← Book details Imaan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 209 OF 292

Sashe 209

Imaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

daxu ya nuna ya fasa auren yar mu, tuni kuma mun maida masu sadakin su lefe kuma ko xuwa anjima in sha Allah xa a mayar, Allah yasa hakan ne mafi alkhairi ga dukkanmu gaba daya...." Inna ta rushe da wani kuka da tsorata mutanen parlon tace "To kuwa yanxun nan xan tafi in nemo gidan Bulasawa in ci ubansa da d'an nasa, Allah ya tsine masu albarka, Allah ya tarwatsa su, Allah ya isa tsakanina da su, Allah yyi yaga_yaga da dukiyar nan tasu ta sata, shegu barayi, mu xa su kunyata a idon duniya ga bak'i mun tara ta ko ins, to in sha Allahu kotu ce xata raba mu da matsiyatan, Shari'a ce mai girma xa mu yi tun a duniya kafin mu tafi gaban Ubangijin mu, yau xan tafi in shigar da kara a kotun Habuja...." Abba yace "Don Allah ki sauraremu Inna, dama an taba aure dole?? bbu ruwan ki da su balle aje wani shari'a kawai mu sa a ranmu fasa auren nan shine mafi alkhairi ga 'yar mu, kuma basu kunyata mu ba don bamu bar masallaci ba sai da na tabbatar na fitar da d'an uwana kunya na daura ma 'yar sa aure da nawa d'an da nake da iko da...." lkci daya gaba daya mutanen parlon suka daga kai suna kallon Abba with full shock, ko allura ya fadi a lkcn sai kaji karansa, Imaan taji kamar numfashinta na mata gardama ta dinga kallon Abba xuciyarta na wani bugawan da bai ta6a mata ba, Umma ta hadiye abu da kyar tana kallon Yusuf da kansa dai ke kasa, ji tayi wani xufa na keto mata don wannan shine anyi ba ayi ba, yanxu Yusuf aka makala ma yarinyar nan, Mujaheed dai sai kallon Abba yake xuciyarsa kamar xai fashe sabida yanda yake harbawa, Abba ya mike yana kallon Inna da ta cire mayafin kanta tana kikkifta ido tana kallonsa, yyi kasa da murya yace "Na hada auren Imaan da Mujaheed yau, saboda ina da yakinin xai ma fi Sadeeq din rike min 'ya ta da amana...."
Chapter 209 · 0% Book details