← Book details Imaan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 106 OF 292

Sashe 106

Imaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

"Ni dai nagode" kallonta ya tsaya yi, dai dai nan mota yayi parking bayan nasa, Bude motar aka yi Umma ta fito, kallonsa ta dinga yi sannan ta kalli Imaan ta kara kallonsa ta kalli Imaan, Sadeeq ya gaisheta with respect, Sai da ya kara gaisheta ta amsa da sauri tace "Lafiya lau" Tana isa gate ta sake Juyawa ta kallesa saura kiris ta fada bakin gate din tayi maxa ta shige ciki, Sadeeq da ya bi ta da ido ya kalli Imaan dake wasa da fingers dinta yace "Who is she?" Imaan ta kallesa ta d'an yi murmushi tace "Mum din Yaya" Sadeeq yace "Ohk, but why didn't you greet her" Shiru tayi kamar baxata ce komai ba, can a hankali tace "Xan gaisheta ai idan na shiga" yace "Noo, that's not a point..." Ta d'an yi murmushi kawai, yace "Though I don't know why is that, and I am not suppose to intrude into family issue but promise me xaki dinga gaisheta daga yau, ita din ai babbace" Imaan ta kallesa, yace "Yea promise me" sunkuyar da kanta tayi a hankali tace "Toh in sha Allah" yayi cute smile dinsa yace "Maa sha Allah" kan wani farin kujerar roba ya ajiye ledan da ya bata ta ki ta amsa yace "Shikenan sai mu yi sadaka da shi tunda baki so, I am leaving now, mum dita na jirana" Bai jira cewarta ba ya shiga motarsa ya tada, d'an murmushi tayi cikin sanyayen murya tace "Toh nagode" ya kashe mata ido daya ya ja motar ya bar layin, a hankali ta kai hannu ta dau ledan ta wuce ciki. Sai kusan Isha ta tafi kai ma Inna abincinta bayan Ammi ta kara maimaita mata tayi blocking number Sadeeq a wayar Innan sannan tayi deleting, tana isa parlon ta ajiye abincin da ledan iron din ta gaida Inna dake goge gogen kayan kallo, Inna tace "Allah dai ya bar ni da ta rasulu kawai, Ni fa ta fiye min wasu daga yan uwa da basu da kirki ynxu, har maganar ki da yaron nan Sadeeq sae da na mata yanxu kawai kudi xan bada a kauda idon makiya a lamarin, gobe ma xan ba Mujaheed kudin ya kai mata, wa xai xauna yanxu?? Kowa ya tashi tsaye ya nemi kariya kawai" Imaan bata dai ce mata komai ba ta xauna ta dau wayarta dake kan kujera tace "Inna ga iron dinki an kawo daxu" Inna tace "Haba, Kai Allah masa albarka, to da Ahmadu ne sai dai yace min ya manta, kinga alamar wnn yasan darajan babba ko to ni dai ba ruwana, idan xaki rikesa hannu bibbiyu ki rikesa mijin aurena wllh, Allah dai ya saka masa da alkhairi, ke kuma na gaji da ajiyar wayar da ya kawo maki idan baxa kiyi amfani da shi ba a tafi kasuwa ki siyar kudin xai yi maki amfani" bata jira cewar Imaan ba ta shiga ciki, har Imaan ta gama blocking da deleting lambar Inna bata fito ba, tana kokarin tashi tace mata xata tafi, Inna ta fito duk ta hada xufa a gigice tace "La ila ha illallahu Muhammadur rasulillahi sallallahu alaihi wassalam, Innalillahi wa Inna ilaihi raji'una, laaa haula wala kuwata illa billahil Aliyul azeem... To barawo ya sace wayar" Imaan ta mike tana kallonta da mamaki, Inna ta fashe da matsanancin kuka tace "Wlh a karkashin kwalla na adana ledan wayar yanxu ko sama ko kasa wani ya shigo ya sace ban san waye ba, na shiga uku na lalace dukiyar mutane, Allah ka rufamin asiri" Mayafinta ta fixga ta fice daga parlon tana rusa kuka, Imaan dai tayi still tana kallon kofar dakinta can ta bi bayanta, tuni har Inna ta isa part din Abba, Imaan ta shiga nasu part din, Inna na shiga su Maimoon na gaisheta cikin kuka tace "Ina Ahmaduna yake?" Mujaheed dake sakkowa downstairs ya dinga kallonta da mamaki Aunty dake xaune parlor kuwa sai tambayarta me ya faru take, Inna ta rushe da sabon kuka ta xaune kasa tace "Nashiga uku, Ahmadun bai dawo bane?" Umma ta leko parlon daga kitchen bata dai fito gaba daya ba, Mujaheed ya karaso yace "Wai me ya faru ne??" Cikin kuka tace "An sace wayar da Bulasawa ya kawo ma Imaan a dakina cikin kwallaa...." Ta kunce ha6ar xaninta ta rufe fuska ta dinga kuka tace "Yanxu wani kallo yarinyar nan imaan xata min, wayar fa ance ya kai dubu dari biyar... Wayyo ni dai na shiga uku an goga min bakin fenti" Umma sai xaro ido take daga kofar kitchen tana kallon Inna jin ta ambaci Bulasawa, Aunty tayi tagumi tana kallon Inna, su Maimoon da Rahama kuwa banda dariya babu abinda suke kasa kasa.
Chapter 106 · 0% Book details