← Book details Imaan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 292

Sashe 86

Imaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

27.....

Imaan dai bata tanka ta ba ta nufi stairs, Umma tace "Ragowar ciwo kawai" Sai da Imaan ta isa stairs ta turo baki ta wuce sama, sai kuma ta fashe da kuka, dai dai corridor suka hadu da Mujaheed ya fito dakinsa, ya bi ta da ido har ta shiga dakin Aunty, Karasawa stairs yyi yana lekan downstairs ganin Umma xaune ya dawo da sauri ya bude kofar dakin Aunty ya shiga ya kulle, Aunty na tsaye kanta sai tambayarta me ya faru take hankali tashe, Imaan da ta xube mata nan tsakar dakin ta dinga kuka ta ki cewa komai, Aunty tace "Kinga iskancin nan naki ne bana so, baxa ki bude baki ki min magana ba, me kika yi ma Ammin?" Still ta ki cewa komai, Mujaheed ya karasa kusa da su yana kallonta yace "Baxa ki bude baki ba ana maki magana?" Ta hade kai da gwiwa cikin rawar murya tace "Ko ba Umma bace take xagina ni ban mata komai ba har da ce min ragowar ciwo" Aunty ta ja tsaki tace "Shine xaki xo ki tada min hankali a nan? Sai me don ta ce maki ragowar ciwo? Xa kuwa ta ga ragowar ciwo a xuri'arta wataran, domin ita ta gama haihuwa ai yanxu su kuma 'ya yanta xa su fara...." Juyawa Mujaheed yyi ya nufi kofa, Aunty ta bi sa da harara har ya fita, Aunty tace "Banda shashanci shine xaki xo kina ma mutane kuka, yau ta saba gaya maki haka?" Ita dai Imaan bata ce komai ba sai share idonta take, Anty tace "Aiko ki Ammi tayi ko me?" Ta dago ta kalleta a hankali tace "Abba ne ke kirana" Aunty tace "Tashi mu je, yana parlon sa ai" mikewa imaan tayi ta bi bayan Aunty suka fita, Umma ta dinga bin su da wani kallo, Aunty ta nufi parlon Abba tana cewa "Ae ba mahalukin da ya isa raba ki da ubanki, sai dai a ganki a kyale bbu ynda aka iya da ke" Aunty ta bude mata kofar tace "Shiga" Imaan ta shiga parlon Aunty ta rufe kofar ta koma sama, Abba na xaune yana kallon news Mujaheed ma na parlon, sallama Imaan tayi ta xauna kasa ta gaida Abba dake kallonta, yace "Lafiya lau Mamana sai yanxu kika xo?" Kai kawai ta gyada masa, Abba yace "Toh yayi" bai kuma cewa komai ba, Imaan ta saci kallon Mujaheed taga kallonta yake, suna hada ido ya hade rai, turo baki tayi tana fidgeting fingers dinta, Bayan few minutes Abba yace "Imaan ai kin san wannan yaron Sadeeq koh?" Shiru tayi bata ce komai ba ta kuma kasa kallon Abba, Abba yace "Ina saurarenki" ta gyada masa kai tace "Uhm" Abba yace "Kar fa ki boye min komai I am ur father, ki gaya min meye tsakaninku" dauke kai tayi ta ki cewa komai, Abba yyi murmushi yace "Baxa ki gaya min ba kenan" Nan ma dai ta ki cewa komai, Abba yace "Toh tunda ni kunyata kike ji sai ki gaya ma Mujaheed meye tsakanin ku" Xaro ido tayi tana kallon Abba, Abba ya mike yace "Xan dawo yanxu, let me make a call outside, sai ki gaya masa kafin in dawo shi kuma ya gaya min" daga haka Abba ya fita ya kulle kofar, tun da Abba ya fito Umma ke binsa da kallo har ya fita main parlor, ta kalli kofar parlon sa.... Imaan dai ta kasa xaune waje daya bayan fitar Abba, jin shiru ta d'an saci kallon Mujaheed, ganin irin kallon da yake mata xata mike yace "Koma ki xauna" ta marairaice tana dubansa tace "Ni fa ruwa xan je in sha in dawo" ya dawo kusa da ita ya xauna yana kallonta da kyau cikin husky voice dinsa yace "Me nace ki ce ma Abba?" Ta 6ata fuska kamar xata yi kuka a hankali tace "Yaya ba ka riga ka gaya min jiya ba, ai xan gaya masa...." Sai kuma tayi shiru, ya hade girar sama da ta kasa yace "I will slap you idan baki gaya min abinda xaki gaya masa ba" Tace "To ba cewa kayi ince ban san sa ba...." ya dinga kallonta fuskarsa daure, a hankali ta mike da nufin fita parlon ya fixgota ta fado jikinsa, xaro ido tayi tace "Yayaa" bude kofar parlorn aka yi yyi saurin janyeta jikinsa, Kallonsu Aunty ta dinga yi daga inda take tsaye bakin kofa, Mujaheed duk