Sashe 40
Imaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A hankali Imaan tace "Abba nasan idan muka fita kilan xai min fada a hanya" Mujaheed ya kalleta bai ce komai ba Abba yace "Toh ya maki fadan mu ga" Murmushi kawai Mujaheed yayi ya fita parlon, Abba yace "Maxa ku tafi kar kiyi latti mamana" Imaan ta bi bayan Mujaheed tana share idonta, tunda Mujaheed ya fito parlon Abba gabansa ya dinga faduwa, xaune ya ga Umma a main parlor fuskar nan nata a tamke, Mujaheed ya karasa inda take, ita ko bata fasa kallonsa ba, kofar fita Imaan ta nufa, Mujaheed yyi kasa da murya yace "Umma dama Abba...." Katse sa tayi tace "Bana son jin komai, Ban baka izinin fita parlon nan ba in har ni na haife ka Mujaheed, ko da kuwa me xai faru yau" Kallonta Mujaheed ya tsaya yi ba tare da yace komai ba, Anty ta fito kitchen da breakfast a hannunta tayi wani dariya tace "Su haihuwa manya...." Umma ta kalleta ta dakatar da ita da sauri tace "Ke in kina cin k'asa ki kiyayi ta shuri, ki daina min shisshigi a lamari na, ki yi mai fissheki kawai a gidan nan" Anty ta tabe baki tace "Anya akwai wanda ya kai me shiga lamarin d'a da ubansa shisshigi kuwa, kuma naga duk wanda xai ce d'a kada ya bi umarnin mahaifinsa shine mai babban shisshigi a rayuwa kuma bai dauko abinda xai fishshesa ba" Umma ta mike rai bace tace "D'an ki ko nawa? tunda ba wata shegiya ce ta haifa min d'an ba sai kiyi ta kanki ki, ki kuma cire min ido kan d'a na" Anty tace "Na wuce in tsaya ina xance irin na yara da ke, amma bari in baki shawara, domin kin haifi Muhammad ba yana nufin ke kadai ke da iko da shi ba duk ki bi ki takura ma yaro sai abinda kike so xai yi a gidan nan, kina amfani da advantage din ganin yana maki biyayya dari bisa dari...." Cikin tsawa Umma tace "Da ke da shawarar taki Allah kwashe maku albarka..." Dai dai nan Abba ya fito parlon jin hayaniya, ya kalli Mujaheed dake tsaye, ya kalli Yusuf dake tsaye stairs yana kallon su shi ma sannan ya kalli su Umma yace "Me ke faruwa nan?" Rai bace Umma tace "Ka ja ma matar ka kunne Alhaji ta fita harkata kada abu ya bace tsakanin ni da ita a gidan nan, ta cire ido kan d'a na, ta kuma yi ta kanta..." Abba ya dakatar da ita yace "I asked what happened kina min warning madam" Anty ta tabe baki tace "D'an ta da ka aika yanxu... ta hana shi xuwa saboda isa da gadara, to ni kuma bana gani inyi shiru...." Abba ya kalli Mujaheed da ya kasa dagowa ya mika masa hannu yace "Bani makullin motar...." Da kyar Mujaheed ya dago yana kallonsa sannan ya kalli Umma, ta watsa masa wani kallo alamar ya basa, a hankali Mujaheed yace "Abba ai bance fa baxan je ba" yace "Eh baka ce ba, amma ba ni" Mika masa makullin Mujaheed yayi, Abba ya kalli Yusuf yace "Here, ka tafi ka ajiye Imaan a makaranta" Yusuf ya karasa saukowa stairs da yake tsaye ya amshi makullin sannan ya nufi kofa ya fita, Juyawa Abba yyi ya koma parlonsa, Mujaheed ya wuce sama a sanyaye, Anty ta tabe baki ta wuce