← Book details Imaan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 292

Sashe 93

Imaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mikewa Imaan tayi da sauri ta nufi cikin gidan tana waigan ko Mujaheed ya dawo har ta shiga ta kulle kofa, dakin gwaggwo ta wuce ta boye box din a cikin trolley dinta, tsoronta daya yanxu Ammi, bata san me xata ce ba idan ta ga dankunnen, bayan Magrib suna cin abinci tare da Anty Halima da wata kawarta, wayar Halima ya fara ring, dauka tayi bayan taga mai kiran ta kalli Imaan tace "Wai ina wayar ki?" A hankali Imaan tace "Yaya ya kwace min" Halima ta xaro ido tace "Saboda me?" Buda hannu Imaan tayi alamar bata sani ba, Halima ta mika mata wayar tace "Toh gama magana tukun" karba Imaan tayi ta kai kunne bayan ta daga hade da yin sallama, Sadeeq ya amsa mata daga daya barin yace "Har yanxu baki yi charge din wayar ki bane Imaan?" A hankali tace "Ehh" yace "But naga akwai wuta ai yanxu, ina ma anguwar" ta langwabar da kai tace "Wayar na gida fa" yace "Ohk after Isha xan kira ki, it's almost time now" tace "Allah ya kai mu" daga haka ya katse wayar, Imaan ta ajiye gefen gado, Halima tace "Haka kawai Mujaheed din ya amshe maki waya?" Tace "Ehh wai saboda abokin Muhsin na kirana" Bude baki Halima tayi tace "Toh shi ina ruwansa" Imaan ta buda hannu tace "Nima ban sani ba" Rabi'ah kawar Halima tace "Yayanki ne kuma?" Halima tace "Cousin dinta dai" Rabi'ah ta d'an bude ido tace "Toh ko son ki yake?" Still Imaan tayi tana kallonta da wani expression, can tace "Yaya ne fa... Yayana ne shi" Rabi'ah tayi dariya sosai tace "Wai yaya ne, to haka kawai baxai dinga hana ki waya da samari yana kwace maki wayar idan babu wani abu a kasa" Imaan ta ajiye cokalin hannunta a hankali tace "Abu kamar me?" Halima tace "Tukunna dae me yace maki da yaga Sadeeq din na kiran ki?" Imaan ta jingina da gado tace "Kawai ya hanani waya da shi ne, har blocking dinsa yyi ni kuma nayi unblocking dinsa, a gida ma da Abba ya kira ni xai tambayeni meye tsakaninmu da Sadeeq kafin in je ya sameni wai ince ban san sa ba" Dariya sosai Rabi'ah take, Halima tayi murmushi tace "Tabb, lallai Mujaheed" Imaan dai sai kallonsu take don bata san me ya basu dariya ba, Rabi'ah ta ajiye spoon din hannunta tana kallon Imaan da kyau tace "Toh wllh son ki yake...." Imaan ta xaro ido ta koma baya da sauri tace "Don Allah ki daina cewa haka plss, wllh yaya na ne fa, Anty Halima yaya fa ne" Halima tayi wani murmushi tace "As far as ba ciki daya ku ka fito da shi ba ki daina deceiving kanki Imaan Mujaheed son ki yake, so mai tsanani ma kuwa, ni dama tun lkcn da yake kawo ki nan few years back ina ganin irin kallon da yake maki nasan ba a banxa ba da abu a kasa, sannan kulawar da yake maki ko kanninsa basa samun haka, abinda Mujaheed ke maki a da ya wuce shakuwa ko so na 'yan uwantaka, ke dai ce ban san lkcn da xaki yi wayo har ki fahimci inda ya dosa, wai yaya ne... A'a ba yaya ba..." lkci daya hankalin Imaan ya tashi ta fashe da kuka sosai tace "Wllh ku daina cewa haka ba kyau, ni ba wani so na da yake yi, ina ce maku yayana ne fa, to taya xai so ni, ni kanwarsa ce fa..." Dariya kawai Rabi'ah take don imaan tayi mugun bata dariya nan kuma ta yarda har sannan Imaan na tare da yarinta ba kadan ba sannan ga ta only child shi sa abun ya taru ya mata yawa, Imaan ta mike da sauri ta fice daga dakin ta koma wani daki ta xauna kan gado maganganunsu na mata yawo a kai, fashewa tayi da matsanancin kuka ta fada kan gadon tace "Ni baxan ma kwana a gidan nan ba, ta ya xa a ce wai yaya na so na, wai yaya fa?? Allah ya kiyaye wllh" Imaan bata ta6a jin abu ya tsaya mata a rai irin abinda Halima da kawarta suka gaya mata ba, wai Mujaheed sonta yake, tabbb, ji tayi ita gaba daya duniyar ma babu wanda take jin haushi kamar Mujaheed din, duk da tasan baxai ma taba yiwuwa ace yana sonta ba, amma abinda suka gaya mata yasa ita taji bata ma son sa shi a ido, bata son ganinsa kwata kwata, lamo tayi kan gado very restless, aka bude kofar dakin ta juya da sauri, Halima ta shigo tace "Gashi Sadeeq ya kira" Imaan ta mike xaune a hankali ta amshi wayar ta kai kunne tare da masa sallama, ya amsa yace "I am outside Imaan" tace "Toh bari in fada ma gwaggo" daga haka ta katse wayar ta tafi ta nemo gwaggo ta gaya mata, Gwaggwo tace "Toh ya shigo mana ai ba kowa parlon ma, ce masa yayi shigowarsa kawai" Imaan bata ce komai ba ta sa Hijab dinta ta fita, tsaye