Sashe 35
Imaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Yaya" fuska daure yace "Kiyi providing min furan nan yanxun nan idan ba haka ba wllh kinji na rantse sai na sa ki kuka" ta fashe da kuka amma ba hawaye tace "Yaya bayan kana gani duk ya xube nima ban sha ba, don Allah kayi hakuri xanje waje in siyo maka wllh" ya wani hade fuska yace "Wannan nake so ba na waje ba" ta marairaice tace "Toh yanxu yaya a ina xan samo maka wani, nima fa kaga bata bani ba" ya kalli part din Inna sannan ya kalleta, murya can kasa yace "Kinsan abinda xa ayi yanxu?" Ta kara marairaicewa tana girgixa masa kai, yace "Komawa xa kiyi part dinta ki shiga daki ki fito da bowl din furan da gudu yanda kika fito min da nawa yanxu" ta xaro ido tana kallonsa, sai kuma ta fashe da dariya tace "Yaya kasan baxata bari ba fa" ya hade rai yace "Irin dubaran da kika yi kika fita da nawa haka xaki fito da wancan ma ae" Imaan ta dinga dariya har da kyakyatawa, ya ja kunnenta yace "Baxa ki daina wannan dariyar mahaukatan ba" ta hadiye dariyar da kyar tace "Toh amma tare xa mu sha?" Yace "Eh mana" tana murmushi tace "Toh nasan yanda xan yi" a tare suka koma part din inna ya nuna mata bayan window din bedroom din inna yace "A can xa ki sameni ina jiran ki" tace "Toh" daga haka ya wuce yana waigota, a guje Imaan ta shige parlon inna tana cewa "Wayyo inna kice masa wllh kar ya ta6a ni xan gaya sa da Abba, inna kice kar ya taba ji xan kira daddy na...." Mujaheed yyi murmushi ya koma bayan window din ya tsaya yana shafa kansa, Inna ta mike da sauri kar Imaan ta take ta koma wani wajen ta xauna tace "Fito min daki wllh, ba ruwana ku je can ku karata kar wanda ya dameni, yara dai kamar na jaraba" Imaan da ta shige dakin tuni ta dinga dariya kasa kasa ta dau bowl din furan ta datse murfin yanda idan tana gudu baxai xube ba, ta tattara rigar jikinta tayi saitin bakin kofar fita sannan ta fice a dari da sittin, inna ta kyakkyafta ido don tabbatar da abinda ta gani hannunta amma tuni Imaan har ta fice parlon kamar xata tashi sama, inna ta mike da sauri tace "Isuhu me na gani a hannunta kamar kwanon fura na???" Ummi ta kyalkyale da dariya tace "Wllh shi ne" Yusuf ya fashe da dariya, Inna ta fashe da kuka tana kallonsa. Imaan bata tsaya ba sai da ta isa inda Mujaheed yake jiranta, murmushi yayi ya amshi bowl din yace "Yauwa kinyi kokari" ta washe baki tace "Nagode" ya xauna kan dakali dake wajen ya bude bowl din ya dau ludayin ciki ya juya furan sannan ya fara sha, Imaan ta daina murmushin da take ta durkusa gabansa tace "Yaya kai kadai xaka sha" Ya harareta yace "Toh da ni da wa xa mu sha?" Ta xaro ido tace "Wllh baxan yadda ba ni fa na sha wahala na dakko kaga irin gudun da nayi yanxu ma fa kirjina ciwo yake" banxa yyi da ita yana shan furansa don furan inna ba dai dadi da gardi ba, Ta fashe da kuka tana kallon sa, ya hade rai ya debi rabin ludayin hannunsa ya kai bakinta, ta turo baki tace "Wannan d'an kadan din bayan kai cika wanda xaka sha kake?" Yace "Baxa ki bude bakin ba" ta bude bakin da kyar, ya xuba mata yace "Toh tashi ki tafi" kamar jira take tace "Wllh baxan tafi ba ji fa abinda ka bani bayan ni na sha wahalan daukowa, Allah sai dai ka bani in mayar" Yace "In baki ki gudu da shi gidanku dai" Ta fashe da wani dariya har da kyakyatawa, ya harareta ya ci gaba da shan furan, kamar xata yi kuka tace "Yaya" ya kalleta sannan ya debo furan rabin ludayi ya kai bakinta, kin bude baki tayi tana masa wani kallo, ya kai bakinsa ya shanye, ta fashe da kuka, yayi light murmushi ya kara deba ya kai bakinta, bude bakin tayi ya juye