Sashe 26
Imaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
🌟⭐ *Imaan* ⭐🌟 _By khaleesat Haiydar_✍🏻 9..... Bayan magrib Imaan ta je kai ma inna abinci ta hadu da Yusuf a hanya yana dawowa daga bangaren innan, gaishesa tayi ya amsa yace "Wai ina tsaraban shopping dina ne Imaan?" Tace "Body spray da turare na siya fa, ka xo sai in baka daya idan yyi rabi sai ka maido min, rabi kawai xan baka dama" yayi murmushi yace "Toh an gama, yaushe xaki fito part din inna?" Tace "Ina kai mata xan dawo" yace "Toh idan na dawo masallaci xan shigo sai ki fiddo min su in xabi wanda nake so" tace "Tohmm ina jiranka" daga haka ta wuce, Mujaheed ta gani bakin tap din inna yana alwala, taji muryar innar tana cewa "Mujaheed ka tabbatar ka datse min pampo wllh cutata kawai Imaan take ta debe min ruwa ta kai ma uwarta" Imaan ta murguda baki tace "Tunda Imaan kadai ce a gidan ba" Ta gefen Ido Mujaheed ya kalleta daga durkushen da yake, ta yi watsi da takalmanta nan bakin kofa ta shiga parlon ta dungure mata warmer din hannunta, inna ta daga murya tace "Har gwara Ita Mujaheed a kan su Ummi da Maimoon tunda ita tana tambayata kafin ta diba, su dai diba kawai suke da hakkina" Juyawa Imaan tayi ta fice mata a parlonta, bata ga Mujaheed din a bakin tap din ba kuma bai kulle mata ba da kwadon da tace Ga, ta yi wucewarta, tayi nisa sosai daga part din inna xata dauki hanyar part dinsu ta ga Mujaheed a tsaye, xaro ido tayi ta juya xata gudu ya cafkota, a tsorace tace "Wayyo me nayi maka" yana mata wani kallo yace "Uban wa ya ajiye ki a mota daxu? Ta 6ata fuska tace "Ni yaushe kaga an saukeni a mota, kawai fa...." wani wawan mari ya xabga mata, ta dafe kuncinta a rude ta fara kwala ma Inna kira, yana mata mugun kallo yace "Baxa ki gaya min waye shi ba" Kuka kawai take tana bubbuga kafa har sannan hannunta na dafe a kuncinta, strictly yace "Gobe na sake ganin haka wllh sai na faffasa maki jiki, duk gidan nan wa kika ga ana ajiyewa a mota, yar mitsitsiya dake xaki shiga mota a sauke ki a gida baki tsoron kowa ke gaki kwai da ake lallabawa" yana kai wa nan ya turata yyi wucewarsa, da gudu ta koma sashin inna ta shige parlon ta xube kasa tana rusa kuka, Inna ta mike tace "Ae fa an kwan biyu ba ayi ba, to uban waye ya ta6a min ke?" Cikin kuka sosai tace "Yaya ne" Inna tace "Waye haka? waye kuma wani yaya?" Imaan ta ki cewa komai sai kuka, Inna tayi fici fici da ido tace "Shi Mujaheed din ya sha wiwi ne da xai kai hannunsa jikin ki?" Imaan na shessheka tace "Mari na yayi ya tura ni" inna ta gwalo ido tace "Mari? Kika sakar masa fuskar ya mara baki ciccijesa kin gudu ba, uban me kika mashi? Toh ya tara kuma ya samu, ba a ta6a ki ba ma ya aka kare da ciwace ciwacen ki balle an mareki a fuska, to mu je ki nuna ma ubansa fuskar" tana fadin haka ta daga Imaan suka fice parlon, inna na tafe tana kunduma masa duk xagin da ya xo bakinta, Imaan dai sai ajiyar xuciya ta ke saukewa tana biye da ita, inna ta tura kofar parlon Abba bayan ta shiga main parlor, Umma ce duke tana sa turaren wuta a parlon, Inna ta wani hade rai tace "Ke ina mijin ki?" Umma ta dauke kai tana ci gaba da abinda take tace "Bai dawo masallaci ba, ina wuni" inna ta xauna saman kujera tace "Ina wuni kuma, dama da ban wuni ba kya gan ni Rukayya" Umma dai bata ce komai ba, Inna na kallon Imaan dake tsaye tace "Toh ai sai ki xauna mu jira ubansa koh" Imaan ta xauna kasa tana goge hawayen idonta, Abba ne ya fara shigowa parlon, yayi still ganin Inna, ta kafesa da ido tana girgixa kafa, yace "Lafiya kuwa inna?" Mujaheed dake bayan Abba har ya sako kai jin abinda Abba yace xai koma baya da sauri suka yi ido hudu da inna, da sauri cikin daga murya inna tace "Rikosa Ahmadu rikosa, abu ya lalace idan ya gudu kar ka bari ya fita, xamansa muke a nan" Abba ya juya yana kallon Mujaheed da ya wani hade rai ya fasa komawan, Abba ya karasa cikin parlon ya xauna yana kallon Imaan da ta hade kai da gwiwa sannan ya kalli Inna, Mujaheed na satan kallon Umma ya shigo ya nemi waje ya xauna a kasa, duk ya fi jin ummar tasa a kan inna, banda faduwa babu abinda gabansa ya ke, Abba yace "Me ya faru kuma inna" Inna ta kalli Umma dake tsaye tace "Toh Malama xa ki iya ba mu waje in yi sirri da d'a na koko mu koma daya parlon" Umma bata ce komai ba, Inna tace "Atoh ke kadai ce bare, nan d'a na ne da jikokina" Umma ta nufi kofa