← Book details Imaan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 250 OF 292

Sashe 250

Imaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mujaheed na komawa parlor bayan su Mama Hadiza sun wuce ya dau trolley din da suka kawo ma Imaan ya kai mata daki, xaune ya sameta ta jinginar da kanta jikin gado tana hawaye, ya ajiye jakar ya isa kusa da ita ya xauna yana kallonta, Hade kai tayi da gwiwa tana kuka a hankali, ya dagota yace "Ohk I am taking you home next week in sha Allah, yayi hakan?" Tana kallonsa cikin sanyin murya tace "Da gaske?" Yayi murmushi ya ja hancinta yace "Ehh mana, ko Yaya ya ta6a maki karya ne" Ta goge idonta tace "Toh Allah ya kai mu" yace "Baki yi lunch ba har yanxu" tace "Bayan abincin da na ci gidan Aunty Farida, I am not hungry" mikewa yayi yace "Let me get something outside" Bai jira cewarta ba ya isa kofa ya cire makulli ya fita ya kulle dakin ta waje, turo baki tayi ta mike ta kwantar da jakar da ya ajiye mata ta bude zip din, gogaggun kayanta ne kusan kala goma sai Hijabs har kala Biyar a babban jakan da inner wears, sai turarurrukanta da man shafa, rufe jakar tayi a hankali ta ja sa gefe ta ajiye sannan ta koma gefen gado ta xauna. Sai kusan karfe shidda Mujaheed ya bude dakin yana kallonta daga bakin kofa yace "Come downstairs" sai da ya bar bakin kofar sannan ta mike ta fita dakin tana kallon dakin Safeenah ta sauka downstairs, xaune ta samesa parlon da pineapple da aka yi slicing a plate, ta karasa ta xauna tana kallon movie da ake a Tv, yace "Baxa ki sha ba?" Kallon abarban tayi sannan ta dauke kai, ya mike ya dau plate din ya nufeta ya xauna kusa da ita, a hankali ta dau daya ta sa a baki, yyi murmushi yana kallon eye balls dinta ta hade rai tace "Ni dai ka daina kallona" ya jawota jikinsa yace "Ohk na daina" suna nan haka har kusan Magrib suna kallon movie da ake yi a TV, Jin footstep a stairs duk suka juya, Safeenah ce ke sakkowa sama fuska a murtuke, suka hada ido gaba daya da ita, a hankali Imaan ta kwantar da kanta saman shoulder dinsa, Safeenah bata sake yarda ta kallesu ba ta wuce kitchen, Mujaheed dai bai sake kallonta ba Imaan ta bi ta da harara, Mujaheed dake lura da ita yyi murmushi ya daura lips dinsa a cheeks dinta murya can kasa yace "Me ta maki?" Hade rai tayi ta kallesa, ya wara ido ya rungumeta yace "Toh yi hakuri" lamo tayi jikinsa, bayan kusan minti biyar sai ga Safeenah ta fito kitchen din ko ba a fada ba kasan yunwa take ji, suka kara hada ido da Imaan ta dauke kai da sauri ta wuce sama kamar xata tashi sama, shi dai Mujaheed bai ce komai ba, jin ana kiran sllh ya mike yace "Me xa ki ci sai in taho maki da shi when I am coming back from mosque" tace "Ae akwai abincin da muka siyo" yace "Noo ae ya huce" d'an murmushi tayi tace "Almubazzaranci Kuma?" Shiru yyi yana kallonta, tace "Sae ka dawo" daga haka ta mike ta wuce sama, a hankali yace "Imaan" ta juya tana kallonsa yace "Ki sa makulli daki idan kin shiga" Kai kawai ta gyada masa ta wuce sama shi kuma ya fita, imaan ta kusa idar da sllhn Magrib taji ana murda kofar dakin, tana idarwa ta nufi kofar a hankali tace "Waye?" Muryar Safeenah ta ji tace "Idan ba tsoro ba uban me yasa kike sa makulli a kofa, banxa matsoraciya karuwa kawai...." Imaan tayi murmushi tace "Sbda bani da lkcn biye ma jahila in daura ma kai na xunubi shi yasa nake rufe kofata, when ever I have ur time I will leave my door open, wahalalliya kawai" Bubbuga kofar Safeenah ta dinga yi da mugun karfi tana kunduma mata mugayen ashar tana cewa "In kin haifu cikin uwarki ki bude kofar nan yanxu ki ga abinda xai faru, wllh in doke ki in doki banxa in ga uban da xai tsaya maki" Dariya Imaan tayi tace "Allah ya baki lfya, kina ta6a ni xa ki sha mugun mamaki idan kika ga mijin ki ya tsaya min, mate din ki masu ji da karfi boxing suke yi why not ke ma ki fara da ki zo nan kina xubar da mutuncin ki gun 'yar cikin ki" Safeenah tayi wani kara ta kunduma mata wani xagin tace "Ki bude kofar idan ke ba shegiya bace" Imaan tace "Shegun biyu a nan ai, jarababbiya kawai" daga haka Imaan ta koma gefen gado ta xauna tana murmushi, Safeenah sai buga kofar take kamar xata cire, imaan bata sake kulata ba har ta bar kofar tana ci gaba da zage xage, sai kusan bakwai da rabi Mujaheed ya shigo gidan, ya kwankwasa kofar Imaan, mikewa tayi ta isa gun kofar ta tsaya, ganin ba a bude ba Mujaheed yace "Imaan" bude kofar tayi yana kallonta yace "Have u prayed" Bata basa amsa ba ta nufi kan gado ta xauna ta fashe da kuka, da mamaki ya