ya daburce ya mike tsaye, Imaan ta zamo kasan kujeran kamar xata yi kuka, Aunty tace "Meye hakan" Mujaheed yace "Aunty kawai daga mata magana shine xata fado kaina" Aunty ta tabe baki har sannan tana kallonsu, juyawa tayi xata fita sai ga Abba, ta basa hanya ya shigo parlon, Anty ta fita waje, Abba na kallon Mujaheed bayan ya xauna yace "what did she say about him?" Mujaheed ya xauna saman kujera yana shafa kansa a hankali yace "Tace ba komai tsakaninsu, bata ma wani sansa ba kawai shine ke kiranta a waya..." Imaan ta kallesa da sauri, Abba yace "Haka ne Imaan?" Kamar xata yi kuka tace "Abba ni dai bance masa haka ba, frnd dina ne fa, kuma yana koya min karatu ta waya wani lkcn, ina ganewa kuma" Mujaheed ya kasa kallon Abbansa, Abba ya kafe sa da ido, can ya d'an yi murmushi mara sauti yace "Toh shikenan mamana, tashi ki tafi" mikewa tayi ta nufi kofa, xata fita ta d'an saci kallon Mujaheed da ya ki dago kansa ta fita. Bata damu da irin kallon da Umma ke mata ba har ta fita parlon ta wuce part din su. Abincin inna ta dauka ta tafi kai mata, sallah ta sameta tana yi a parlor ta ajiye abincin xata fita, inna ta dinga gyaran murya alamar ta tsaya, imaan tayi kamar bata ji ba tayi wucewarta da sauri, a hanya ta tadda Yusuf rike da ledan fruits xae kai ma inna, ta gaishesa tana kallonsa, sama sama ya amsa mata ya wuce, ta tsaya ta bu sa da kallo har yyi nisa, turo baki tayi ta bar wajen, har ta gama shirin kwanciya kiran Sadeeq ya shigo wayar ta, ta kashe fitilan dakin ta hau saman gado ta rufe har kanta da duvet sannan ta daga kiran, murya can kasa ta amsa sallamansa yace "Kin fara bacci ne?" Ta girgixa masa kai tace "A'a" murmushi yyi yace "Toh ya kike?" Tace "Alhmdllh, ya aiki?" Yace "Lafiya lau..." A hankali tace "Shine daxu baka ce min xa ku xo da ya Muhsin ba koh?" yyi murmushi yace "Shi yace kar in gaya maki" tace "Toh yanxu da kun sameni ban sa Hijab ba fa?" Ya wara ido yace "Yea sai in ganki da kyau, ai ba laifi bane don naga abinda nake so ba hijab" ta xaro ido tace "Uhnnn?" Yace "Yess" murmushi tayi bata ce komai ba, Yace "Ya Ammi fa?" Tace "Tana lafiya" yace "Maa sha Allah, kinje gun kaka yau?" Tace "Ehh na je kai mata abinci" yace "Ina son in samu time in xo mu yi hira sosai da ke da kaka" ta xaro ido tace "Ai ita bata hira, bata fiye son magana ba ma" Dariya Sadeeq yyi yace "Really?" Kamar xata yi kuka tace "Ehh" yace "Uhm to shikenan, yaushe xan xo mu yi hiran mu biyu kadai, I want to tell you lot of things Imaan" Murmushi tayi tace "Ae Daddyna na gari bai koma ba tukun" Yace "Toh baxa ki gidan gwaggo ba mu hadu can?" Ta d'an yi shiru, murya can kasa yace "Are you there Imaan?" A hankali tace "Toh gobe xan ce ma Ammina xan je can dama ai saura kwana uku bikin Anty Halima kilan idan na je sai bayan bikin xan dawo gida" yace "Toh shikenan idan kin shirya goben sai ki kirani" ta xaro ido tace "But ai sai Ammi ta amince in je, kasan ba a son ina fita ni kadai" yace "Toh Allah yasa ta amince" Tace "Ameen" da sauri Imaan ta cire duvet din kanta jin kamar ana bude window, ganin farin abu tayi ya fadi kasan dakin, ta sauka gadon ta nufi windon da sauri ta bude labule har sannan waya na kare kunnenta, Mujaheed ne tsaye kusa da window din, ta xaro ido tana kallonsa, yana mata wani kallo ya juya ya bar wajen, ta rufe window din ta durkusa ta dau takardan tana kallo, muryar Sadeeq taji a kunnenta yace "Are you there?" Tace "Yea ina ji" yace "Ko kin fara jin bacci ne" murmushi tayi tace "Um" don so kawai take ta bude takardar ta ga content dinsa, yace "Toh shikenan, sleep like a baby dear" murmushi tayi tace "Toh nagode, good night" daga haka ta katse wayar ta ajiye ta kunna fitilar wayar ta warware takardan tana haska rubutun kai, xumburo baki tayi ta cukwuikuye takardan ta jefar ta kwanta kamar xata yi kuka tace "Ni dai ba ruwanka da ni"
Chapter 86 · 0% Book details