ta gansa ya jingina da motarsa, ta karasa kanta a kasa ta tsaya keeping a enough distance tsakanin su, kallonta kawai yake, ita ko bata yarda ta kallesa ba, a hankali yace "What's wrong imaan you look disturbed" da sauri ta daga kai ta kirkiri murmushi tace "A'a ba komai fa, ya gida" yace "Lafiya lau" tace "Gwaggwo tace ka shigo ciki ba kowa a parlor" Yace "No ni baxan shiga ba kunyarta nake ji yanxu" murmushi Imaan tayi tace "Toh akwai kujeru a compound ai, shi ma baxa ka shiga ba?" Ya shafa kansa smiling sweetly yace "Ohk then mu je" ita ta shiga gaba ya bi bayanta har suka shiga cikin compound din. Sai da ta fara xama kan farin plastic chair sannan ya xauna shi ma yana kallonta, dauke kai tayi ganin kallon da yake mata yace "Amma ba dai kunyata kike ji ba" murmushi tayi tace "Shi nake ji mana" Yayi dariya yace "Aa kiyi hakuri kar ki ji plss" Ita dai bata ce komai ba, bayan few seconds yace "Did you know what imaan" ta daga kai ta d'an kallesa, cikin sanyin murya yace "I am hoping to spend the rest of my life with you" Imaan ta sauke idonta kasa, yace "I was born and bred in Uk, yawancin rayuwata duk can nayi sa, daga baya na dawo Nigeria gaba daya, I've neva for once thought xan hadu da mace yar Nigeria inji ina son rayuwa na har abada da ita sai kan ki Imaan, my ex was white ita ma it's not as if I have much feelings for her, it's just to while away time... Here in Nigeria frndship kadai ne tsakanina da yan mata, Ni ban san meye so ba, I don't even believe in it until I met you few months back, pls don't break my heart imaan, it's too fragile for something this big...." Imaan tayi murmushi a sanyaye bata dai ce komai ba, yace "Yea... I have been counting down tun yanxu xuwa ranan da xaku fara waec, but plss me yasa baxa kiyi waec din a ss2 ba" xaro ido tayi ta kallesa, yace "Sure, a lot a ss2 suke waec" tace "Aa nafi son inyi ss3" ya lumshe ido ya bude yace "almost a year to come in sha Allah kenan fa Imaan?" Imaan ta kallesa tace "Sure" yace "Toh Allah ya kai mu lafiya" Tace "Ameen" Yace "Promise me something plss...." Imaan tayi shiru tana kallonsa, yace "Ki min alkawarin baxa ki yi betraying din soyayyata gare ki ba, and I am also promising u same, I will and will neva leave u for any reason" lkci daya jikin Imaan yyi sanyi tace "Ae an riga an san ka gidanmu, so there is nothing to worry about" yace "Sure an san ni, but I am afraid of ur cousins" da mamaki tace "Cousins dina kuma?" Ya d'an yi murmushi yace "Yea kada su min fin karfi...." Imaan ta kasa daina masa kallon mamaki tace "Su ai yayyina ne ba so na suke ba" Sadeeq ya girgixa kai yace "I saw their reactions ranan da Abbansu ya kira ni, more especially the very fair one" Imaan gabanta ya shiga faduwa, Sadeeq yace "They might not tell you now amma kada watarana su xo su ce suna sonki ki mance alkawarin mu, kada ki min haka plss Imaan..." cike da damuwa ya fadi haka, imaan ta ji kamar ta fashe da kuka tace "Ni ka daina cewa haka, ba wanda ke so na cikinsu duk yayyina ne su wllh, they are only disturb sbda ban gama secondary schl ba" yace "Toh Allah ya sa haka, amma ba sai kin min kuka ba gimbiyata, reminder ne" Imaan ta boye fuskarta da Hijab, yyi murmushi yana kallonta, murya can kasa yace "Kin san inda xan kai ki for our honeymoon?" Kamr yace ta kara boye fuskarta da Hijab cike da shagwaba tace "Ni dai bana sooo" yyi dariyarsa mai dadin sauraro yace "Toh na bari baby, when the time comes xa ki ga, amma fa tare da kaka xa mu" da sauri Imaan ta bude fuskarta ta xaro ido tace "Aa ba inda xata bi mu" Sadeeq couldn't help it but laugh yace "Are you serious??" Ita kanta sai daga baya taji kunyar abinda ta fada ta mike da sauri xata wuce ciki yace "Noo plss wait dear, ki rakani first plss" da kyar ta yarda ta rakasa gate tana sinne kai, ya juya yana kallonta kafin yace komai, a hankali tace "Thanks much for the earrings na gode sosai" Ya mata wani kallo yace "Bana son ki min godiya idan na baki abu, ba don ki gode min bane na baki" murmushi kawai tayi bata ce komai ba, nan suka yi, sallama ta daga masa hannu ta koma cikin gida. Washegari gidan gwaggwo ya xamo ba masaka tsinke saboda yan uwa da abokan arxiki duk da gobe ne daurin auren, imaan dai na daki duk ta takura, ita dama haka Allah yayi ta bata da sakewa cikin mutane, babu yanda Halima bata yi da ita kan ta bi su gidan wata makociyarsu ba don can xata xauna har
Chapter 93 · 0% Book details