← Book details Imaan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 292

Sashe 7

Imaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

kafar da kyar. A hankali ta bude kofar parlorn Inna ta shiga da sallama, Abba ne xaune parlorn sai Inna da Anty, Imaan ta sunkuyar da kanta ta karasa kusa da Anty ta xauna kanta a kasa ta gaida su, Abba da Anty kadai suka amsa, inna ta wani tsuke fuska, Imaan dai bata ko kalleta ba, Inna tace "Wato shi Mujaheed din jira yake kaje ka ciccibo sa da kanka koh?" Abba ya kalli Imaan yace "Tashi ki tafi can bangaren ki kira min Yayanku" Imaan ta mike ta d'an harari inna ta gefen ido ta fice a parlorn, tana isa part din su Mujaheed ganin bbu kowa parlor sama ta haura ta tsaya corridor tana kallon door din dakinsa har ta mance rabon da ta je kusa da kofar, bude kofar Umma aka yi sai ga shi ya fito, ta matsa da sauri don kusa da kofar dama take tsaye tace "Abba yace in kira ka" ko kallon ta bai yi ba ya fara sauka stairs, ta murguda masa baki ta bi bayansa, har suka isa part din Inna bai juya ba, ya bude kofar ya shiga da sallama, kusa da Anty Mujaheed ya durkusa kansa a kasa, Abba sai kallon sa yake yana girgixa kafa, Imaan ta shigo parlorn ganin inda ya durkusa tace "Waje na ne nan" Murmushi Anty tayi, shi kam ko kallon ta bai yi ba balle ya motsa, Inna tace "Ahmadu na fa gaji da xama nan kamar warce xa a ma gafara, aji da ni in tashi in shiga ciki in kwanta" Abba ya kalli imaan yace "Samu wani wajen my friend" ta harari Mujaheed ta koma wani wajen ta xauna, Abba na kallon Mujaheed yace "Muhammad ita innar ka mayar abar wasar ka a gidan nan?" Inna ta tabe baki tana jijjiga kafa, Mujaheed bai dago ba kuma bai ce komai ba, Abba yace "Am I not talking to Mujaheed" ya dago a hankali yace "Abba kayi hakuri don Allah" Abba yace "Stupid, ni ma kake ba hakuri?" Ya kalli inna yace "Kiyi hakuri inna" dakatar da shi tace "A'a malam a gaban ubanka xaka ce min inna kenan, wllh Ahmadu daxu yana nuna ni da yatsa a can bakin kofar kamar xai make ni Hajiya yace min, ni na ma xata duka xai kai min bayan ya gama kashedin, to gaskiya da sake, sam yaranka basu da d'a'a basu da kunya Ahmadu, isuhu ne kadai dama mai gudun bacin raina duk da shi ma ko aiki xai kashe ni baya taimakona, to ynxu Mujaheed da wani ne da ya xo ya gan ni durkushe ina faman gurje gun pampo ba amsa xai yi ba ya taya ni, to wllh bai amsa ba sai xagina ma ni da yayi daga karshe, a xo har sashina a dinga ci min mutunci, to hirrr don duk ranan da aka isheni tattara kayana xan yi in bar gidan nan kuma sai anyi shekara duba ana nemana" Mujaheed ya d'an daga kai ya kalleta ta gefen ido ya maida kansa kasa, Abba dai bai iya yace komai ba, Anty tace "Kiyi hakuri inna, a yafe masu" Inna tayi kasa da murya tace "Wllh Amina daga nace kai kuwa Mujaheed haka kake ma Mamarka a gida ina ma magana xaka wuce, kuma fa cikin lallami nayi tambayar kawai ba sai ya sakar min aradu a kai ba, ita kuma wancan lankwasasshiyar mai kama da yar tsana bbu abinda ta mance bata gaya min ba daga nace Imaan ga maganin da na amso maki saboda ciwon ki da ba a san kansa ba ba a san dalilinsa ba, wllh Ahmadu sae kaga wanke ni da yarinyar tayi tasss har da ce min ba ruwana da ciwonta kuma ciwon ba me warkewa bane" Imaan ta fashe da kuka har da shessheka, Abba yyi mata tsawa cikin rawar murya tace "Abba xagina fa ta ke yi wai...." Abba ya dakatar da ita yace "Keep shut" ta hadiye abinda xata ce tana hawaye, Mujaheed yace "Kiyi hakuri Inna" Inna tace "Atoh ya xan yi idan ban hakura ba, dama wanda aka cuta ake ba hakuri, amma daga kai har ita kar in sake ganin kafufuwanku a bangarena, tunda kun raina ni, Isuhu da Maimuna sun ishe ni" Fada sosai Abba ya dinga ma Mujaheed da kansa ke kasa, inna sai matsar kwalla take ita a dole an 6ata mata rai, hakuri Mujaheed ya kara bata, Anty ta sa Imaan ma ta bata hakuri, mikewa Imaan tayi da sauri ta fice parlorn tana kuka, Inna tace "Sai ubansa na magana yayi ta sinne kai kamar na kirki alhalin crooo kenan ku ke gani, kar ka sake xuwa min sashi ni dai na gama magana" Mujaheed bai kalleta ba balle ya tanka ta ya mike ya fice parlorn, can kusa da wani flower ya ga Imaan durkushe tana kuka, ya dinga hararanta har ya isa wajen da take, ta mike cikin rawar murya tace "Yaya don Allah kai kaji na xage ta daxu?" Ba tare da ya tsaya ba yana ci gaba da tafiya yace "Ke ma ai ba dukan ki naga aka yi ba" Ta bi shi da kallo tana shessheka. [6/11, 12:34 PM] +234 703 570 1601: 🌟⭐ *Imaan*⭐🌟
Chapter 7 · 0% Book details