mata, daga nan ya ci gaba da sha bai kara kallonta ba, kiris ya rage ta fashe da kukan gaske, ganin bai san tana yi ba ta fixge ludayin hannunsa, ya wara ido yace "Ke ina wasa da ke ne" ko kallonsa bata yi ba xata diba ganin xai dauke bowl din ta marairaice tace "Don Allah yaya ka bari in sha wllh baxan cika ba" yace "To diba in gani" ta turo baki ta ciko ludayin ta kai baki da sauri, ko shanyewa bata yi ba ya fixge ya juye ragowar a bowl din sannan ya diba ya kai baki, tana ganin haka ta dauke bowl din ta kai baki ta kwankwade ya xaro ido kafin yace komai suka ji muryar Inna cikin kuka tana cewa "Ahmadu idan ba a bi min hakkina ba yau a babbake ni cikin dare idan na kwana cikin gidan nan" Mikewa Mujaheed yyi da sauri xai bar wajen imaan ta mike ta rikosa a rikice tace "Wayyo yaya kai ne kace fa in dauko" Ya wani xaro ido yace "Ni?? You are sick, kar ma ki sa ni a maganan nan" daga haka ya bar gun da sauri don da dukkan alama nan suke taho, Imaan ta bi sa da gudu har suka iso gaban compound din gidan, ya wani hade rai yace "Wai me yasa kike bi na ne ma dai tukun?" Ta marairaice tace "Yaya kai fa ka sa ni" Ya xaro ido yace "Ohh dama idan nace ki shiga wuta sai ki shiga, kar ki kuskura ki ambato sunana a maganan nan" on a serious note ya fadi hakan, ta hararesa tace "Wllh kai ne kace in dauko da gudu in fito" xai yi magana suka ji alamar suna tahowa, inna na cewa "Kuma ko tantama babu wannan tantirin Mujaheed din da ka haifa ne xai sa ta, banda haka imaan ta san wani sace abincin mutane ta fita da gudu, wllh a min iyakan gaske da yaran nan a gidan nan yau, a kan me xa su dinga cutata suna ci min mutunci haka, wai har sun shanye furan sun bar min kwano a bayan window, me nayi masu a rayuwa xa su min haka" tana kai wa nan ta rushe da kuka, Anty tace "Kiyi hakuri don Allah inna" a fusace inna tace "Shegiya nake idan na hakura, a sace min furan a shanye kice in hakura kamar uwata tace min je ki kya gani, ae Aisha dai ta haifi fitina, wannan yarinya Imaan dai fitina ce wllh, a ma kira min Bukar yanxu, idan ban tada gidan nan da bala'i ba yau ace bani ba" da sauri Mujaheed ya nufi gate, imaan kamar xata fashe da kuka tace "Wayyo yaya" sai da ya kusa gate ya juya yana kallonta ya fara dariya kasa kasa, bin bayansa tayi da gudu, gun motarsa dake parke a kofar gida ta gansa xai bude maxaunin driver, ya buda ido yace "Wai me yasa kike bi na ne?" Ta karasa gun motar tace "Wllh yaya ni ba ni kadai xa a gani a gidan ba bayan ni da kai muka shanye, kawai Ammi ta kama ni ta min duka" ya daure fuska yace "Kinga ki juya ki koma ciki wllh" ta fashe da kuka ta make masa kafada, ya shige driver seat, ta bude front seat ta shiga tana turo baki, yace "Wai kin san inda xa ni" kin cewa komai tayi, jin an bude gate ya rufe door dinsa da sauri, Yusuf ne ya fito, Mujaheed ya tada motarsa ya yi zooming off, Yusuf ya dinga dariya mai gadi na kallonsa, sai da suka hau saman titi Mujaheed ya kalleta yace "Dama seriously idan kika kira sunana a case din nan wllh sai na sa ki kukan sati daya, sai ki gaya masu furan ma ke kadai kika shanye" Ta gefen ido ta kallesa kafin tace "Sai dai in ce masu ludayi daya da rabi kawai na sha sauran kuma ban san wanda ya shanye ba" Yace "Kina son in sauke ki nan kenan" ta marairaice tana kallon sa, yace "Toh me xaki fada masu a kan furan" a hankali tace "Cewa xanyi ayi hakuri ni da yaya muka shanye" parking yyi gefen titi, ta rikosa da sauri tace "Aa yi hakuri xan ce ni kadai na shanye" ya hade girar sama da ta kasa yace "Ki rantse" Kamar xata yi kuka tace "Bayan ni da kai muka sha"