayi ma Mujaheed dake xaune dinning yana shan coffee tace "Ka sameni daki yanxu" sosai gabansa ya fadi ya bi ta da kallo har ta haura sama, bai iya ya karasa shanye coffee din ba ya mike ya bi bayan ta, tsaye ya ganta tana safa da marwa a dakin, Yace "Gani Umma" ta juya tana kallonsa fuska daure tace "Mujaheed ina son sanin meye matsalar ka don kaga shegiyar yarinyar nan da mai mota jiya har kake ikirarin hukuntata" ya xaro ido yace "Ban gane ba Umma" Ta masa wani mugun kallo tace "Bana son ka gane dama ai, warce kaje ka ba sakon take fadi yanxu naji, dama baka raba kanka da makiyan nan nawa ba har ynxu Mujaheed? Mujaheed ka gaya min meye hadin ka da yarinyar nan Imaan?" Yace "Haba Umma, ke yanxu maganar inna kike dauka, kila ma don ta ganki yasa ta kirkiri haka, ni a ina na ganta har muka yi wannan xancen da ita?" Shiru Umma tayi tana kallonsa, a ranta kuwa tunani take kila hakan ne ma, ganin Umma tayi surrender, Mujaheed yace "Kawai ta fada haka ne don ki sa a rai, ni yaushe nake da wannan lokacin ma a gidan nan yanxu" Umma ta sauke ajiyar xuciya tace "Sae ma kaga rashin mutuncin da ta min kayan da na kai mata, ni na ma ji dadin da ta gane cewar in don ta nine baxan bata ko tsinke na ba, basirar Abban ku ne kamar yanda ta fada" Mujaheed yyi murmushi bai ce komai ba, Umma tace "Gobe xan baka sako ka kai ma Hajiya Mansura ta marafa, bata samu xuwa bikin ba amma ta bada gudunmawarta dubu dari, cin cin da su alkaki xaka kai mata daga nan nasan xa ku hadu da Safeenah, tana nan ba ta koma makaranta ba, ni so nake nan da 'yan watanni a fara xancen naka bikin" shi dai Mujaheed bai ce komai ba banda kallonta da yake, ta xauna gefen gado tace "Kar fa kace min ka manta gobe kayi ficewarka, xuwa sha biyu in sha Allah xaka kai masu, tunda gobe lahadi" ya shafa kai yace "Allah ya kai mu" daga haka ya nufi kofa ya fita. Imaan ta kara leka samirar dake cike da cin cin da dubulan da alkaki da inna ta basu su kai ma ta rasulu aminiyarta, ta tabe baki tace "Wllh duk kin kwashe ma tsohuwar, mu fa har ynxu ba mu ci ba" inna ta tsuke fuska tace "To ina ruwana da rashin cin ku, ni na aurar da 'ya ko ko? Kaji min dai, Dubu talatin ta rasulu ta bada a kawo min gudunmawa, kuma ace baxan cika mata samira da kayan flawa ba, ni ta ma fi min Aisha kiji in gaya maki" Imaan tace "Kice ma ta fi maki har daddy mana" Maimoon tace "Toh ina dubu talatin din?" Inna ta kalleta da sauri tace "Amina aka ce in ba wa da xaki tambayeni dubu talatin Maimuna? Ko ko kin ban ajiya ne? Ni dai ku daina sa min ido a gidan nan, idan ba haka ba mugun alkaba'i ba shi da kyau amma to xance kowa ya ci kansa gaskiya" Imaan ta kalli Maimoon tace "Maimoon karbo kudin motar mu wuce" Inna ta kunce ha6ar xaninta ta fiddo naira dari ta ajiye masu tace "Hamsin xai kai ku ya dawo da ku, nan nan kabala dai" Imaan ta ajiye samirar ta xauna tace "Tabdi ko naira dari dari ma baxa a yarda a kai mu ba balle hamsin" Inna tace "Barawo ne mai adaidaitan da baxai kai ku a hamsin ba, ko ya sha wiwi ne, wllh kullum a hamsin ake kai ni a dawo da ni" Maimoon tace "Saboda ke tsohuwa ce ai" A fusace inna tace "Oh oh Allah, idan baxa ku ba ku ajiye min kayana ku fita, Xan kira Bukar ko Ahmadu cikinsu wani ya kai mun, ku fitar min a parlor" Kin fita suka yi jin abinda tace wai xata kira daddy ko Abba, Maimoon tace "Toh wai don Allah mu muka siya masu adaidaitan da xasu kai mu a hamsin su dawo da mu a haka, ki kara mana kudin mu tafi mana" Inna ta jefa masu wani hamsin tace "Aniyar ku ta bi ku dai" Maimoon ta dau kudin tana gunguni tace "Ae sai dai mu cika da kudin mu" Imaan ta tabe baki ta dau samirar tace "Sai dai ke ki cika, sisina baxan kara a kai ba tunda ba ni xan ci cin cin ba" daga haka ta fice parlon, inna tace "Shi sa har yau aka kasa gano cutar da ta sa ki gaba, saboda mugun xuciyar ki da rashin kunya, ni dai Allah ya saka ma d'ana, Allah ya saka masa kan kudaden da yake kashewa a kan tsadadden ciwon nan naki, Allah kuma ya raba shi dake lafiya, ya aurar dake ya huta ma ransa mijin ma ya d'and'ana ukubar, ba a taba jin alkhairi ya fito bakin ki sai sharri, to meye kuma don kin cika kudin mota" Maimoon ta bi bayan imaan ta kullo mata kofarta tana turo baki. Suna tsaye bakin titi suna jiran adai