Sashe 118
Imaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Imaan ta kwace kafarta a hannunsa bayan ta ga Sadeeq ya wuce tana turo baki a hankali tace "Ni ya ma daina, dama gurdewa kawai nayi" bata jira cewarsa ba ta mike da kyar, Yusuf dake tsaye shi ma ya iso wajen yyi murmushi yace "Dama ba wani ciwo, ke dai kika san abinda kike boyewa a waje" Mujaheed ya kalleta ya kalli gate da sauri, ledan da ta jefar ya dauka ya bude yana kallon abinda ke ciki, sai kuma ya nufi gate din.... Tana ganin haka ta dau ledarta da takalmanta ta wuce apartment dinsu da sauri tana waigan Mujaheed, Yusuf yyi murmushi ya koma ya xauna, Parlor ta tadda Ammi xaune, Ammi ta amsa sallamarta tace "Meye kuma kike sa min makulli a kofa" ta xaro ido tace "Ohh na manta, nayi xaton dare yyi..." Still dai bata bude kofar ba tana murmushi ta karasa cikin parlon ta xauna tace "Ammi Sannu da gida" Ammi tace "Yauwa, ya mai jikin?" Imaan tace "Da sauki, Mum dinta tace in gaishe ki, ta ma bani wannan" tana fadin haka ta ajiye ledan a kusa da Ammi, Ammi tace "Toh Allah ya amfana" mikewa Imaan tayi ta wuce daki har sannan xuciyarta bai daina bugawa ba, yanxu da Mujaheed ya ga Sadeeq ya xata yi yau. Tun bayan da ta idar da sllhn magrib Ammi ta ce ta dau abincin Inna ta kai mata gabanta ke faduwa, har claiming ciwon kafa tayi duk don Ammi ta kira Maimoon ta kai ma Inna abincin amma Ammi tace ita dai xata daure ta kai a hakan, tana goge guntun hawayenta ta dau abincin ta fita a sanyaye, ita kanta bata gane wani sabon tsoron Mujaheed da ya diran mata yanxu ba, a hankali ta bude kofar parlon Inna ganin takalmin da bata dai san ko na waye ba bakin kofar, ta ajiye abincin a nan bakin kofa Inna na tambayar wani munafukin ne amma tuni ta juya da sauri har tana tuntube ta koma part din su. Washegari Saturday karfe takwas saura Imaan ta fito bangarensu cikin shirin islamiyya, duk gaba daya a tsorace take har Ammi ta lura da hakan amma da ta tambayeta damuwarta sai cewa tayi ita bayanta ke mata ciwo, Ammi ta sa ta sha magani sannan ta fita, parking space ta dinga lekawa ko xata hango motar Mujaheed, ganin motar tasa yasa ta ki jiran su Maimoon ta nufi gate da sauri, ta gwammace ta tafi bakin titi ta samu adai daitan da xai kai ta islamiyyar. Suna jiran drivernsu bayan an tashi islamiyya Maimoon tace "Imaan wai me yasa kika ki jiran mu daxu?" Imaan ta tabe baki tace "Salon kawai ku 6ata ma mutum lkci mu yi ta yin latti ana xane mu, naga baku fito ba ni kuma bana son inyi latti shi sa nayi wucewata" Rahma tace "Har akwai wanda ya kai ki saka mutum yin latti? Kullum sai mun yi ta jiran ki bakin mota kafin ki fito, daga ace bayan ki ya rike sai ace kafar ki ya rike, to daga yau ma kar ki sake jiranmu kiyi wucewar ki" Imaan ta kalli Maimoon tace "Kin ga dai ba da wannan matar nake magana ba ko, ki gaya mata ba ruwanta da harkata tayi ta kanta ta kyaleni..." Rahma tayi dariya tace "Ehh gwara in kyaleki kiji da ciwace ciwacen ki kam....." Maimoon ta kalli Rahma tace "Haba meye haka Rahma?" Rahma ta watsa mata wani kallo tace "Sai dai ki tambayeta meye haka, ko ni sa'arta ce aka gaya mata??" Tsaki tayi ta wuce gun motar gidan su da yyi parking dai dai lkcn, Ummi ta ja tsaki tace "Mutum sai neman fitina kawai, ana taba ta kuma lalura ya tashi a shiga uku, to dama wa xai taba sauran ciwo idan ba tsautsayi ba ma" tana fadin haka ta wuce ta shiga mota ita ma, Maimoon ta kalli Imaan dake kallonsu tace "Ki rabu da su kiyi hakuri" Imaan bata ce komai ba ta bude front seat ta shiga Maimoon ma ta shiga back seat... Suna isa gida driver yyi parking Imaan ta bude motar ta fita bata xame ko Ina ba sai part din Inna, Inna na xaune parlon tana hada kwadon rama Imaan ta shigo ta xube nan kan kujera ta fashe da matsanancin kuka, Inna ta tura roban gabanta tace "Auzubillahi, me ya sami Aishar?" Cikin kuka Imaan tace "Ko ba su Rahma da Ummi bane daga Ina magana da Maimoon suka fara xagina har da ce min sauran ciwo...." Mikewa Inna tayi ta rufe roban kwadonta ta dau gyalenta ta nufi kofa ta fice, Imaan ta dinga kuka har da shessheka, can dai tayi shiru ta goge idonta ta shiga kitchen ta dauko wani plate ta debi kwadon da Inna ke hadawa ta fice a parlon. Babu abinda Inna ta mance bata xaxxaga ma Umma dake dakinta a xaune tare da su Ummi dake mata tsarin abinda ya faru tsakaninsu da Imaan, Inna na huci tace "Kuma in sha Allahu sai kinga sauran