← Book details Imaan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 255 OF 292

Sashe 255

Imaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Karfe sha daya saura na dare Umma ta shigo dakin Mujaheed sanye da hijab dinta har kasa, yana xaune ya jinginar da kansa da gado ya daga kai ya kalleta sannan ya dauke kai, he looks so frustrated har lkcn kuma bai ci abincin da Imaan ta kawo masa ba, Umma ta kulle kofar a hankali ta karaso cikin dakin tana kallonsa ta xauna saman kujera, kana ganinta kasan tana tare da damuwa ba na wasa ba, and she looks so sick, bai ce mata komai ba hakan yasa a hankali ta fara magana tace "Kana ji na Muhd?" Kai ya gyada mata ba tare da ya kalleta ba still yace "Ina ji" Maimakon tayi magana sai ta fara hawaye, sai kuma ta fashe da kuka sosai, shi dai bai yarda ya kalleta ba bai kuma ce komai ba, tana girgixa kai cikin sanyin murya tace "I don't know where to start from Mujaheed, ban san ta inda xan fara ba, amma lallai ka sani duk abinda Safeenah ta fada gaskiya ne bbu karya ko daya a ciki, she said nothing but the truth, kuma ba komai yasa na aikata hakan ba Mujaheed sai k'in da nake ma Aisha, I've gone through a lot in my husband's house all bcos of that woman, ita ce ta jefa ni cikin halin da nake ciki na sa6on ubangiji na, ta dalilinta na dinga aikata abubuwan da na aikata, amma kuma da na san Allah xai yi Ikonsa ya juya abun nan ya dawo kai na Abban ka ya baka auren Imaan wllh wllh da ban fara abinda na yi ba, I wouldn't have done what I did, I still can't imagine you having kids with Aisha's daughter, ban san ya xan dau lamarin nan ba idan ka haihu da Imaan Muhd, har yau bana son auren nan naka da ita na fada da babban murya, bana so, bana so har cikin raina, kuma baxan ta6a so ba, da auren nan ya dore wllh gwara ko raina ne ubangiji ya dauka..." Kuka take yi sosai cike da tashin hankali, ta cigaba cikin rawar muryar tace "Amma nasan babu yanda xan yi yanxu, ba abinda xan iya akan auren nan da bana so, sai dai kawai in xuba ido in ci gaba da k'in auren, kuma ni baxan ce xan sa maka baki a auren ba, I will neva do that coz you've always been obedient to me from the first, ko me na sa ka in ma kana so, in ma baka so yi kake yi with respect, baka ta6a min musu ba Mujaheed, kawai abinda na sani babu ruwana da matar ka da abinda xata haifa, babu ruwana da su har abada, put it at the back of ur mind baxan ta6a son auren nan ba kawai adalci xan maka, Baxan ta6a daukan 'yar wajen Aisha surka ba, baxan dau 'ya yan da xata haifa a jikokina ba, Wanda Ina ma fatan kada Allah ya bata 'ya ya da kai, lastly I want to say I am sorry for all the shame and frustration I've caused you before and is still causing you now, don magana na gaba sosai, you just have to take heart and pretend everything is fine" daga haka ta mike tana goge idonta ta bar dakin Mujaheed ya bi ta da kallo, jinginar da kansa yyi a hankali da gado ya lumshe idanuwansa hawayen dake makale idonsa suka sakko kasa. Imaan na kwance daki sai dai ba bacci take ba, she's just imagining ko Mujaheed ya ci abincin da ta kai masa ko bai ci ba, a hankali ta mike xaune ta sauka saman gadon ta nufi press dinta, ta fi minti biyu tsaye kafin ta bude ta ciro jakar islamiyyarta ta koma kan gado ta xauna ta bude jakar a hankali, takardar da ya ta6a jefo mata ta window da dadewa ta ciro daga cikin jakar ta dinga kallon well folded takardan sannan ta warware tana kallon rubutun ciki, ko layi daya bata kai ga karantawa ba ta daga kai da sauri jin an bude kofa, Ammi ce ta shigo dakin ta kulle kofar, kallonta Imaan ta dinga yi har ta karaso kusa da gadon ta xauna a gefe tana kallon takardar hannunta ta amsa, Imaan ta sunkuyar da kanta gabanta na faduwa, Ammi ta gama karanta Content din takardan ta ajiye gefe sannan a hankali tace "Imaan" imaan ta daga kai tana kallonta, Cikin sanyin murya Ammi tace "From all indication you are now happy getting married to Mujaheed right?" Imaan ta sauke kanta kasa bata ce komai ba, Ammi ta girgixa kai tana murmushin karfin hali tace "I am surprised har xa ki hakura lkci daya haka Imaan, I am very surprise at you, amma ki sani har gobe baxan ta6a alfahari da auren ki da Mujaheed ba, never!" Kuka Imaan ta fara yi a hankali bata ce komai ba, Ammi tace "And since you accepted him lkci daya sbda ya maki dadin baki irin na maxa, to ki sani duk abinda xai je ya dawo iyaka in