daita da xai je kabala, Imaan tace "Ko da yake nasan tsohuwar da xa mu kai ma baxa ta bar mu haka nan ba, kila ta ba mu kudin mota" Maimoon tace "Wllh da ba dan Abba da tace xata kira ya kai ba ba inda xanje ni dai, kullum fa idan xata aiki mutum sai ta raba kudin motar xuwa wajen kashi uku ta baka daya" Imaan tayi dariya tace "Kawai so take ayi ta mana fada shi sa tace xata aiki daddy ko Abba" motar Mujaheed da suka gani yasa suka yi shiru suna kallon motar, shi ma daga gida ya fito, ya sauke glass yana kallon Maimoon, Maimoon ta marairaice tace "Ya M.A inna ce ta aike mu kabala kuma ba mu samu adai daita ba har ynxu..." Ya gyada kai yace "Toh Allah ya kawo adai daitan" xai dage glass da sauri tace "Wait... Kai ina xaka plss?" Yace "Marafa" tace "Toh ka rage mana hanya mana don Allah" ya mata wani kallo yace "Me ya hada Marafa da kabala?" Tace "Yaya ai duk hanya ce mu dai ko ina ma ka ajiye mu nasan xa mu samu a can gaba" yace "Toh shiga" Imaan ta bude back seat ta shiga ya dinga hararanta ta madubi fuska daure, dama tun da suka hada ido taga kallon da yake mata bata sake yarda ta kalli madubin ba, Maimoon na kallon fancy nylon dake gaban motar ta dauka tace "Ya M.A wa xaka kai ma cin cin da dubulan?" Yace "Anty" dariya tayi bata sake cewa komai ba, sai da suka yi nisa yace "Gidan Baaba ta rasulu xa ki kenan?" Tace "Xa mu dai, ai ba ni kadai bace, ni da Imaan ce" ya watsa mata wani kallo ta xaro ido tana yar dariya ta rufe bakinta, har kofar gidan aminiyar inna ya kai su, Maimoon sai murna take tace "Ya M.A mun gode, ko mu raka ka marafan mu ma?" Shiru ya d'an yi da farko yana shafa kansa a hankali, lkci daya yace "Toh kar ki dade a ciki idan ba haka ba inyi wucewata" bude motar tayi ta fita tana kallon Imaan da ta fita tuntuni tana cinno baki suka shiga gidan, dari biyar ta rasulu dake ta sa masu albarka ta basu kudin mota, tace "Ina gaida Hajiya Asaben, kuyi mata godiya sosai, ita kuma amarya Allah ya basu xaman lafiya da mijinta, ku kuma Allah ya maku albarka ya fiddo maku maxaje na gari" suka amsa mata da Ameen, sannan suka mata sallama suka fita da samirar don juye kayan ciki tayi a nata samiran. Maimoon na kallon imaan tace "Wai Imaan me yasa baki gaida ya Mujaheed yanxu?" Imaan tace "Saboda baya gaida Ammi na sai ya ga Daddy" Maimoon ta xaro ido tace "Da gaske?" Imaan tace "Ehh mana" Maimoon tace "Toh saboda me" imaan tace "Oho" bude back seat tayi ta shiga Maimoon ta shiga gaba ya tada motar yayi reverse ya bar anguwar. Tafiyar kusan minti sha biyar suka yi suka iso gidan Hajiyan Marafa, Dai dai gidan yayi parking daga kusa da flowers yana kallon Maimoon yace "Xan yi sllh kafin in shigo" ya mika mata ledan yace "You take this in with you" tace "Amma yaya bamu san kowa a gidan ba fa" yace "Sai ki ce Hajiya ce ta aiko ki, ina nan shigowa nace idan nayi sllh" daga haka ya fita motar, Imaan dai na tsaye ta rungume hannu jikin motar bayan ta fita, Maimoon ta fito ya kulle motarsa da lock, ya wuce masallacin da ya gani a layin, Maimoon ta kalli Imaan tace "Mu je" bin bayan ta Imaan tayi suka shiga gidan, bayan sun sanar da mai gadi gun Hajiya suka xo, duk girman gidansu haka suka saki suke kallon gidan, Maimoon tace "Ni dai baxan shiga ba gwara mu jira sa a nan, kawai mutum yaje yana ta introduction ana masa wani kallo" Imaan ta yi dariya tace "Sai kice Hajiya Rukayya ce ta aiko mu" Maimoon ta buda ido tace "Bari ya Mujaheed ya jiki, wai Hajiya Rukayya" Imaan ta tabe baki suka shiga babban balcony din dake dauke da kujeru sannan ga babban rug a shimfide kasa, kan rug din suka xauna suna kara k'are ma gidan kallo, sai bayan da aka idar da sallah Mujaheed ya shigo gidan, kallonsu ya tsaya yi ya hade rai yace "What did I tell you Maimoon?" Ta marairaice tace "Yayanmu mun yi sallama kamar basa parlor" hararanta ya dinga yi kafin ya danna bell, ko minti daya ba ayi ba mai aiki ta bude kofar, ta gaishesa ya amsa yace "Hajiya tana nan?" Tace "Wa xa ace mata" Yace "Dr Muhd, Kice Hajiya Rukayya ce ta bada sako a kai mata" Murya can kasa Imaan tace "Toh ba gashi shi ma cewa yayi Hajiya Rukayya ba" Maimoon ta yi murmushi bata dai ce komai ba, Mai aikin tace "Toh ka shigo" bin bayan ta yayi xuwa cikin parlon da sauri imaan ta mike ta bi