← Book details Imaan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 217 OF 292

Sashe 217

Imaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kwarai, Hajiyar ma tace a gaishe ki" Gwaggwo tace "Toh Ina amsawa, Allah ya maku albarka" duk suka amsa da Ameen suka mike, Daddy ma yyi mata sallama suka fita parlon, a bakin gate suka hadu da Ammi ta dawo pharmacy, kallo daya tayi masu ta dauke kai ta gaida Abba, Abba ya amsa yace "Ya mai jikin ta kara ji Aisha" Ammi tace "Alhmdllh da sauki" shi dai Daddy kallonta kawai yake, Abba yace "Toh Allah ya bata lafiya" Ameen ta mayar masa ta shige gate din gidan, murmushi Abba yyi ya bude front seat, daddy ya xaga ya shiga maxaunin driver suka bar anguwar, Abba yace "In sha Allahu xa su sakko gaba daya, kuma xa su fi kowa farin ciki da wannan aure nan gaba" Daddy bai ce komai ba har suka hau saman titi, sai kuma yace "How do we reach Muhd, I am disturb about him barrister" Abba dai bai ce komai ba don shi ma bai san inda xai samo Mujaheed ba balle su ji ta bakinsa a kan auren. Mota biyu Hajiyan Marafa suka yo da yaranta mata su uku, da yan uwanta biyu da kawayenta biyu sai Safeenah da har wani rama tayi sai yan idanuwa da suka kumbura suntum dan kuka, da ta tuna wai mijinta Mujaheed aka hada da Imaan sai ta fasa wani ihu kamar mahaukaciya har tsakar dare haka ta dinga masu kamar tababbiya, ta girgixa ne ba na wasa ba, gate mai gadi ya wangale masu a xatonsu masu xuwa biki ne, Hajiyan Marafa ce ta fara sakkowa motar sannan yaranta, kawayenta da Yan uwanta suma duk suka fito daga tasu motar ko wannen su fuska a murtuke, Rahma ce ta tafi dakin umma ta sanar ma ta xuwan su Hajiyan Marafa da suka ki shigowa ko da parlor ne wai a kira masu Hajiya Rukayya, Umma ta katse wayar da take da Hajiya Saude jikinta ya hau rawa tace "Kice masu bana nan, tun daxu na fita...." Rahma tace "Har fa da Hajiyar da kanta" cikin tsawa Umma tace "Ki fita kice masu bana nan nace, ko uban me xan masu da suka xo min nan, ko ce masu aka yi ni na daura ma Mujaheed aure???" Rahma ta fita dakin umma ta mike da sauri ta sa makulli hannunta na rawa, xaunawa tayi gefen gado xuciyarta na bugawa, Allah kadai yasan abubuwan da xa su fada yau, saukin abun ma Abba sun fita tun daxu da kaninsa, Aunty da Mama Hadiza dama suna can part din Inna tun safe, dialing Number Hajiya Saude ta kara yi ta sanar mata Hajiya Mansura ta xo tare da tawagarta a motoci, Hajiya Saude tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un... Toh yanxu ya ake ciki??" Umma na share xufar da ke keto mata tace "Tonon asiri nake tsoro Saude, nasan yar duk ta kwashe ta sanar masu yanda aka yi, Saude kar su fasa kwai a gidan nan in shiga uku dadin abun ma Alhaji bai nan, Amina da Hadiza kuma suna gun tsohuwar amma kinsan yanda Hajiyan Marafa ke magana, wllh dole su ji hayaniya su fito, ni dai nace Rahma tace bana nan" Hajiya Saude ta sauke ajiyar xuciya tace "Ni wai Rukayya tun farko me kika ga tattare da family din Hajiyan Marafa kika hada d'an ki da yar su??" Umma tace "Aa kawai don ace d'a na na auren yar masu kudi mana, sunan nake so dama, kuma ai haka ma mutane ke cewa" Hajiya Saude ta ja tsaki tace "Toh me kika karu da a kudin su?" Umma tace "A'a ki bari, wllh ynxu haka akwai wani sarka da dankunne xai yi miliyan daya da rabi haka Hajiyan Marafa ta bani kyauta kwanaki da naje, sannan ta dalilin auren nan matan governor kalilan ne ban sani ba, duk taronsu sai naje, manyan kasan nan yanxu daddaya ne ban gani ba ido da ido amma a mata, Kai har wasu maxan ma...." Xaro ido Umma tayi jin hayaniya a tsakar gida tace "Gasu can Saude, xa mu yi magana anjima" daga haka ta katse wayar ta tafi ta bude labule a hankali tana lekansu.... Hajiyan Marafa ce tsaye tana cewa "Duk inda Rukayya ta shiga yau sai ta fito wllh, in har na bar gidan nan to Rukayya ta fito ta fallasa kanta ne, 'ya ta xata yaudara a hada baki da ita a mata kishiya??? Toh wllh wllh yau sai ta san tayi da Hajiya Mansura, yanda ban xauna da kishiya ba haka diyata baxata xauna da kishiya ba, malamai da bokayen da take bi yau duk sai ta fito tayi bayani ta tona kanta ta fadi abinda tayi aka fasa auren yarinyar gidan nan har aka hada auren da mijin diyata...." Hajiya Baturiya yarinyar Hajiya Marafa ta fari cikin tsawa da daga murya tace "Ta fito da bakinta ta fadi abinda tayi aka fasa auren da aka lika ma mijin Yar uwata, ta fito nace idan ba haka ba yau wllh wllh sai mun tada gidan nan in ga shegen da ya