saman ita ma, wani ajiyar xuciya Umma ta sauke ta koma ta xauna ranta fess. Sai bayan da suka bar gidan Imaan ta kalli Yusuf tace "Ya Yusuf Umma ce tace yaya kar ya kai ni koh?" Yusuf na driving yyi murmushi yace "Toh dama ya xa ayi ta bari ya kai ki?? salon ku je ya d'an rankwashe ki ki dawo kina mana ihu kina kuka" xaro ido Imaan tayi tana kallonsa, Ya ki kallonta sai murmushi yake, ta hade rai tace "Toh an doki mutum kuma baxai yi kuka ba" Yusuf yace "A'a xai yi kuka abunsa" Turo baki tayi bata ce komai ba, shi ma bai kuma cewa komai ba har ya iso islamiyyarsu ya tsaya bakin gate, ya kalleta yace "Kin fa yi latti sosai" tace "Ae xa su ga idona kuma cewa xanyi bani da lafiya, dama ban da lafiyan" daga haka ta bude motar ta fita, D'aga masa hannu tayi, yayi mata murmushi ta shiga cikin makarantar. Imaan na dawowa islamiyya karfe sha biyu kashegari lahadi ta fara shirin tafiya gidan gwaggonta wato Mahaifiyar Ammi dake unguwar rimi, Tun da ta fito daki Ammi dake xaune parlor ke kallonta, tsadadden atamfa ne jikinta sai dan kunnenta na gwal, babu abinda ke fuskarta banda eye pencil da chappete da ta goga a lips, sosai tayi kyau duk da haka, da mamaki Ammi tace "Ina xa ki?" Imaan ta xauna kusa da ita tace "Gidan Gwaggwo mana Ammi" Ammi ta mata wani kallo tace "Kin gaya ma Daddy ne?" Ta marairaice tace "Daddy baxai hanani ba fa na sani" Ammi tace "Baxa fa ki fita gidan nan ba sai da saninsa don ba ruwana" tashi Imaan tayi kamar xata yi kuka ta shiga dakinta kiran Abba, wayarta da bata damuwa da ta dauko ta yi dialing number sa, bayan wani lkci ya dauka, ta amsa sallamarsa sannan ta gaishesa, yace "Ya kike Imaan" tace "Lafiya Daddy ya aiki?" Yace "Alhmdllh, har kun dawo islamiyyar?" Tace "Ehh daddy dama gidan gwaggwo nake son in je in gaisheta shine Ammi tace sai na gaya maka" yace "Ae kina da islamiyya da yamma mamana" kamar xata yi kuka tace "Ae kafin karfe hudu xan dawo" yayi shiru kafin yace "Toh waye xai kai ki?" Tace "Ni kadai Daddy ai ina xuwa ni kadai" yace "Kai ma Ammin ta ki waya" fita dakin tayi ta kai ma Ammi waya, Ammi ta amsa ta kai kunne, daddy yace "Why not drop her plss bana son tana fita ita kadai" Ammi tace "Sai kace wata yar shekara goma yallabai, she do go out her self...." Daddy yace "Toh minti nawa ne kin ajiyeta ki dawo" Ammi tace "I told u for the past two month ban shiga motar nan ba, sai dai ta bari next week mu je tare idan Allah ya yarda, ina da aikin da xan yi yanxu, ko jiya fa naje gidan gobe ma xan je, yau kuma sai na kai Imaan?" Daddy yace "Bata wayar" Ammi ta mika mata, daddy yace "Mamana ki bari next week ku je da Ammin ki idan Allah ya kai mu" imaan ta fashe da kuka tace "Bayan na shirya daddy, na fa san hanya ba yau xan fara xuwa ni kadai ba" Daddy ya dan yi shiru kafin yace "Shikenan to kije, but go with ur nose mask, and inhaler, Allah ya kiyaye hanya" tana goge idonta a hankali tace "Toh daddy na gode" Ammi ta shiga kitchen ta dauko