← Book details Imaan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 292

Sashe 30

Imaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A fusace Mujaheed ya juya ganin Imaan na bin sa yace "Kee Why are you following me?" Ta xaro ido tace "Ni ba gidanmu xan tafi ba toh??" kwafa yyi ya ci gaba da tafiyarsa tana kai wa bangarensu ta shiga tana dariya kasa kasa. Sai kusan karfe biyar Farida ta fito bangaren inna bayan ta cikata da abun arxiki, su sabulai, omo, malt har da bottle water duk ta xuba mata a leda, Inna ta rakota har bakin kofa tana cewa "Toh sai ki gaida iyayenki kinji, Allah maki albarka, nagode nagode, naji dadin turaren da kika kawo min duk da dai ba mai tsada bane, sai ayi ta hakuri da Mujaheed dai, Allah kuma ya nuna mana lkcn abun arikin nan" murmushi kawai Farida take ta wuce tare da Maimoon dake rike da ledan da inna ta bata, sai da suka isa bangaren su Imaan tace "Bari na shiga in duba imaan" Tare suka shiga parlon da Maimoon, imaan dake kwance tana kallo ta mike xaune tana murmushi tace "Har xa ki tafi Anty farida" farida tace "Eh xan wuce ya jikin fa?" Imaan tace "Ae na ji sauki" Farida tace "Toh Allah ya sauwake xan fito daxu inna tace kun tafi asibiti da Mujaheed" dariya imaan tayi tace "Ni dai naji sauki" farida tace "Toh ki dinga yawo da inhaler din ki amma" Imaan tace "Toh nagode" Ammi ta fito daga daki tace "Har xa ki tafi Farida" farida tace "Ehh Ammi yamma yayi" Ammi tace "Toh mun gode da ziyara, ki gaida mamarki da mutan gidan kin ji" farida tace "In sha Allah xa su ji" body spray uku Ammi ta sa mata a leda, ta amsa tana godiya suka fita tare da Imaan da ta sa hijab xa ta rakasu, xaune suka tadda Mujaheed a part dinsu kusa da parking space a kan farin kujera idonsa a kan wayar hannunsa, farida na daga inda take ta gaishesa ya kalleta sannan ya mike yace "Why did you come without telling me?" ta d'an buda ido tace "Saboda baka son inna ta bani labarin ka? To yau duk naji komai" Dariya Maimoon tayi har da imaan ya watsa masu wani kallo fuska daure, Farida tayi murmushi tace "Kawai na xo anguwar ne shine nace bari in karaso in gaida inna" yace "But da rana ai mun yi waya kuma baki ce kina anguwar ba" tace "Noo ban taho ba lkcn, nima fa ban san ma xan fito ba, I came on an errand for my mum" Kamar ance Mujaheed ya daga kai ya ga Ummar sa tsaye a balcony na sama tana kallonsu keenly, farida ta kalli sama ita ma, ganinta ta sunkuyar da kanta, murya can kasa yace "I think you have to go in ku gaisa tunda ta gan ki" Tace "Toh" imaan tace "Toh Anty farida sai wani lkci xan amshi number dinki gun yaya idan xai bani" ta gefen ido ya harareta, farida tace "Toh shi kenan imaan na gode sosai" Daga haka ta wuce Maimoon tayi leading din farida xuwa parlon Umma, Umma na xaune wayar ta a hannu suka shigo, Farida ta durkusa kasa tana kallonta tace "Ina yini Umma?" Murya can ciki umma tace "Lafiya lau" Farida na wasa da fingers dinta tace "Ya aiki umma" umma tace "Alhmdllh" shiru farida tayi, Maimoon dai na tsaye sai tabe baki take, Umma tace "Ya 'yan gidan naku?" Farida tace "Suna lafiya" Umma tace "To yayi" bayan kusan minti biyu farida ta mike tace "Toh xan koma umma nagode" umma tace "Toh a gaida gida" daga haka ta fita Maimoon na biye da ita, dakin Anty suka shiga, Anty taji dadin ganin ta, bayan sun gaisa ta tambayeta mamarsu farida tace "Suna lafiya Anty" Da ta tashi tafiya Anty ta bata dubu daya kudin transport, Maimoon ta amsar mata don kin amsa tayi suka fita dakin Anty, Mujaheed na tsaye parking space suka fito gidan, bayan sun iso inda yake yana kallon farida yace "Gida xa ki koma yanxu?" Tace "In sha Allah" yace "Ohk mu je in ajiye ki" har ya bude mota wayarsa ya fara ring, ya duba yaga umma ce ke kiransa, a hankali ya daga ya kai kunne, Umma tace "Ina jiran ka parlor yanxu" yace "Toh" daga haka ta katse wayarta, ya kalli Farida a hankali yace "Bari in baki transport kawai dear, akwai aikin da xan yi yanxu" daga haka ya fiddo dubu biyu ya mika mata, ta girgixa kai tace "A'a ka bar shi I have transport thanks" ya mika ma Maimoon yace "Ki bata plss" Maimoon ta amsa, yana kallon faridar yace "Sai mun yi waya dear" daga haka ya wuce ciki. Maimoon ta tabe baki tace mu je Anty farida. A hankali Mujaheed ya bude kofar parlon Ummarsa ya shiga da sallama, tsaye ya sameta ta rungume hannu tsakiyar parlon wandering about, ya karasa yace "Umma gani" kallon da ta dinga masa ya sa ya durkusa ya sauke kansa kasa, tace "Mujaheed dama ban raba ka da wannan yarinyar ba?" Ya kalleta da kyar yace "Umma ni ban fa san da xuwanta gidan ba, kuma...." Sai yayi shiru, Fuska a murtuke tace "Kuma me?" Yace "Umma don Allah me yasa baki so na da farida?" Tace "Ra'ayi! Wato dai har yanxu kuna tare duk jan kunnen da na maka kwanaki koh? To wllh ka kiyaye bacin raina Mujaheed, ka kiyaye ni a gidan nan, uban me xaka yi da diyar talakawa ka ja min bala'i, in xama abun magana gun kawayena, duk fadin kaduna ka rasa budurwar da xaka nema sai wannan yar, warce iyayenta ke xaune a ghetto ? Haba Mujaheed are you even alright?" Yace "But Umma I see nothing wrong with that, arxiki fa na Allah ne, beside suna da rufin...." Umma ta dakatar da shi rai bace tace "Da ca nayi arxikin na kanin ubanka Sadeeq ne? Ni xaka ma wa'axi? To wllh in dai kana son kwanciyar hankalin ka a rayuwa ka fita harkar yarinyar nan, su je can su samu wani kuma, abubuwan alkhairi da ka dinga masu a baya da ciyar da su da ka dinga yi Allah ya saka maka da alkhairi, ina ji ina gani baxa ka auri yarinyar nan ba ka xama mai bada charity su talautar min da kai, yarinya dai dai class dinka in sha Allah xan samo maka tunda naga ba saiti gareka ba, ba abun mamaki ba wataran ma ka xo min da yar talla kace ita kake so, kai ko kunyan kanka ma baka ji, dubi yarinyar da Yusuf yake nema xar sha'awa yar masu kudi ta ma fi ubansa kudi shi ne kai xaka makale ma yar ghetto ko, to wllh ka guji bacin raina a gidan nan, sannan don munafurci da kinibibi ta shigo sumui sumui ta nufi gun alakakan kakarka da ba so na take ba a gidan nan salon duk ta bata ni gunta ta hure mata kunne, don wllh da ban ganta a sama ba dama bata yi niyyar shigowa gaida ni ba, ta kama ta tafi gun kakarka da kanwar uwarka Aisha tunda ita ta haife ka, Allah kadai yasan me kakar taka ta k'itsa mata, wato Mujaheed tarayyar ka da yarinyar ba abu bane mai yiwu wa samm kayi ta kanka tun wuri, daga this very moment na raba ka da yarinyar na har Abadan abidina, tashi ka ban waje mara tunani kawai" mikewa yayi bai ce komai ba ya nufi kofa ta bi sa da harara har ya fita ya kulle mata kofar ta. Xaune yake cikin Lafiyayyen motarsa nesa da gidan, abokinsa dake gefensa yace "Look ni fa na gaji da xaunar da ni da kayi cikin mota tun daxu Sadeeq..." Sadeeq ya shafa cute Beards dinsa a hankali yace "You just chill Fahad... jikina na bani xata fito soon" Tabe baki abokin yyi yace "Have you changed ur mind about loving and dating only whites?" Sadeeq ya xaro ido yace "Of course No, wannan fa yar yarinya ce.... I think she is not even up to 18, she is....." Sai kuma yyi shiru yana murmushi, Fahad da ya saki baki yana kallonsa yace "Sweet eighteen kenan" Yar dariya Sadeeq yyi a hankali underneath his breathe yace "she is beautiful" Fahad yace "and why didn't you callect her digit?" Wani kallon gefen ido yyi masa yace "Sai kace nine kai? How on earth xan amshi numberta bata ce in bata nawa ba" Bude gate da suka ji aka yi yasa duk suka daga kai da sauri, Mujaheed ne ya fito, walking majestically ya nufi motarsa da yyi parking a waje. Imaan na xaune bakin kofar kitchen tana ta yi ma Amminta dake girkin dinner hira, Ammi tace "Daxu inna ta xo fa wai tana nemanki idan kin dawo schl" Imaan ta xaro ido tace "Ni??? Ba ruwana baxan je ba, ce ma Abba tayi fa kar in sake xuwa mata ina kwasan maganganunta ina yadawa a gidan nan, ita gaskiya xata gudu ta bar gidan idan naje mata" Ammi tayi murmushi tace "Toh tace kwana biyu bata gan ki ba ko jikin ne" Imaan tayi dariya tace "Xa ma ta fadi gaskiya ne, ba inda xanje ta sake cewa na mata laifi gwara dai Maimoon ta ci gaba da xuwa tana kai mata abinci" Ammi tace "Toh ke xa ki kai yau, kina ajiye mata ki gaisheta sai ki fito ba shi kenan ba" imaan ta bata fuska kamar xata yi kuka tace "Ni dai Ammi nayi alkawarin baxan sake xuwa part dinta ba fa" Ammi dai bata ce mata komai ba. Bayan magrib Imaan na Idar da sllh Ammi ta tilastata kai ma inna abinci sabanin Maimoon da ta dinga xuwa tana kai mata kusan kwana uku kenan, Imaan ta dau abinci ta fita fuska daure kamar mai shirin yin kuka, tana isa bangaren inna ta tura kofar ta shiga, Yusuf ne parlon suna hira, Inna na ganinta ta washe baki tace "A'a takwara ce" imaan ta ajiye abincin ba tare da ta kalleta ba tace "Ina yini?" Inna tace "Lafiya lau, ni kwana biyu ban ganki ba nace to ko jikin ne? Duk hankalina ya tashi na tafi sashin ku daxu Aisha tace ai kin ma tafi
Chapter 30 · 0% Book details