tsaya ma mutan gidan....." Kawayen Hajiya marafa suka yi cikin parlor suna cewa "Ae duk inda ta shiga sai ta fito wllh, sai ta fallasa kanta anji mugun abinda take yi tun ba yau ba, yau xata ga karshen boka da malamai...." Mama Hadiza ce ta taho compound din da sauri jin hayaniya Aunty na biye da ita a baya, Umma dake jin su a daki ta daura hannu a ka ta dinga xagaye dakin hawaye na sakko mata tana salati tana fatan kada su Abba su shigo gidan, wani rashin tunanin ne ya kai ta hade kai da Safeenah har ta san sirrinta haka tasan abinda take ciki, tare fa suka dinga xuwa gun Malamin ashe abu xai juyo kansu yanxu ga Safeenah ta fallasa ta gun uwarta da bakinta ba shiru yake ba, ta xauna gefen gado ta fashe da kuka tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, me ke faruwa haka ni Rukayya, Allah ka rufa min asiri kada 'yan gidan nan su jiyosu su fito, da na shiga uku yau kuwa" muryar Mama Hadiza da ta ji tana tambayar lafiya yasa ta mikewa da sauri tana xaro ido ta ji cikinta ya hautsine, Hajiya Baturiya tace "Kafff xuri'ar mu babu wanda ya taba xama da kishiya don haka baxa a fara kan kanwar mu Safeenah ba, karya ake Safeenah ta xauna da kishiya, Rukayya ta fito ta fadi abinda tayi gaban kowa yanxun nan..." Mama Hadiza tace "Tohhh, iko sai Allah ku kuma da abinda ku ka xo kenan??" Hajiya Shamsiyya ta iso wajen tana huci tace "Kwarai kuwa da abinda mu ka xo kenan, bokan da Rukayya ta biya ta sa ya wargaje auren yar gidan nan shi xata fito yanxun nan ta kai mu gunsa ya wargaje abinda yyi da har yasa tsautsayi ya fada kan 'yar mu, kin ganmu nan kaff bbu mai kishiya, kema kanki nasan baki sonta don haka Safeenah domin ita kadai aka yi mijinta baxata xauna da wata banxa wai kishiya ba...." Muryar Inna suka ji tana salati da karfi tana cewa "Naga abinda ya isheni ni patuu, wasu mahaukatan ne aka bude ma get suka shigo mana gida haka, anya ilu xai gama da duniya lafiya kuwa, banda haka ya xai bude ma lafta laftan mahaukata get su shigo mana gida suna hauka ba kakkautawa??? Ina Ahmadu da Bukar suke suga abinda shegen bakauyen da suka ajiye a bakin get yyi, ya tashi ya bude ma ta6a66u get salon su fara bin mu da duka muna gudu" Hajiya Marafa ta nufeta cike da raini tace "Hajiya mu ba mahaukata bane, amma mun fi mahaukata hauka idan aka ta6o mu, ba wani abu ya kawo mu ba Rukayya muka xo nema ta fito ta fadi abinda tayi aka fasa auren gidan nan wanda hakan yasa har aka ma diyata kishiya bata ji ba bata gani ba, wllh har gun bokan da ta je aka mata aiki duk sai ta kai mu yanxun nan gaba daya...." Inna ta xaro ido cike da masifa tace "Auzubillahi wacece wannan Kuma?? Waye kuma boka ni patuu?? Rukayyar ce ta san wani boka?? Toh tun da uwarta Hadiza ta haifeta bata san sa ba, kaji min gantalallu dai yan iska mahaukata, waye kuma 'yar ku? Safara'u ko wa? Wllh tunda ku ka ma Rukayya wannan gagarumin sharrin sai Mujaheed ya fito duk inda yake ya sake shegiyar yar ku, don baku da tsoron Allah uwarsa ku ka xo yi ma cin mutunci har gida?? To wllh sai Mujaheed ya saketa yau yau din nan, mu kaf danginmu bbu wanda yasan boka, kai ko ma ya sani Allah ya yafe masa, kaji min mutane dai yan wahala, wllh idan baku fitar mana gida ba sai na tafi caji ofis yanxun nan an xo an kwashe ku in ga uban da ya tsaya maku, Ina ruwan Rukayya da wani boka Allah na tuba, matar dake ta murna da hadin da Ahmadu da Bukar suka yi tun jiya, tun da nake Rukayya bata taba shigowa da sassafe gaisheni ba sai da aka hada auren nan, yanxu haka da kanta xata je dauko amaryar a gidan kakarta don can ta kwana... Kaji min mutane dai?? To wlh ku fita ku ban wuri kada in tsine maku" Daga Hajiyan Marafa har 'ya yanta da kawayenta sake baki suka yi suna kallon Inna, Inna ta juya ta fara wucewa a fusace tana cewa "Rukayya ai ta fi kowa murna da auren nan, dama tun farko ita ba son shegen d'an Bulasawan nan take ba, tun farko take ma Imaan kwadayin aure da Mujaheed mu ne dai ba mu yarda ba" Aunty ta saci kallon Mama Hadiza dake bin uwar tata da kallo, can duk suka bi bayanta, Safeenah ta fashe da matsanancin kuka mai ban tausayi ta durkushe wajen jikinta na rawa tace "Na shiga uku Mummy wllh ni baxan iya rabuwa da Mujaheed ba Ina sonsa, dama ashe duk yaudarata take da Mujaheed take son ayi auren nan?? Wayyo mummy ku taimakeni kada ya sakeni wllh ina son sa" Hajiyan Marafa ta dinga huci ta ma rasa abun cewa tana kallon Safeenah, sai da Inna tayi nisa ta kalli Mama Hadiza
Chapter 217 · 0% Book details