maki addu'a Imaan, tunda kina ganin auren ki da Mujaheed alkhairi ne har kika hakura cikin sanyi, kuma cikin kankanin lkci Allah yasa hakan..." Daga haka Ammi ta mike ta nufi kofa Imaan ta bi ta da kallo tana hawaye, kafin ta fita tace "Ammi shi fa Yaya babu ruwansa kema kin sani, kuma ai ni ban ce na hakura ba.." Ammi ta juya ta kalleta sannan tayi murmushi a hankali tace "Ae bance da ruwansa ba Imaan, Allah ya raba ki da sharrin uwarsa, ki je ku karata da shi..." Daga haka Ammi ta fita dakin. Washegari Friday Umma taji shiru shiru dai Abba bai kirata ba kamar yanda take ta jira, har dai ya fita gidan da safe, da yamma xuwa parlonsa tayi bayan ya dawo duk da ba ita ce da girki ba amma shiru bai ce mata komai ba sai ma tambayar ta da yyi me Mujaheed suka xo yi gida jiya, don throughout ranan ita kanta bata ga Mujaheed ba, Tayi murmushin karfin hali tace "Kila sun xo gaishe mu ne, amma Ina jin ai sun koma, don duk yau ban gansa ba" Abba bai ce komai ba ta mike ta fita tana mamakin mai ya hana Inna ko Mama Hadiza yi masa magana a kan xuwan Hajiya Khadija gidan, ko ba komai dai ta ji hankalinta ya kwanta, kila basu yarda da uwar Sadeeq din bace, ta dinga fatan Allah ya sa maganar ta tafi a haka, tsabar tashin hankali ko mutum daya bata fada ma damuwarta cikin kawayenta ba, tana fitowa Parlor Maimoon tace "Umma Maman Surayya ta xo neman ki tana sama" Umma ta wuce sama da sauri jin Hajiya Saude ta xo nemanta, xaune ta same aminyar tata a gefen gadonta, Umma ta kulle kofa tana dubanta ganin yanayinta tace "Lafiya Hajiya Saude?" Hajiya Saude ta fashe da kuka sosai ta ajiye takardan hannunta tayi tagumi cikin rawar murya tace "Na shiga uku Rukayya tawa ta sameni Babansu Surayya ya sakeni...." Umma ta xaro ido tace "Ya sake ki kuma Saude? Garin Yaya, me ya faru?" Hajiya Saude ta dinga girgixa kai hawaye na sakkowa idonta tace "Surayya ta cuceni ta kunyata ni gaban kishiyoyina Rukayya, hotel ta bi saurayi karban waya abokin Babanta ya ganta, in takaice maki har hoto yayi mata, ya xo har gida ya nuna ma uban, tun jiya ake abu daya bbu tashin hankalin da ban gani ba, bayan uban ya kusa karyata da duka naga abun yyi yawa sai na nuna bacin rai na shine fa kamar wasa bawan Allahn nan ya rubuta takadda ya bani, dama kwanaki ya min daya bayan wanda yyi min shekaru biyar da suka wuce, yanxu fa duk ya katse igiyoyin, ki tashi Rukayya ki rufa min asiri ki raka ni mu tafi gun mutumin nan baxai rasa abun yi kan matsalar nan ba, fita gidan ubansu Surayya ba nawa bane..." Umma dake ta kallonta baki bude tace "Toh ina ga wllh tawa matsalar ma ta fi taki Saude...." Nan Umma ta kwashe duk yanda aka yi daga jiya xuwa yau ta labarta ma Saude tana matsar kwalla ita ma, tana girgixa kai tace "Saude ban san wani tuggun Hajiya marafa da tsinannun ya yanta xa su hada min ba nan ba da jimawa ba don nasan baxa su kyale xancen nan haka ba, ga uwar yaron nan da muka je har gida muka sameta ban san tsarin da ta xo tayi ma Inna da Hadiza ba, gashi har yanxu shiru Ahmadu bai ce min komai ba ko gaya masa ne basu yi ba oho, ya xan yi Saude? Wllh daren jiya ban rutsa ba kuma gaba daya na kasa tashi inyi sllh, yanxu haka xancen da nake maki tun safe bbu abinda na saka a ciki na sai ruwan da nake ta Sha, ga dukkan alama ma xaxxabi xan yi" Saude na matsar kwalla don ita ba ta Umma take ba ta kanta take tace "Wllh na ki me sauki ne Rukayya a kan nawa, iyaka fa idan an tada maki maganar uwar yaron ki rantse ki kuma rantsewa kiyi ta rantsewa kice baki je gidanta ba, rantsuwa ai ita ce kankat, sai a bar ki da mahaliccin ki a bar ki da rantsuwar ki kawai, ni dai ki tashi ki rakani gun bokan nan idan aure na ya mutu da sufyanu ai nawa ya kare a duniya, na shiga uku na lalace gidan uban wa xan tunkara ina marainiya da ni" Umma ta girgixa kai tace "Saude sai dai kije Balaraba ta raka ki gaskiya, don har abada ni da sake komawa gun bokan nan, saninsa bai amfana min komai a rayuwata ba, kullum ni kenan a gantale ban ta6a nasara na a xo a gani ba, meye amfanin raba auren da yayi aka aura ma d'a na?? Shegen mutumi kawai katon arne dama yasan bai san gaibu ba ya dinga amshe min kudi gashi daga karshe ya tarwatsa min rayuwa dubi irin matsalar da na tsunduma kai na fa yanxu???" Hajiya Saude ta mike tana kallonta tace "Lallai kin kasance butulu Rukayya, duk yanda na tsaya maki bamu gun wannan bokan ba mu gun
Chapter 255 · 0% Book details