← Book details Imaan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 184 OF 292

Sashe 184

Imaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

har ya isa kofa, sai kuma ya juya ya kalleta, da sauri ta rufe idon, har xai fita sai kuma a hankali tace "Sai da safe" Yana kallonta yace "Allah ya tashe mu lafiya" daga haka ya fita ya rufe kofar. Washegari aka sallami Imaan karfe sha daya na safe, Stepmum din Sadeeq da su Suhaila ne suka kai ta har gida, Ammi tayi masu godiya tare da Aunty, basu wani jima a gidan ba suka wuce tunda tare suke da driver. Bayan sati daya da yayi dai dai da saura sati guda a kawo lefen Imaan.... Umma ce xaune makeken parlon gidan Bulasawa tare da Hajiya Balaraba sai Safeenah da ta ke ta taunan cingam ta ci kwalliya iya kwalliya tayi kyau, ba don Suhaila da ta gansu bakin gate a tsaye ta dawo boko a motarta ba da babu yanda xa ayi a barsu su shigo gidan don masu gadi sun ce ba a sanar da su xa ayi bak'i ba, ynxun ma sun fi minti sha biyar xaune parlon suna jiran fitowar uwar gidan Bulasawa, duk sun yi shiru kamar masu xaman makoki, can dai Hajiya Saude na kallon Umma murya can kasa tace "Anya shawarar nan tayi kuwa Hajiya Rukayya??" Umma na kallon Safeenah tace "Ni ban kawo hakan a kai ba fa, sai da Safeenah ta kawo shawarar, kuma jikina ya bani da nasara...." Safeenah ta tabe baki tace "Ku dai ba ni nace ayi haka ba?? ku kwantar da hankalin ku kawai, na fa san abinda nake, haka kawai ga hanya mafi sauki kuyi ta kai ma katti kudin ku suna cinyewa, har yanxu ban ga alamar abun da ake ta ce maku ba gashi saura sati a kai lefe a sa rana, ga dai hanya straight...." Umma tace "A'a wllh babu me cinye min kudi, ana biya min bukatata yanda ya kamata... So nawa kuma??" Shigowar Mummy parlon sanye da hijab har kasa yasa duk suka yi tsit, kallonsu ta dinga yi har ta karaso ta xauna saman kujera, Umma na murmushi tace "Sannu da fitowa Hajiya" Mummy tace "Yauwa daga Ina?" Umma tayi yar dariya tace "Lahh, baki gane ni ba Hajiya??" Mummy dai sai kallonta take don sarai ta gane ta, can kuma ta girgixa kai tace "A'a ni ban gane ku ba, daga Ina?" Umma tace "Toh ni dai sunana Hajiya Rukaiya, in dai kina jin Barrister Ahmad Yusuf na nan kaduna to Mai gidana ne..." Mummy bata daina kallonta ba tace "Ohk..." Umma tayi kasa da murya tace "Hajiya a matsayina na yar uwar ki musulma na xo maki taimako albarkacin musulunci..." Da mamaki Mummy tace "Taimako kuma? Wani irin taimako nace maki ina bukata??" Umma ta gyara xama tace "Hajiya don nace na xo maki taimako ba ina nufin kudi ko wani abu gareni da xan baki ba don kin fi karfinsu, amma ki sani wllh wllh taimakon nan sai ya fi maki kudi ko wani abu na kyale kyalen rayuwa... Hajiya kin san shi aure ba abu bane da xa ayi na rana daya a gama ko na wata daya, A'a rayuwa ce da ake fata ya xama na har abada, kin ga wannan yarinyar da d'an ki ke nema??" Ita dai Mummy kallonta kawai take, Umma tace "Toh wllh wllh kin ji rantsuwar musulmi sickler ce, sannan kin ga yanda kika ganta ita kadai, to har gun iyayenta ita kenan takk... uwar ta fi shekara 13 bata haihu ba, kafin daga karshe taje ta san abinda ta yi Allah ya bata yar, wanda da Allah ya tashi kamata ya hadata da sickler, har yau kuma wllh tllh uwar ta hana uban karin aure kiri kiri, sannan babu wanda bai san abinda take ba, daga ita sai yar suke yanda suka ga dama a daulan uban, matar kanin mijina ne uwa daya uba daya, kin ga dai ba kishiyata bace ita balle ace ina ma 'yar ta bakin ciki, ko daya wllh ba haka nake ba, gaskiya ce duk inda take sai na fade ta, yanxu haka maganar da nake maki d'an kishiyata Yusuf ni ce kan gaba gun nema masa aure gidan Alhaji Mukhtar Kiyawa da kika sani dai na nan garin, wllh wlh mahaifiyar yarinyar nan ba mutuniyar kirki bace muguwar bafillatana ce ta karshe, kije anguwar mu malali ki shiga gidajen layinmu kaf kiyi tambaya a kanta xa ki sha labari, tayi kadan in mata hassada wllh balle ace ko hassada nake mata, Bari ki ji Hajiya wllh a ta dalilin ta Mai gidana ya min kishiya, ta cusa masa aminiyarta ina ji Ina gani ta aure min miji, ita kuma taki barin a mata kishiyar har yau gashi ba haihuwa take ba, ita ma kuma ita kenan gun uwarta, sae gashi ta haifi kwaya daya ita ma, kakar yarinyar ma gwaggwo ita kadae iyayen suka haifa aka ce, kamar yanda baxan so Mujaheed da abinda xai cutar da shi a rayuwa ya xame masa wahala ba haka baxan so ma duk wani matashi ko da ba ni na haifesa ba, a wata wllh uban yarinyar na kashe mata kudi ya fi dubu dari biyu, kullum cikin abu daya ake idan ciwon ya matsa mata kuwa ke kya ce baxata yi ba, shi sa nayo tattaki in sanar maki ki ceci d'an ki, barin ma shi da yake d'an ki na fari....."
Chapter 184 · 0% Book details