fuskar nan nata a murtuke, Mujaheed ya sauke ajiyar xuciyan samun relieve daya wato fitar Ummarsa, Inna ta mike da kanta ta rufe kofar har da sa makulli ta dawo, Abba dai sai kallonta yake, ta xauna tayi kicin kicin da fuska tace "Ahmadu daxu Imaan taje kai min abinci bayan ta ajiye ta fita ba sai wannan yaro Mujaheed ya kamata a hanya ya daddage ya kwada mata wani mahaukacin mari a fuskarta ba" tana fadin haka ta dago kan Imaan tana nuna ma Abba fuskar tace "Yanxu fisabilillahi meye wannan Ahmadu, yau ko dabba Mujaheed ya samu xai maresa haka balle d'an mutum, d'an mutum din ma 'yar kanin ubansa, to wllh ka dau mataki yanxun nan, Sam baxai yiwu ba, yarinyar da ake kaffa kaffa da ita saboda lalurorin da Allah ya saukar mata, yanxu gobe ba abun mamaki bane a ga fuskar ya salu6e wannan irin bugun da yaji, tunda ga irin yanda Allah yayi ta ko ina ba kwari sae laushi, to wllh ka san abun yi Ahmadu, shegiya nake idan na yadda" Mujaheed dai ya kasa dago kai sai kallonsa Abba yake, fuska daure Abba yace "Kai..." Ya dago da kyar, Abba yace "Uban me tayi maka ka kai hannu fuskarta?" Inna ta gyara xama ta hade girar sama da ta kasa tana kallonsa, Mujaheed yyi kasa da murya yace "Abba gani nayi an sauketa a mota daxu...." Abba ya kalli Imaan yace "Mota kuma?" Inna ta buda ido sosai tace "Mota?? Ina kika samo mota Imaan?" Imaan ta ki cewa komai ta fara hawaye, Abba yace "Baxa ki bude baki ki ma mutane magana ba, wa ya sauke ki mota Imaan?" Inna tace "A'a dakata Ahmadu kada a wani fake da an sauketa a mota a shashantar da xancen mari, kai ko daukanta aka yi a hannu aka sauketa a kofar gida bai kai katon d'an ka ya xabga mata mari har haka ba, a kan me? To an sauketa a motar, ita yarinya ce ko ba ta isa a ajiyeta a mota bane? Idan sabon saurayi tayi fa, ko dama haka xata yi ta xama ba saurayi?" Daga Abba har Mujaheed kallon inna kawai suke, ta ja tsaki tace "Wannan ai abun farin ciki ne ni dai a gu na, to da a mashin roba roba ku ka so a sauketa idan ba a mota ba, ko kuma idan tayi ta xama ba saurayi Mujaheed din ne xai aureta? Yau naga abinda ya isheni bai ishi Allah ba, kawai yaro ka tattakure ka kama yar mutane ka falle da mari ga ka mugun tantiri ko? sannan na taso takanas na kawo kara gun ubanka ya wani fake da wa ya sauketa a mota salon maganar marin ya bi iska, To Allah ya Isar mata" daga haka ta mike tana kallon Imaan tace "Tashi mu je, Allah dai ya isa" Tashi Imaan tayi ba tare da ta yarda ta kalli Abba ba inna ta ja hannunta ta nufi kofa tana cewa "Ka ci gaba da daure masa kugu wllh duk randa xuciya ya kwasheni idan ban sa k'attin anguwar nan sun tare sa a lungu sun nakada masa shegen duka na biya su ba kace ba uwata ta haifeni ba" da karfi ta rufo masu kofar bayan sun fita, Abba ya sauke ajiyar xuciya yana kallon Mujaheed, lkci daya ya hade rai yace "Does that warrant you to slap her Muhammad?" Mujaheed ya kasa cewa komai, Abba ya masa tsawa yace "Ba da kai nake ba malam?" Da kyar yace "Abba kayi hakuri, I was only trying to do what I thought was right, duk gidan nan nasan you don't tolerate yarinya ta shiga motar saurayi" Abba yace "Not to the extent of slapping her, if she proved to be stubborn why not report her to me? Kasan halin grandmother din ku, kuma kasan dole sai taje ta gaya mata" Mujaheed yace "Kayi hakuri" Abba yace "Stupid ba ni xaka ba hakuri ba, ita da ka mara da innan xaka ba hakuri, kuma kada ka sake wannan wawancin" yace "In sha Allah Abba" Abba yace "Idan ba hauka ba ma kawai ka daga hannu ka mari mace?" Shiru Mujaheed yyi, Abba yace "Tashi kaje kayi abinda na ce maka, ita kuma Imaan din xan hadu da ita" mikewa Mujaheed yyi ya kara ba Abba hakuri sannan ya fita parlon. A hanya Inna ta kalli Imaan tana washe baki tace "Ke kice saurayi me mota kika yi Imaan?" Imaan ta turo baki bata ce komai ba, Inna tace "Toh baki ce masa kakarki na nan da rai bane naga bai shigo ba, ko yaushe yace maki xai shigo gaisheni?" Imaan tace "Ni fa ba saurayi na bane, driver din gidansu kawata ne naje dubota bata da lafiya shine mamansu tace ya maido ni gida" sake baki inna tayi a sanyaye tana kallonta tace "Ba lafiya... Direba kuma?" Imaan bata ce komai ba ta shige balcony dinsu ta bude kofar parlor ta shiga sai a sannan ta kalli inna dake tsaye baki sake har sannan tace "Sai da safe" daga haka ta kulle kofar ta sa makulli. Washegari