← Book details Imaan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 248 OF 292

Sashe 248

Imaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

je siyo maki abinci, ni dai ga wani nan na samu" Inna na kallon Imaan tace "In har kika yarda kika ba mayyar kishiyar ki daman raina ki baki dinga cin ubanta ba to gaskiya an cuce ni da aka sa maki sunana, irin gallazawar da nayi ma uwarsu Bala da Hansai ai sai Allah, komai sai yanda nace ayi xa ayi a gidan nan, keee!! wllh ki kara kaifin bakin ki da fitsara..." Inna na nuna mata bakinta tace "Kinga bakin nan nawa, to shi ya kwace ni a kuruciyata, kwata kwata ban daukan nansans" Dariya Imaan ta fara yi, Mama Hadiza dai tayi murmushi tana kallon uwar tata, Inna ta ci gaba da cin abincinta tace "Wacece kuma Safara'u da cikin mintuna kalilan baxa ki kwace Mujaheed a wajenta ba, shi fa Mujaheed wllh tun ba yau ba dama yake son auren ki, irin son da yake maki ba ni har tsoro ya dinga bani lkcn, duk ina lura da shi yyi ta wani takura ki yana sa maki ido d'an banxan, gashi yyi ta latse min ke kuma sbda bashi da tsoron Allah, ashe dai kayansa ce ke, ohh Allah mai girma gashi yanxu har kin tare gidansa kin kwana" Imaan ta rufe fuskarta da kujera tana murmushi, Mama Hadiza ta fara dariya tana kallon Inna, inna ta tabe baki tace "Ni dai ba ruwana, ashe dama Allah ya riga ya kaddara shi din dai ne mijinki, tohh ya muka iya Mujaheed dai jikana ne kuma bbu wanda ya fi ni saninsa gaskiya...." Shigowar Mujaheed ya sa Inna tayi shiru tana ci gaba da cin abincinta, Mama Hadiza dai sai kallonsa take tana murmushi, ya ajiye ledan hannunsa yana kallon Imaan da ta ki dago kanta, Inna ta kallesa ta gefen ido ta tabe baki, xaunawa yyi yana kallon Mama Hadixa yace "Ga abinci na siyo maki Mama" Mama Hadiza tace "Toh nagode" Mikewa inna tayi tana kallon Imaan tace "Mu je in ga dakin ki" Imaan ta mike ta nufi sama Inna na biye da ita Mujaheed ya bi su da kallo, Inna ta dinga bin dakin da kallo bayan sun shiga sannan tace "Kina dai sane har yanxu Mujaheed bai maki lefe ba dai koh? Kuma sadakin ma Ahmadu ne ya bada sbda lalacewa, To ba ruwana kada ki yarda ya kai ki ya baro ki sai ya hada maki lafiyayyen lefe irin na Bulasawa gaskiya, don ba sadaka aka basa ke ba" Imaan tayi dariya bata dai ce komai ba, inna tace "Allah kuwa kar ki yarda ya shigar maki daki bai maki lefe ba ya kai ki ya baro ba ruwana" Imaan sai murmushi take Inna ta xauna gefen gado tace "Ita kuma Safara'u kar ki kuskura ki raga mata, ko mi ta maki ki rama ke dai kar ki yarda ta kai maki hannu, da kinga haka ki ja bakin ki kiyi shiru ki gudu tunda ba karfi ne dake ba, Ni fa nayi dambe yyi sau dari da uwar Bala damben mu na karshe sai da na tsaga mata goshi, da tabon ta mutu, Allah dai ya ji kanta ya gafarta mata, lafiya muka xauna da ita wllh matar kirki..." Shigowar Mujaheed dakin yasa inna ta ja bakinta tayi shiru, sai kuma ta mike tana kallon Imaan tace "Ke mu je" imaan ta mike tana murmushi ta fita dakin Inna na biye da ita suka koma parlor suka xauna. Karfe biyar saura Mama Hadiza tace "Toh inna ya kamata mu kama hanya yanxu...." Inna ta katse ta tace "Haba Hadiza da maraicen nan mutum ya kama hanyar kaduna yanda duniya bbu gaskiya ga yan kinnappin da yan fashi kaca kaca a titi??" Mama Hadiza tace "Shi tafiyar minti araba'in din ne dare yayi Inna??" Inna tace "Ni fa tun ina gidan mijina in dai la'asar ya gota to bana bin babban titi" Imaan dai sai murmushi take, Mama Hadiza tace "Abinda nan da yan kwanaki ma xa su dawo kadunan Inna" a fusace Inna tace "Toh me kike nufi? Nufin ki xama nake son yi masu a gida tsofe tsofe da ni koko? Da ba don maraice yyi ba me xan xauna in yi Hadiza?" Mama Hadiza ta mike ta dau handbag dinta tana kallon Imaan tace "Tafi ki ce ma Mujaheed xan koma" dai dai nan Mujaheed ya sakko parlon, yace "Mama ba dai tafiya ba?" Mama Hadiza tace "Wucewa xan yi, sai ayi ta hakuri kuma" Mujaheed ya saci kallon Inna da ta hade rai tana kallon Tv sai kuma ya kalli Mama Hadiza yace "Is she staying here" Mama Hadiza tace "Don Allah ni dai mu je ku raka ni in wuce" daga haka ta nufi kofa, Mujaheed ya kara satan kallon Inna sannan ya bi bayanta, Imaan na kallon Inna murya can kasa tace "Kar ki tafi Inna kiyi xaman ki a nan kin ji" Inna ta tabe baki tace "Yanxu xuwa xata yi ta 6ata ni gun 'yan uwanta su kullace ni ko don ba ni na haife ku yasa suke min walakancin nan oho, bari dai in tafi kada a sa ni a bakin duniya, amma duk abubuwan da na gaya maki kar ki kuskura ki watsar don xa su maki amfani, in sha Allahu nan da kwana biyu tun da naga gida ko shawara da su Ahmadu baxan yi ba sai dai su ga wayam bbu ni, tashi mu je ki rakani...." Imaan ta mike kamar xata yi kuka ta bi bayanta, fuska daure Inna ta shige bayan mota Mama Hadiza dai bata ce komai ba, Mujaheed ya sauke wani boyayyen ajiyar xuciya, Imaan ta fara hawaye Mama Hadiza tace "Meye haka? Bana son shashanci fa" juyawa tayi ta koma ciki tana share hawayen idonta.
Chapter 248 · 0% Book details