Sashe 221
Imaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abba ya kalleta yace "Allah ya kyauta, xa mu xuba ido mu ga inda matsalar yake kafin a dau mataki" Inna tace "Atoh dai nima haka nace a hankali xa mu bi komai har mu gano gaskiya, ba wani gaggawa" shi dai bai ce mata komai ba, tace "Toh wai ni jama'ah ina xancen jikana ne, tun jiya fa har yau shiru, ko gidansa xan dau mayafi in tafi?" Abba yace "Daxu mun biya gidan baya nan" salati Inna ta saki tana kallonsa tace "Toh me ya samesa?" Mama Hadiza tace "Gun aikinsa fa?" Abba yace "Sadeeq ya je baya nan" cike da damuwa Inna tace "Toh anya lafiya kuwa??" Mikewa Abba yyi shi ma dai duk abun ya damesa sosai, yace "Bari in tafi masallaci Inna" daga haka ya fita parlon yana tunanin to Ina Mujaheed xae tafi tun jiya. Daren ranan Inna ta fito tsakar gida tana salati tana kiran Abba da karfi, Daddy ne ya fito part dinsa ya sakko yana tambayar me ya faru, Ko saurarensa bata yi ba balle ta kallesa ta karasa part din Abba tana kwalo masa kira, Yusuf ne ya fito parlon Aunty na biye da shi, yace "Lafiya Inna? Me ya faru" Daga sama har kasa ta kallesa tace "Kai rabu da ni, kai ne Ahmadu, ni ba duk xatona kana gun amaryarka ba ashe kana gidan nan har yanxu baka shigo ka min jajen abinda ke faruwa ba...." Ganin Abba tace "Wllh Ahmadu na kasa gane kan Imaan, abinci fa na tilasta ta ci sai gashi ta dinga amai kamar xata mutu ga jikinta duk xafi kamar garwashi, ka ga dai yanda nake tsaye kyam to bata iya tsayawa haka, kada wani cuta ya kamata fa in shiga uku ka taho mu je ka kaita asibiti, a gaskiya bata da lafiya sosai wllh" shi dai Daddy na tsaye bayanta yana kallonta, Abba yace "mu je to" daga haka ya fara tafiya Inna ta bi bayansa Aunty da yusuf na biye da su, kafin su je har Mama Hansai ta kintsa Imaan da duk ta wani langwabe, Abba yasa ta sa hijab suka wuce asibiti.... Daren ranan asibiti Imaan ta kwana tare da Aunty sbda karin ruwan da ake mata, tausayinta sosai Aunty take ji don abun ya hade mata biyu ne, ga heartbreak ga kuma unexpected marriage, ga shi duk ta wani rame, wajen karfe daya Imaan ta farka daga baccin da take, Aunty dake xaune kan farin kujera ta jinginar da kanta da gadon ta dago jin motsin ta, mikewa tayi tace "Sannu Daughter, ya jikin?" Imaan ta kamo hannunta lkci daya hawaye ya kawo idonta cikin sanyin murya tace "Aunty don Allah baxa ki taimakeni kiyi ma su Abba magana su yi hakuri kada su ce ya Mujaheed ya aureni ba??" Aunty na kallonta da tausayi tace "You need much rest imaan ki kwanta ki yi bacci ko na hada maki shayi?" Imaan ta girgixa kai hawaye na sakko mata tace "Aunty kice wani abu plss" Aunty tace "Imaan meye da Mujaheed din da baki son auren sa?" Imaan ta xaro ido tace "Aunty yayana ne fa" murmushi Aunty tayi tace "Eh yayan naki, ae da aure tsakanin ku ko, Mujaheed is good ba shi da wani flaws da xai sa ki daga hankalin ki, ke da ma kika fi kowa sanin sa, kinsan halinsa ya san naki so what more, in just few days time da xa ku yi tare am telling you sai kun gode ma iyayen ku da suka hada ku aure, but wait ynxu ki gaya min me yasa baki son auren, amma kada ki ce min yayan ki ne, don ke kika laka6a masa wannan matsayin, tell me yana da wani abu ne da ba ki so" ta fashe da matsanancin kuka tace "Wllh Kunyan sa xan dinga ji Aunty, ni kunya nake ji...." Sosai ta ba Aunty dariya, Aunty ta rungumeta tana murmushi bata dai ce komai ba, cikin rawar murya Imaan tace "Allah kunya xan ji Aunty" Aunty tace "Toh ki kwanta yanxu ki huta sosai, gobe sai mu yi magana" da haka ta lallaba ta ta kwanta, amma imaan bata yi bacci ba daren ranan, da ta tuna wai ynxu Mujaheed fa mijinta ne sai taji kamar ta bace duniyar gaba daya da wannan abun kunyan kawai, washegari sai da rana aka sallamosu suka dawo gida. Sadeeq ne durkushe gaban Mum dinsa dake xaune tana kallonsa da mamaki, ya hade kansa da kneels dinsa hawaye na sakko masa yace "Mummy I don't know what just came over me, don Allah ki tausaya min ki ba Abbana hakuri ya sami iyayen Imaan ya basu hakuri I cant imagine loosing her, don Allah ki taimakeni ki masa magana ya same su sai a daura mana auren" Mummy tace "Anya kana da hankali kuwa Sadeeq??" Ya dago kansa yana kallonta hawaye na sakko masa yace "Sure mum, ni ban san me yasa nayi abinda nayi ba, help me speak to dad plss" mummy tace "Kaje ka samesa da kanka Sadeeq I won't invole my self