← Book details Imaan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 109 OF 292

Sashe 109

Imaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da addare Imaan na kwance parlon Inna dake xuba wani garin magani a kindirmon dake cikin cup din gabanta, Maimoon ta shigo da sallama ta ajiye abincin hannunta ta gaida ta, Inna ta mika mata cup din tace "Mika ma waccan matar" Imaan ta juya masu baya da sauri tana turo baki, Inna ta kalli Maimoon tace "Kinga walakanci ko, wannan wace irin yarinya ce don Allah, ta san daga inda maganin nan ya fito?" Imaan tace "Ni nace maki na sha magani fa a gida, ya xa ayi in hada magani iri biyu" Inna ta ajiye spoon dina hannunta tayi tagumi tace "Oh waannan 'ya ta Bukar dai jarababbiya ce wllh, Toh meye da maganin da baxata sha ba? Ba daci, ba 6auri, ba hamami, ba galmi sai ma gyara mata bakin ta da xai yi, ta ji dadi kuma a jikinta, to ni dai ba ruwana gashi can uwar ki da ubanki sun fara laka maki ciwon da ba a san ki da shi ba ba a san kansa ba, wai dama idan lkcn gabatar da yaro ya kusa ba duk iccen da aka jika ma yaron aka basa sai ya amsa ya sha ba sbda a kauda ikon makiya, Ni dai ba ruwana Ina taimakon ki kina min wlknci, idan ta uwarki ce sai dai fa ki mutu ba abinda xata maki, shi kuma Bukar na can na neman na abinci a Habuja, to wa gare ki banda Allah sai ni din, to ni ba ruwana, ki tashi ki amshi maganin nan ki sha ni ba asararriya bace, uwata bata ce min jeki kya gani ba da xan dinga maki bauta baki gani, ko ubanki bai samu haka a guna ba" Maimoon ta ajiye cup din hannunta ganin imaan ta ki amsa tace "Inna ni dai xan je inci abinci" Inna tace "Toh idan kin gama ki dawo kema ga naku da su fitsararrun can Ummi, ba dai don halinsu ba, ya xanyi tunda ni na haifi Ahmadun" Maimoon dai bata ce komai ba xata fita sai ga Mujaheed ya shigo parlon, gaishesa Maimoon tayi ta fita, Inna tace "Mujaheed waya dai ko sama ko kasa, an dai rasa wanda ya sace, ni na ma fi xaton hauro kantangar aka yi, ai daga yanxu ni kaca ma xan dinga sawa in rufe kofar da kwado idan xan fita, Ina dalili? Ai ko ya daukan ma kansa fitinar duniya" Mujaheed ya gaisheta sannan yace "Za a xo daukan akwatunan nan" Inna ta kallesa sannan tace "Ita da ta turo ka ba sai ta xo ta kwasa ba in ga, Rukayya dai tayi hankali da ni ba ruwana.... Wannan yarinya kuma kayi mata magana ta rufa min asiri ta dau nonon nan ta sha ba sato kudin nake yi ba, dubu goma kenan cikin kofin a kwance ta rasulu ta sa aka amso min" Mujaheed bai ko kalli imaan ba yace "Kaya xa a karasa xubawa cikin akwatunan shi sa xa a dauka" Inna tace "Sai kuma ka yi ai, ko Ahmadu bai isa yace xa a dau akwatunan nan ba balle kai" Kallonta ya dinga yi fuska daure, can ya juya ya fita. Washegari da safe Mujaheed ya shigo parlon Abba da sallama ta dalilin kiransa da yayi a waya, Abba na kallonsa yace "Jikin Imaan ya matsanta mata, yanxu Hajiya Aisha ta kirani..." Mujaheed yace "Toh a tafi asibiti kawai" Abba yace "Toh xa ka kai ta