← Book details Imaan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 292

Sashe 68

Imaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ammi ta bi Imaan da kallo ganin xata shiga daki tace "Kee" juyowa tayi tana kallon uwarta ta, Ammi tace "Ajiye min plate din kika yi kika fito?" Imaan tace "Ammi na wanke wllh" Ammi tace "Toh ki tafi ki sha maganinki ki daina min wannan yatsine yatsinen da kike yi" a hankali tace "Na sha Ammi, kai na ke min ciwo da bayana" Ammi tace "Allah ya sauwake" Har Imaan zata shiga daki sai kuma ta fasa ta dawo ta xauna kusa da Ammi murya can kasa tace "Ammi don Allah idan na gaya maki abu baxa ki min fada ba?" Ammi na kallonta tace "Idan ya kama in maki fada ae dole in maki" Shiru tayi tana kallon Ammi, Ammi tace "Ina jin ki" Sauke idonta kasa ta yi tace "Dama..." Sai kuma tayi shiru, Ammi tace "Dama me?" Murya can kasa tace "Wannan mutumin da kika ji ina waya da shi da daddare shine da naje shopping mall daxu muka hadu" Marairaicewa tayi tace "Ammi wllh ban san ma ni ya siya ma ba" Ammi tace "Me ya siya maki?" Ta ja baya kadan tace "Chocolates, da abubuwan ci...." Ammi ta dinga kallonta, kafin tace "Ina suke?" Imaan na kara matsawa daga kusa da ita tace "Na kai part din inna, ina tsoron kar ki min fada" Ammi tace "Ni xa ki ma karya baki san xai siya maki ba koh??" Kamar xata yi kuka tace "Wllh Ammi ban sani ba, we just met at the supermarket" Ammi tace "Toh shi yaron a ina kika san sa?" Tace "Ai na ce maki abokin ya Muhsin ne kuma Yayan Classmate dita Mariya ce, a gidan gwaggwo muka hadu" Ammi tace "Toh yyi kyau, you had better be careful Imaan, kin san Abbanki won't take it likely with you if he should find out, ni dai kar ki ja min matsala bbu ruwana, banda shashanci ya maki yawa you ought to have known ur left from right now" shiru Imaan tayi bata ce komai ba, can ta mike a hankali ta wuce dakinta. Mujaheed na zaune parlon inna bayan ya dawo aiki ran Tuesday ita ko tana can tana shara, Imaan na kwance tana bacci kan 3 seater, tun da ya kalleta sau daya bai sake kallonta ba, bayan wani lkci inna ta shigo parlon, kakkabe kujeru ta dinga yi tana cewa "Ni dai gaskiya wannan yarinya ta Bukar tana takurani duk ta kare min kujerun sun lotse, sai dai naji kunya idan nayi manyan baki, yarinya dai kamar kyanwa kwanciya baya karewa, gashi yau laluran ciwon kafar ya tashi bata je islamiyyan ba ma, Allah ka dubi jikata ka yaye mata wannan bala'in da ba a san kansa ba, ni bari ma kwanan nan xan shirya inje in samu ta Rasulu in ji yanda xa ayi, sai dai duk abinda Ahmadu da Bukar xa su ce su ce, ai dai ba gun boka xa mu je ba" ganin ruwan kumfa inna ke kokarin kadawa Mujaheed yace "Ni dai magana na xo mu yi, ki bar wannan aikin naki da baya karewa ki saurareni" ta kallesa ce "Toh idan aiki ya kare ae kazanta ta tabbata kenan, ni ko ina xan yarda in daina aiki in mutu cikin dauda, ko kai baka ji dadi da kamshi da ka shigo parlon ba" yace "Abba nake son ki yi ma magana inna, wllh bana son tafiyar nan, ruwan garin ma ba iya sha nake ba balle abinci, kwanaki da muka je da ku har muka dawo ni ban ci abun kirki ba fa" Inna ta saki baki tana kallonsa, can tace "Toh yanxu ya kake son ayi?" Tace "Kawai ce ma Abba za ki yi xa ki aikeni kano in kai maki wani sako sai Yusuf ya kai su gaskiya" inna tace "Tohhh, yanxu kiransa xan yi kenan?" Yace "Ehh ki kirasa, sae kice masa ya min magana don kinsan in kece kika min ba xuwa maki aiken xan yi ba" Inna ta mike ta dauko wayarta tace "Toh kirasa" Dialing number Abba yyi ya sa a speak on ya mika mata, imaan sai tsaki take tana turo baki ita a dole an hanata bacci, sai dai ba wanda ya tanka ta, Abba na d'aga kiran inna tace "Yaro??" Abba yace "Ina yini" Tace "Toh lafiya lau, sae dai wuni nayi ina aiki wllh har bayan window na duk na share, na goge gilashin windon" Yace "Alhmdllh, fatan dai lafiya?" Ta gyara xama tace "Ina fa lafiya, wato kai dai ka haifa ma kanka fitina da abinda ya fi karfin ka ne baka sani ba har yanxu Ahmadu, wai dama don Allah ina ne asalin ko wani mutum dai bahaushe?" Abba yace "Ban gane ba inna" a d'an fusace tace "oh oh Allah, Asalin kowa nake tambayarka, ina ne asalina da na Ubanka?" yace "Asalin kowa kauye inna" Inna tace "Toh Alhmdllh, yanxu wannan mutumi Mujaheed ya xo ya sameni, ko gaisuwar kirki ba mu yi ba, ya fara bani sako in baka, wato cewa yyi ince