Sashe 263
Imaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
a can don ita tsoron kowa take a gidan bata yadda da kowa ba, A bedroom Imaan ta samu Ammi xaune, ta duka kasa jikin gado tana kallonta a hankali tace "Ammi Ina kwana" Ammi tace "Lafiya lau, kin tashi lafiya?" Imaan tace "Alhmdllh, daxu da kika xo ina wanka" Ammi tace "Ohk, kinyi breakfast?" Kai Imaan ta gyada mata, Ammi ta yi shiru sannan tace "Me Mujaheed din yace maki kan komawar ku?" Imaan ta sunkuyar da kanta tace "Inna ce tace A'a" Ammi tace "Ba Aunty ta fara hada maku kayan ba" Imaan dai bata ce komai ba, Ammi tace "Idan ma xa ki daina biye ma Inna ke daina biye mata ki bi mijinki ku tafi, Daddy ma yayi magana jiya" Kai kawai Imaan ta gyada mata, Ammi tace "Ki tafi kitchen ki debi abinci, idan kuma shayi xa ki hada sai ki hada, ko in soya maki kwai?" Imaan tace "Ammi nayi breakfast fa" Ammi tace "Toh shikenan" Shiru ne ya biyo baya, Ammi tace "Kina ji na?" Daga kai Imaan tayi ta kalleta tace "Ina ji Ammi" Ammi tace "Bana son ki saka duk abubuwan da suka faru a ranki, no matter what you've got to respect ur mother in law, in ma tana son ki in ma bata son ki, duk wani abu na kyautata da kika san ya kamata ki dinga mata albarkacin d'an ta da kike aure yanxu, kaninnsa ma gaba daya ko suna sonki, ko basa son ki kiyi masu abinda ya kamata, babu ruwan ki da abinda suka maki a baya duk wannan ya wuce, kuma nasan baki riko, lkci lkci sai ki ce ma Mujaheed din ya kai ki ki gaisheta a can Zaria, just that you have to be very prayerful, never get tired of praying domin addu'a shine makamin mumini, mijin ki kuma kiyi masa biyayya yanda ya kamata, nasan ba sai na tsaya maki wani bayani a kan aure ba you are educated Imaan, kin san komai, sai dai kawai kamar yanda kike yi a nan gida haka nake son ki ci gaba da kasancewa cikin kamshi da tsafta, sannan ki dinga kama jiki don wani lkcn na sanki da shegen son jiki, ko yaya ne ki dinga aikin da baxai takura ki ba, kin dai ga yanda nake barin gida na a ko da yaushe very neat, try to keep ur home clean kuma ya kasance cikin kamshi ko da yaushe, duk da nasan ki da kokarin gyaran daki da wankin bandaki, but put in more effort daughter, Allah ubangiji ya albarkaci auren ki, ya baku xaman lafiya me dorewa, da hakurin xama da juna.... Kasa cewa komai Imaan tayi kanta a kasa hawaye na sauka idonta, Bude kofar dakin aka yi Ammi ta kalli direction din ta ga Inna tsaye bakin kofar, Ammi ta sauka saman gadon tace "Sannu Inna" Inna tace "Sannu, me kike kitsa mata tun daxu bata dawo ba Aisha??" Murmushi Ammi tayi tace "Kawai nasiha nake mata Inna" inna tace "Ai kullum cikin yi mata nake" tana fadin haka ta kalli Imaan tace "Tashi mu tafi, nasiha kuma wanne ne ban maki ba tun da kika dawo wajena idan ba gulmar uwarki bane ya tashi" Imaan ta kalli Ammi a sanyaye, da fillanci Ammi tace mata ta tashi ta tafi, inna ta saki baki tana kallonta, mikewa Imaan tayi ta nufi kofa, Inna tace "Ba ruwana da munafurci wllh" daga haka ta bi bayan Imaan suka fita, bayan sun fita apartment din Inna na kallon Imaan tace "Me ta ce maki wai?" Imaan ta turo baki tace "Toh Ina ruwanki?" Da yamma Inna ta dinga bin Imaan da kallo ganin yanda ta shirya cikin riga da skirt har da shafa powder, Jin shiru bata fito ba bayan ta shiga daki Inna ta mike ta bi bayanta a hankali ta leka cikin dakin, a duke ta sameta jikin gado waya kare kunnenta, Inna ta buda baki a sanyaye tana kallonta, Da sauri Imaan ta katse wayar hannunta ta ajiye tace "Daddy ne fa nake kira" Inna ta karasa ta dau wayarta tana kallo kamar xata yi kuka tace "In dai Mujaheed kika kira da wayata ke da Allah, ba ruwana" Imaan ta mike ta fice daga dakin tace "Ai dai ba ke kika saka katin ba Daddy ne ya saka maki naga" Maimoon ce ta shigo parlon tana kallon Imaan tace "Abba na kiran ki Imaan" Inna tace "Ya dawo ne?" Maimoon tace "Ehh ya dawo yanxu" Inna tace "Toh su kuma gantalallun nan da suka tafi raka katuwa Rukayya basu dawo bane?" Maimoon tace "Ehh kila xa su yi sati daya a can" Inna na tafe hannu tace "Toh maza maza su dawo don rukayya Bata da tarbiyar da xata yi ma yaran nan kada ta kai min jikoki ta barosu in shiga uku...." Imaan ta dau Hijab dinta ta saka ta bi bayan Maimoon suka fita parlon, Abba na xaune parlor hannunsa rike da remote Imaan ta shiga parlon ta xauna kasa ta sunkuyar da kanta tace "Ina yini Abba?" Abba yace "Lafiya lau Mamana" Imaan tace "Ya aiki?" Yace "Alhmdllh" Bude kofar aka yi Mujaheed ya shigo da sallama, suna hada ido Imaan ta sunkuyar da kanta tana wasa da fingers dinta, Mujaheed ya xauna kasa a hankali yace "Barka da dawowa Abba" Abba yace "Yauwa, ya aiki?" Yace "Alhmdllh" Abba yace "Maa sha Allah, kana ji na Muhd?" Mujaheed ya kallesa yace "Ina ji Abba" Abba yace "Ka dau matar ka ku wuce gida yanxu, Allah ya ba ku xaman lafiya... na yarda xaka rike Imaan yanda ya kamata don nasan tarbiyar da nayi maka, so I need not to say much, Kai dai kayi kokari ka rike min ita da amana, sai kuma ayi ta hakuri, daga nan yanxu ku tafi ku yi ma Hajiya Aisha sallama da Amina sai ku wuce ba sai kun je gun inna ba" Mujaheed ya kalli Imaan da ta rufe fuskarta ta fara hawaye, ya d'an yi murmushi cikin sanyin murya yace "Toh nagode Abba, Allah ya kara girma" Abba yace "Ameen, Allah maku albarka, ya baku xaman lafiya" Mujaheed ya amsa da Ameen ya mike a sanyaye yana kallon Imaan da ta ki motsi, Murmushi Abba yyi yace "To tashi ku je Mamana" imaan ta mike da kyar tana share hawayen dake sakko mata da hijab ta bi bayan Mujaheed da ya nufi kofa suka fita parlon.