ne?" Girgixa kai yyi yace "Zaria xan tafi Abba, kuma likitan ta na gari ai" kallonsa kawai Abba yayi bai ce komai ba, Mujaheed yace "Xan je in shirya yanxu" Abba yace "Ohk then" Juyawa yayi ya fita parlon. Sai kusan la'asar Ammi da Aunty suka dawo asibiti da Imaan, nan parlor Imaan ta kwanta Ammi ta shiga kitchen don girka mata light food ta ci, Imaan ta jawo wayar Ammi dake vibrate kusa da ita ta kalli screen din, Sadeeq ta ga ke kira, sai da ya kusa katsewa ta daga da kyar ta kai kunne tayi masa sallama, ya amsa yace "Kun dawo gida ne?" Tace "Um..." yace "Ohk before magrib xan kawo maki drug din, but I have to see wanda aka baki a asibiti" tace "Toh" yace "Allah ya kara lafiya" a hankali tace "Ameen" yace "Do you need anything" tace "A'a" yace "Sure?" Ta gyada kai kamar yana ganinta, yace "Ohk sai na xo" daga haka ya katse wayar. Karfe shidda saura Yusuf ya shigo parlon da sallama, Imaan na xaune bayan tayi wanka ta shirya tana cin farfesun kayan ciki da Ammi ta mata, xaunawa yyi ya sakar mata murmushi yace "Sannu, ya jikin?" Ta mayar masa murmushin tace "Da sauki ya Yusuf" yace "Toh Allah ya kara lafiya, Ammi fa?" Imaan tace "Ta shiga daki" Yace "Ohk, me xa a kawo maki na marasa lafiya" ta kallesa ta marairaice tace "Kawai awara nake son ci" ya d'an buda ido yace "Awara?" Ta gyada masa kai a hankali, yyi murmushi yace "Toh bari a nemo maki" mikewa yayi yace "Anjima xan taho maki da shi, ki gaida Ammi idan ta fito" tace "Toh" daga haka ya nufi kofa ya fita, ko minti biyar ba ayi da fitansa ba sai ga kiran Sadeeq, sanar mata yyi yana waje tace "Toh ka shigo" Sadeeq ya d'an buda ido yace "Ni fa Ina jin kunyar Ammi" Murmushi tayi tace "Ae tana daki" Yace "Uhn toh gani nan shigowa" ajiye wayar tayi bayan ta katse, ta mike ta wuce dakin Ammi ta sanar mata Sadeeq xai shigo, Ammi tace "Toh haka xaki tsaya babu hijab" ta girgixa kai tace "A'a xan dauko a daki yanxu" Ammi tace "Ohk" daga haka Imaan ta fita ta shiga dakinta ta dauko hijab ta sa ta dawo ta xauna xata rufe farfesun gabanta yayi sallama bakin kofa, ta kalli kofar ta amsa sallaman sa, ya shigo parlon, sunkuyar da kanta tayi ya xauna saman kujera ya ajiye ledan hannunsa a kasa yana kallonta yace "Sannu Imaan, ya jikin?" d'an murmushi tayi tace "Ina yini" yace "Lafiya lau, Ina drugs din da suka baki a asibiti" mikewa tayi ta nufi daki ya bi ta da ido, ta dawo rike da ledan drugs din, ajiye masa tayi a kusa da shi, sannan ta koma ta xauna, yayi murmushi ya dau ledan ya fiddo Magungunan yana dubawa, can ya mayar da su, ya dau karamin ledan da ya shigo da ya ciro drugs biyu yace "You can take this also ba komai, na rubuta prescription din a jiki" ta gyada masa kai ya ajiye maganin, ya ciro wani na tube yace "Wannan ma ki dinga shafawa a duk inda kike jin pain" Imaan tace "Toh..." Ya d'an bude ido murya can kasa yace "Ko in shafa maki dear?" Xaro ido tayi ta kallesa sai kuma ta boye fuskarta a kujera, murmushi kawai yake yana kallonta, ganin ta ki