maka shi baxai je kauye ba gaskiya, don kwanaki ma da mu ka je a gantale ya dawo ba abinci, har yana koya min karyar da xan maka na cewa xan aikesa kano ko uban wa gareni kano oho, wai sai Yusuf ya kai su kauyen, bai san ni yar gaskiya bace, ba a cin amana da ni, yanxu fisabillahi Ahmadu in ji kaga abinda yasa tun suna yara nake cewa ka dinga kai su can koh?" Mikewa Mujahedin da ya bude baki yyi yana kallonta, imaan ta sauko kasa ta dinga 6a66aka dariya, Abba yace "Toh yayi kyau ki kyalesa kawai, sae su tafi da Yusuf din" inna tace "Atoh, ni dai ba ruwana, ka tashi tsaye da rokan Allah kan Mujaheed" daga haka ta katse wayar ta tayi kasa da murya tana kallon Mujaheed tace "In dai ranka bai kwanta xuwa kauyen ba kada kaje gaskiya, duk bambamin da Ahmadu xai yi xuba masa na mujiya, haka kawai kaje ka cutu, don gaskiya ko ni bana cin abincin gidan hansai, to idan na ci na tsuge da xawo ya za ayi da ni???" Mujaheed ya juya a mugun fusace xai fita jin dariyar da Imaan take ya juyo ya haureta da karfi ya fice, wani ihu ta fasa ta rike kafar, inna ta mike da sauri tace "Fita ki bisa ni ba ruwana kada a dameni ya xa mu dinga magana ki mayar da mu mahaukata kina dariya" Imaan ta mike tana kuka sosai ta fita parlon tana dingishi ta wuce part din su, Ammi ta fito kitchen da sauri, Tace "Lafiya, me ya faru?" Cikin kuka tace "Yaya ne ya haure min kafar dake min ciwo da karfi gashi yanxu ya rike Ammi, Wllh ban masa komai ba" tana fadin haka ta xube kan kujera tana kuka sosai, Ammi ta karaso tana kallon kafar, har gun ya tashi yyi ja, Hijab dinta ta dauka ta sa ta fita parlon bata xame ko ina ba sai bangarensu, Yana xaune dinning takaici ya ishesa Anty kuma na kitchen da su Maimoon. Nan parlon Ammi ta tsaya tace "Mujaheed me Imaan tayi maka ka haureta a kafa?" Kallonta yyi ya dauke kai bai ce komai ba, ta karasa dinning din fuska daure tace "Tambayar ka nake malam, ka fara hauka ne xaka haureta a kafa, to Wllh even by mistake kada ka sake don zan dau mummunan mataki a kanka" Anty ta fito kitchen da sauri tace "Lafiya Hajiya Aisha?" A fusace Ammi tace "Wllh ku ja masa kunne ya fita harkar Imaan a gidan nan, duk ranan da ya sake gangancin ta6a lafiyarta xa ayi tashin hankali a gidan nan, haka kwanaki ya mareta na kai xuciya nesa ban ce komai ba, to this shud be the last, kada ya sake idan ba haka ba wllh sai na rama mata" Hakuri Anty ta dinga bata, Mujaheed ya mike ya wuce sama ba tare da ya sake kallonta ba, Ammi ta nufi kofa xata fita suka kusa cin karo da Umma xata shigo sun dawo anguwa da Rahma, ko kallonsu bata yi ba ta fice, tana komawa dama daki ta shiga ta dauko man xafi ta fito ta shiga shafa mata a gun, Imaan ta dinga yarfe hannu tana kiran daddy, bayan Ammi ta daina shafa wa a hankali tace "Ammi xuwa kika yi gun yaya?" Ammi tace "Baxan je ba ko shi ya haifa min ke?" Imaan na kallonta tace "Fada kika masa" Ammi tace "Abinda ya fi fada ma" imaan ta zaro ido tana kallonta, can tace "Ni da baki je ba Ammi ni ne fa nake ta masa dariya...." Da gudu ta mike bayan ta kauce marin da Ammi tayi niyyar sauke mata, ta wuce daki tana turo baki ta kulle kofar ta sa key, tana jin Ammi na cewa "Xaki fada min ko kanin ubanki ne yayan, daga yau ma kika sake xaunawa inda yake wllh sai na kakkarya ki a gidan nan" Inna ta saki baki tana kallon Mujaheed har ya gama, tura tuwon gabanta tayi tace "Ba lafiya, ita Aishar? To yaushe ta xama haka, atoh gaskiya imaan dai ta zama yar jaraba tunda akan ta uwarta taje tana maka bala'i, wato Allah kadai yasan abinda yarinyar ta tsara ma uwar, saboda irin wannan halayyar tata yasa aka rasa gane kan ciwonta fa har yau, to meye kuma yarinya karama da hada gurmi a gida, ae da sai kace ma Aishar A'a ni ba ruwana baxan yi fada da ke ba don kin haifeni, ai ke kusan sa'ar uwata ce, to kawai kuma sai ka tsaya kallonta kayi shiru" Mujaheed yace "Ni baxan ce mata komai ba ko sbda daddy, amma ta sake min haka a gidan nan gaskiya sae dai duk abinda xae faru ya faru" Inna tace "Ni ko sai naje na sameta wllh" da sauri Mujaheed yace "A'a kar ki ce mata komai" Inna ta ja tsaki tace "Ba dole in sameta ba xata sa ka gaba tana jaraba a kan figaggiyar yarinya mai hada gurmi" tana fadin haka ta fice parlon, Ammi na shafa ma Imaan man xafinta a kafa Inna ta shigo ba ko sallama, Ammi ta mike tace "Sannu da xuwa inna"
Chapter 68 · 0% Book details