dambun naman da tayi ma mahaifiyarta tace "Ki kai ma gwagggo ina gaisheta sai na xo goben" Imaan ta amsa tace "Toh" dubu Biyu Ammi ta bata ta bar gidan bayan tasa gogaggen Hijab dinta har kasa, a dai daita Imaan ta samu da xai kai ta har gidan, bayan sun isa ta sauka ta basa kudinsa sannan ta shiga gate din gidan, babban gida ne sosai da su Ammi suka siya ma mahaifiyar tasu, Ammi ce ta biyu gun gwaggwo bayan babban yayansu Umar, sai maxa biyu da mace daya Anty Murja, duk sun yi aure da 'ya yansu, yar Anty Murja ta biyu Halima ce ke gaban gwaggwo kuma ita xa ayi aurenta kwanan nan, Sosai Gwaggwo tayi murnar ganin Imaan, duk cikin jikokinta ko da bata nunawa ta fi jin Imaan har ranta, Imaan ta rungumeta cike da jin dadin ganinta ita ma, Gwaggwo tace "Kin guje ni Fatima" Imaan tace "Toh Gwaggwo kinga idan naje boko da safe da yamma muna dawowa xan wuce islamiyya, ranan asabar kuma islamiyya safe da yamma, yau ma kawai dai na taho ne kuma da wuri xan koma saboda islamiyya" Gwaggwo tace "Toh Allah ya maki albarka ya baki sa'a a karatun ki, ya Ammin ki fa?" Imaan tace "Tana gaishe ku, tace in kawo maku wannan" Gwaggwo tace "Toh nagode Allah mata albarka, fatan mutan gidanku duk suna lafiya" Imaan tace "Duk lafiya lau" Ammi tace "Mujaheed ya daina xuwa min kwata kwata yanxu yana kasar kuwa?" Imaan tace "Yana nan" Gwaggwo tace "Ikon Allah, shi kuma d'an farin fa, duk da shi baya ma gaida mutane dama" Imaan tayi dariya tace "Shi ma yana nan" Gwaggwo tace "Toh Allah maku albarka, in ji kakarku tana lafiya" Imaan ta turo baki tace "Ehh" Gwaggwo tace "Toh Allah ya kara mana lafiya, ki dauko lemo fridge ki sha" Imaan ta gyara xamanta tace "Anty Halima bata nan ne?" Gwaggwo tace "Taje kai anko" Imaan tace "Toh ni ba a ban ankon ba" Gwaggwo tace "Xa ta kai maki naki har gida tace" Imaan ta washe baki tace "Toh" mikewa tayi ta dauko malt daya ta dawo ta xauna ta fara sha tana cin dambun naman da ta kawo, Gwaggwo tace "Inji yanxu ciwon ki yana sauki sosai kamar yanda mahaifiyar ki ke gaya min idan na tambaya" Imaan tace "Ehh da sauki" Da damuwa Gwaggwo tace "Allah ubangiji ya yaye maki wannan cutar Fatima, in sha Allah xaki samu lafiya gaba daya muna nan muna gaya ma Allah" Yar dariya Imaan tayi tace "Gwaggo ya Salim yana xuwa?" Gwaggwo tace "Yauwa kwanaki yayanki Muhsin ya kawo min karar ki wai baki gaida mutane" Imaan ta hade rai ta daina cin naman da take tace "Ni kullum sai yace bana gaishesa, to ma a ina nake ganinsa balle in gaishesa" Gwaggwo tace "A'a Fatima ga wannan dai waya da ta kawo komai da sauki, ko shi kika dauka ai xa ki kirasa ku gaisa" Imaan ta turo baki tace "Toh shi ma fa ba kulani yake ba wllh" cike da damuwa Gwaggwo tace "Ni dai ku rike xumunci don Allah, ba kya ganin yanda iyayenku ke yi ne, ubansa ya sha nono ya bar ma uwarki, wllh baki da yan uwan da ya wuce su don mutan gidanku ba son ke da uwar ki suke ba duk an sa maku ido, ga kakarku fitinanna, kiyi