dagowa yace "Toh baki cinye pepper soup dinki ba" a hankali ta dago tace "Ko xaka ci ne?" Yayi murmushi yana shafa beard dinsa yace "Ai baki bani ba" daukan bowl din tayi ta kai gabansa ta ajiye, ya xaro ido yace "I am only joking" tace "Ae sai ka ci" yace "Plss ki dauke, wllh wasa nake maki I am okay" ta make kafada tace "Ai kace ban baka ba to gashi ynxu na baka" ya wani xaro ido yace "Kar Ammi ta fito ki dauka plss" cike da shagwaba tace "Sai ka ci" yace "Ohk ohk idan na ci xaki dauke" tana murmushi tace "Ehh" yace "Toh dago min" daukan bowl din tayi ta rike da hannu biyu ta durkusa gabansa tana kallonsa har sannan tana murmushi, ya lumshe ido ya bude ya dau spoon din ya dau nama guda daya yayi kamar xai bata a baki ta koma baya da sauri, bakinsa ya kai spoon din ya ci, ta wara ido tana kallonsa, ya lumshe ido yace "It's sweet" dariya ta fara yi kasa kasa tace "Ashe kai ma ka iya kwadayi" da sauri ya bude ido, ta koma ta xauna still tana dariya, murmushi yyi yace "Ai xan rama" ta buda masa hannuwanta tace "Ko dai ka rame" kallonta kawai yake affectionately, ta turo baki tace "Ni dai ka daina kallona haka" dauke idonsa yyi yana murmushi yace "Watarana xaki yi bayanin me yasa xan daina kallonki" bude kofar parlon aka yi duk suka juya, daddy ne ya shigo parlon da jakar laptop dinsa Mujaheed na bayansa rike da traveling bag dinsa, imaan ta wara ido ta mike da sauri tace "Daddy" murmushi ya sakar mata, tana son xuwa ta rungumesa amma ta kasa saboda Sadeeq, ta isa gabansa cike da farin ciki, a hankali tace "Sannu da dawowa Daddy, baka ce min yau xaka dawo ba" Daddy ya shafa kanta yace "I just decided to come back and check on you daughter, how are you feeling now" tace "Da sauki sosai Daddy, har na ci abinci ma" amsan ledan hannunsa tayi, ya karasa parlon yana kallon Sadeeq kamar yanda Mujaheed ma ke kallonsa, Daddy na murmushi yace "Sadeeq" Sadeeq yyi kasa da kai yace "Sannu da dawowa Abba" Daddy yace "Thanks son, ya aiki" Sadeeq yace "Alhmdllh" Daddy yace "Ya Mai jikin?" Sadeeq yace "Alhmdllh she's getting better" Daddy yace "Maa sha Allah" Kallon Mujaheed Sadeeq yayi yace "Barka da yamma...." Mujaheed yace "Thank you" Ajiye jakar hannunsa yayi yana kallon daddy yace "Allah huta gajiya Abba" Daddy yace "Ameen son" imaan dai ko kallonsa bata yi ba kamar yanda shi ma bai ko kalleta ba ya juya ya nufi kofa, Daddy ya wuce bedroom dinsa, mikewa Sadeeq yayi yana kallonta yace "Kin ga kunyar da naji" dariya imaan tayi tace "Kunyar me? Sadeeq na shafa kai a hankali yace "Kunyar Abba mana" Imaan tayi murmushi bata ce komai ba, yace "Ki gaida min da Ammi, let me get going now" a hankali imaan tace "Toh nagode, Allah ya tsare" yace "Ameen dear, Allah ya kara lafiya, and plss kar kiyi wasa da drugs din ki" Ta d'an yi murmushi tace "In sha Allah" yace "Toh baxa ki rakani ba" tace "Toh xan raka ka bakin kofa" yace "Noo bakin mota dai plss my dear" tace "Toh idan na fadi a hanya
Chapter 109 · 0% Book details