ciwo a jikokin da xa a haifa maki..." Da sauri kuma tace "Astagafirullah, jikokin ki ai na Ahmadu ne, to in sha Allahu sai kinga sauran ciwo a dangin ku.... Kuma a kawo maki riko kiyi ta fama, duk wanda ya sake sa min jikata a bakin duniya Allah ya isa ni dai, Allah ya isa, kuma bari Ahmadun ya dawo...." Tana fadin haka ta fice. Imaan na shiga apartment din su ta tadda Ammi na ta girke girke, gaisheta kawai tayi ta wuce daki, tayi wanka tayi sllh sannan ta shirya ta fito parlor, kitchen ta shiga gun Ammi dake hada drink din Zobo tace "Ammi jirgi daddy xai biyo ko train?" Ammi tace "Ce maki yyi xai dawo yau?" Imaan ta xaro ido tace "Naga kina girki ne ai" Ammi tace "A'a mamar ku ce dai ke hanya...." Imaan tace "Mama Hadiza?" Ammi tace "Ehh sun ma kusa landing Ina ga" Imaan ta wara ido tace "Shine Inna bata gaya min ba?" Ammi tace "Ita ma bata sani ba shi yasa ban gaya maki tun jiya ba kar ki je ki gaya mata don ba control gare ki ba" Murna Imaan ta dinga yi tace "Da su Maryam xa ta xo in gansu plss?" Ammi tace "Da Maryam kadai suka taho" Imaan tace "Toh wa xai je daukota a airport nima xanje plsss" Ammi tace "Mujaheed Daddy yace yaje ya daukota" shiru Imaan tayi bata ce komai ba, can ta dau plate ta bude abinci xata diba. Hudu na yi Mujaheed ya tafi airport dauko small mum din tasa da autar ta, tun da suka kamo hanyar gida Maryam ke tambayar sa Imaan da turancinta dake kala da na turawa, yyi murmushi yace "Tana nan, tsayin ku daya sai dai ita bata jin magana..." Maryam ta kyalkyale da dariya tace "Ni duk na kagu in ganta wllh, muna fa vid call da ita once in a while" Mujaheed yace "Ae xa mu je ki ganta" Mama Hadiza tace "Amma dai yanxu ta ji sauki sosai koh?" Yace "Ehh mama da sauki sosai" Hadiza tace "Toh Alhmdllh haka Yaya Sadeeq din yace min, Toh in ji dai xa a kawo min amaryar mu gaisa kafin biki..." murmushi kawai yyi bai ce komai ba, tace "Au baxa ka kawota ba kenan" yar dariya yyi yace "Toh xa a kawota in sha Allah mama" Mama Hadiza tace "Toh da dai ya fi, kuna ta dai hakuri da tsufan Inna koh?" Mujaheed yace "Mu wllh da ma ki tarkatata ku koma tare mama" dariya Mama Hadiza tayi tace "Baka da kirki Mujaheed, ita uwar tawa kake cewa in tarkata?" Yace "Wllh mama duk ta addabi kowa a gidan..." Mama Hadiza tayi murmushi tace "In sha Allahu nan da wata hudu ma xa mu dawo Nigeria gaba daya sai in dauke uwata ta dawo wajena sai in ga ta inda xa ku dinga gajiya da ita" Mujaheed yyi dariya yace "Wllh baxata yarda ba, xata gwammace tayi ta xama tana dagawa Ahmadu da Bukar hankali" Mama Hadiza tayi dariya tace "Baka da mutunci wllh Mujaheed" parking Mujaheed yyi a parking space din su bayan sun isa gidan, Mama Hadiza tace "Allah sarki, rabona da gidan nan shekara uku kenan, anjima idan na huta da Magrib sai ka kai ni gidan Seeyama" yace "Toh Mama Allah ya kai mu" part din Abba Mama Hadiza ta fara shiga tare da Maryam don gaisawa da Aunty da Umma... Bata wani dau lkci a part din ba ta fito tare da Aunty, Umma dama tun bayan da suka gaisa ta shige daki ta kulle, Mama Hadiza na kallon Aunty tace "Rukayya dai na nan da rashin kirkinta har yanxu koh?" Dariya kawai Aunty tayi, Mama Hadiza tace "Toh yayi kyau ta ci gaba, har ni xata walakanta ta shige daki sbda bata da mutunci" ita dai Aunty bata ce komai, suka shiga part din su Imaan, Imaan ta fito daki jin muryar Maryam ta rungume ta cike da murnan ganinta, Ammi na kallon mama Hadiza bayan sun gaisa tace "Toh Ina jakar? Ko ba nan dama xa ku sauka ba" Mama Hadiza tace "Yana cikin mota Mujaheed bai fiddo ba" Ammi ta kai ta har bedroom dinta don ta kintsa, Aunty dai tayi masu sallama ta koma. Maryam na idar da sllh bayan ta ci abinci tayi wanka dakin Imaan, suka dinga hira... Ganin Magrib ya kusa Imaan tace "Plss mu je ki ba Inna surprise kawai ta gan ki" Maryam tace "Hope ta daina xagin mutane dai yanxu" Imaan tayi dariya sosai tace "Sai dai bata ga abinda xata xaga ba, ke dai mu je" A tare suka fito dakin suka wuce part din Inna ba tare da sun sanar da su Ammi dake bedroom ba, Inna na bakin tap suka iso bangaren nata, ta daga kai tana kallonsu, Imaan dai sai murmushi take, Inna tace "Waya wannan kuma kamar Zabiya?" Imaan ta fara dariya tace "Baki ganeta ba Inna?" Inna ta ci gaba da wanke wajen tace "Ka dai ji wata magana wai ban ganeta ba, yanxu ko uwata ce ta fito daga kabari idan ban ganeta baxan ce mata ban gane ta ba, tun daxu nake