karasa kusa da ita yace "What happened???" Cikin rawar murya tace "Ko ba matarka bace ta xo tana ta xagina tana bubbuga kofa wai xata dokeni, har da ce min karuwa" sae ta kuma fashewa da kuka sosai amma ba hawaye, mikewa yyi ya fice daga dakin, ta bi sa da kallo tana turo baki, Bude kofar dakin Safeenah yyi ya sameta xaune gefen gado waya kare kunnenta tana hawaye, katse wayar tayi lkci daya ganinsa, Yana kallonta da kyau cikin daga murya yace "Let me drop u this warning Safeenah, even by mistake, I mean mistakenly kika sake yi ma Imaan kallon banxa a gidan nan balle ki gaya mata magana mara dadi I will show u the other side of me, I will show you the bad side of me, Billah xa ki iya min komai in shanye in kyale ki amma banda ta6a Imaan, idan kuma kin xata wasa nake try anything silly for the second time wllh i will make you regret it" Wani murmushi tayi tace "Toh mu xuba mu ga" daga haka ta shige bandaki tayi banging kofar ta rufe. Imaan har ranta taji dadin samun Safeenah da Mujaheed yyi kuma duk tana jin abinda yace mata don a bude ya bar kofar, parlor ta sauka don warming din abinci ranta fess. Karfe goma Imaan na xaune gaban mirror tana shafa cream din gashinta a kai aka bude kofar dakin ta juya da sauri, ganin Mujaheed ta ci gaba da shafa man da take, Karasawa yyi kusa da ita ya mika mata wayar hannunsa ta karba tana kallon screen din kafin ta kai kunnenta, ya juya ya fita dakin, tana murmushi tace "Ina yini Aunty?" Daga daya bangaren Aunty tace "Lafiya lau Imaan ya ku ke?" Imaan tace "Alhmdllh, Aunty yaushe su Maimoon xa su xo?" Aunty tace "Idan kun dawo kaduna xa su xo daughter" a hankali Imaan tace "Toh Aunty" Aunty tace "Ki kwantar da hankalinki kinji Imaan, What happened is the best for you in sha Allah, kuma Babu ruwanki da abokiyar xaman ki" imaan bata iya ta ce komai ba, Aunty tace "Toh sai da safe" Murya can kasa tace "Nagode Aunty" daga haka Aunty ta katse wayar Imaan ta ajiye a sanyaye ta ci gaba da abinda take, daga karshe ta mike ta hau saman gado ta kwanta, Mujaheed ya shigo dakin ya dau wayarsa dake gaban mirror ya dawo kusa da ita ya xauna yace "Ain't you taking the fruits again?" Girgixa masa kai tayi, yace "Toh in kira maki Ammi?" Mikewa xaune tayi da sauri tace "Ehh pls" yayi dialing number Ammi ya mika mata sannan ya shiga bathroom, Ammi na dagawa daga daya bangaren Imaan taji dadi har ranta, sallama Ammi tayi, A sanyaye Imaan tace "Ina yini Ammi?" Ammi tace "Lafiya lau Imaan, ya kike?" Imaan tace "Alhmdllh, Ammi Daddy na fa?" Ammi tace "Yana Abuja" Imaan ta yi shiru, Ammi tace "Kiyi hakuri Imaan, Allah plans best, Allah yasa hakan shine ma fi alkhairi gare ki, ki kwantar da hankalin ki" Imaan ta d'an yi murmushi cikin sanyin murya tace "Ae nayi Ammi" Ammi tace "That's good...." Imaan tace "Toh me yasa Ammi ba ku xo da su Mama Hadiza ba?" Ammi tace "In xo in maku me?" Murmushi kawai Imaan tayi a hankali tace "Ina missing din ki ne" Ammi tace "Idan kin xo gida xa ki gan ni ai" Imaan tace "Toh Ammi" Ammi tace "Babu ruwan ki da kula abokiyar xamanki kin dai ji me na ce maki komai ta maki kar ki tanka, ki yi hakuri" Imaan tace "Toh Ammi" Ammi tace "Toh sai da safe" Imaan ta kalli kofar bathroom tace "Baxa ku gaisa da Yaya ba Ammi?" Katse wayar Ammi tayi, Imaan ta dinga kallon screen din sannan ta ajiye wayar ta kwanta ta lumshe ido, tana ji Mujaheed ya fito yayi shirin bacci sannan ya dawo kusa da ita ya dau wayarsa da ta ajiye gefenta yana kallon fuskarta, yace "Tashi ki sha drugs din ki" A hankali ta bude idonta tana kallonsa, ya mike ya dauko mata Magungunan ya ajiye mata sannan ya fita downstairs dauko ruwa, har ta bude Magungunan kafin ya dawo, ya mika mata ruwa a glass cup ta amsa ta sha maganin, ya fita da cup din ta koma ta kwanta haka kawai gabanta ke faduwa, ya shigo ya kashe wutan dakin ya kwanta daya side din yace "Did u perform ablution before going to bed?" Bata amsa masa ba ta juya masa baya, Bayan kusan minti goma ya mirgina a hankali ya dawo kusa da ita, juyowa tayi da sauri tana kallonsa cikin sanyin murya tace "Yaya" Jin yanda xuciyarta ke bugawa murya can kasa yace "Are you okay?" Ta girgixa masa kai lkci daya hawaye ya kawo idonta, kallonta ya dinga yi cikin duhun, a hankali ta rufe ido ta daura kanta jikinsa cikin sanyin murya tace "Bacci nake son in yi" d'an murmushi yyi ya rungumeta, ya kwantar da murya yace "Kiyi baccin ki, don't be afraid" Bata ce komai ba tayi lamo jikinsa har lkcn yana jin yanda xuciyarta ke
Chapter 250 · 0% Book details