coz har ynxu ur Dad is angry with me bcos of what u did" tashi yyi ya nufi kofa ta bi sa da kallon mamaki don tun shekaranjiya sai yau ya shigo gida kamar an jefo sa, mikewa tayi duk jikinta yyi sanyi sosai tana tunanin to me ya sami son dinta, ita tun farko tasan ba yin kansa bane fasa auren nan da yyi, then who is after her son? Waye yyi masa haka? Girgixa kai tayi tace "I will surely find out...." Tana fadin haka ta fita dakin. Inna na xaune parlonta ta sa Mama Hadiza gaba bayan Magrib wai sai ta samo mata layin Mujaheed kawai ita dai, Mama Hadiza ta kira for the third time da damuwa tace "A kashe fa wayar yake Inna ba a kunna ba har ynxu, gashi kina jin ance switched off" Inna ta xaro ido kamar xata rusa kuka tace "Anya Hadiza Mujaheed ba kashe kansa yaje yayi ba kuwa??" Sai kuma ta fashe da kuka tana kallon Mama Hadiza tace "Da mun shiga uku mun lalace" Mama Hadiza ta hade rai tace "Haba Inna ya kashe kansa a kan me kuma?" Sallaman da suka ji bakin kofa yasa duk suka yi shiru, Imaan dake kwance daki duk tana jin su ta mike xaune da sauri xuciyarta na bugawa jin muryar wanda yyi sallaman, Inna ta kalli Mama Hadiza tace "Waye kuma wannan yake min sallama?" Mama Hadiza ta amsa sallaman tana kallon bakin kofa, Sadeeq ne ya shigo parlon kansa a kasa, Mama Hadiza ta dinga kallonsa da mamaki, Inna ta mike da sauri tace "Naga abinda ya isheni, waye kuma wannan Hadiza?? Wa yake nema a parlon nan" A hankali ya durkusa gabanta cikin raunin murya yace "Don Allah ku yi min rai kaka kar ku raba ni da Imaan, ban san me ya sameni nayi abinda nayi ba, don girman Allah ku yafe min kaka, wllh Ina son Imaan baxan iya rayuwa ba ita ba don Allah kaka ki taimakeni kada su Abba su ce baxa su bani ita ba..." Hawaye sosai yake yana kallonta hankali tashe, Mama Hadiza ta bude baki tana kallonsa, lkci daya taji tausayinsa sosai ba kadan ba don gaba daya a hargitse yake ga wani rama da yyi ba na wasa ba, Inna ta xauna ta rushe da kuka tayi mitsi mitsi da ido tana kallonsa cike da masifa tace "Amma dai kai gantalalle ne wawa, da can uban me ya hau kanka ka yaudari jikata ka sa mata cuta ka gudu?? kunyata mu fa kayi a idon duniya makiyan mu na ta mana dariya ta ko wani lungu da sako, uwar me xa mu maka ka xo mana nan d'an nan, wllh maxa ka fita kada Bukar ya gan ka don ba ruwana, gwara ma Ahmadu...." A rikice ya kamo hannunta yace "Wllh kaka ban san me ya sameni nayi haka ba, don girman Allah kar a raba ni da Imaan xan iya rasa rai na" Imaan ta mike ta shige bathroom ta dinga kuka kamar ranta xai fita, Inna ta gwalo ido tana kallonsa tace "Baka san abinda ya same ka kayi haka ba kuma?" Kuka sosai yake mata yace "Wllh ban sani ba Kaka, ban san me ya faru ba, ban san me yasa nayi haka ba, Kar ku hana ni Imaan don Allah, nasan ke kadai xa ki saurareni kaka" Inna ta fashe da kuka tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Lalacewa ta sameka baka rike Allah da karfi ba Bukar, ni dama nasan da akwai abu a kasa don wannan ba halinka bane, yanxu ni ya xanyi da kai an riga an daura ma mutumi auren yarinya??" Dago kai yyi da sauri yyi still yana kallonta ko kiftawa babu, Mama Hadiza ta sauke wani boyayyen ajiyar xuciya tace "Ka bari iyayenta su dawo xa a san abinda xa ayi Sadeeq...." Sadeeq ya kalleta yace "Don Allah ki sa baki Mama I can't imagine me loosing her, u just can't imagine it" Mama Hadiza tace "You don't worry ka tafi gida, in sha Allah xa a san abun yi" Inna na matsar kwalla tace "Ehh ka tafi xa a san abun yi, ae kai din mutumin kirki ne" xuciyarsa na bugawa yace "Toh anjima xan iya dawowa Kaka?" Mama Hadiza tace "A'a ka bari dai gobe dare yyi yanxu, I will talk to my brothers..." mikewa yyi ya isa gabanta ya durkusa hawaye na sakkowa idonsa a hankali yace "Nagode sosai Mama, Allah ya kara girma" Mama Hadiza ta kasa cewa komai wani tausayinsa ta dinga ji har ranta, cikin sanyin murya tace "Don't worry ka tashi ka tafi Sadeeq" mikewa yyi a sanyaye ya nufi kofa wiping off his tears ya fita parlon, Inna ta kalli Mama Hadiza ta fashe da kukan takaici tace "Kinga maganan iyayen Safara'u a fili ko Hadiza? Kinga magana ya fara fitowa koh, wllh ni dama nasan da kyar Sadeeq yyi ma jikata haka, yaro ne fa mai hankali da natsuwa, ubansa ma ga dattako da sanin ya kamata sannan ga kudinsa na halak, duk satan da ake a kasar nan ko biyar bai taba sata ba wllh inda ya burgeni