← Book details Imaan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 292

Sashe 55

Imaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

shiga jama'a ba sanin cewar bata wani jin dadi, kuma dama bata son tayi stressing kanta ta jogana masu wani ciwon, sai dab da xa a tafi da Amarya Ammi ta tasheta don tun daxu Inna ke cigiyarta, sai a sannan imaan ta shiga bayi tayi wanka ta wanke baki ta fito ta shirya cikin daya daga ankon da suka yi, ta d'an shafa powder tasa eye pencil da chappette, sannan ta dau farin hijab har kasa ta saka ta dau wayarta, ganin missed call ta tsaya ta duba, Sadeeq ne ya kirata, komawa tayi ta xauna tayi dialing, katsewa yyi ya kirata, bayan sun gaisa yace "Ina kika shiga yau" tayi murmushi tace "Bacci" yace "Uhm baki da damuwa, ya su mama?" Tace "Alhmdllh" yace "Daxu Mariya tace min kuna biki gidanku" tace "Ehh haka ne" yace "Shine ba gayyata?" Tace "Uhmm" yace "Toh kin kyauta" a hankali tace "Kayi hakuri, next time" yace "Toh waye next din auren? Ko ke?" Ta xaro ido sai kuma tayi dariya tace "Ni kuma, yar yarinya da ni" yace "Haba?" Tace "Ehh mana" yace "How old are you?" Ta langwabar da kai tace "Na kusa 19 soon" dariya yayi yace "Ehh gaskiya ne, ke yarinya ce sosai ma" tace "Toh kaga" yace "Ko aure aka maki yanxu ma baxa ki haihu ba ai" ta xaro ido sai dai bata ce komai ba tayi murmushi, yace "Yeahh" tace "Xa mu je raka Aunt dina dakinta yanxu" yace "Wani anguwa ne?" Tace "Ban sani ba dai" yace "Toh idan kun je gidan ki kirani" tace "Toh in sha Allah" sallama yayi mata ya katse wayar. Inna ce tsaye tsakar gida ta cakare cikin atamfa England an mata dinkin su irin na tsoffi, ga katon gyalenta ta yafa, ga mutane duk ana ta shirin xa a wuce da seeyama gidanta, motocin dake compound din sun fi shidda duk na daukan yan kai amarya, tun daga nisa Imaan ke jiyo Inna ta tana cewa "Naga abinda ya isheni bai ishi Allah ba, duk an wani yi cirko cirko a gaban motoci ku ja baya mana kar ku gurje masu dukiya in shiga uku, ni wllh saboda bala'in mata ma duk xafi ya isheni abu kamar maita dai, ke Maimuna ba ca nayi ki dubo min Imaan ba ko har yanxu jinin bai dauke ba ne, duk yau ban ganta cikin jama'ah ba ko bakin ciki take ma yar uwartata ban sani ba" Imaan ta turo baki bayan sun hada ido da Innar, inna ta ja tsaki tace "Kai ni dai ko limamin babban masallacin Habuja ne Bukar yau dai baxai hanaki sa gyale ba, duk yan uwanki ga su fess cikin gyale ke ko kin maka hijabi uwa xamu je xaman makoki ba amarya xa mu kai ba haba imaan, ni dai na gaji da maganar ki a gidan nan" Imaan ta dauke kai har ta iso gun motar, wata kawar Umma ce ta xo tayi announcing wai Umma tace wasu su fara tafiya kafin a fito da amarya, nan aka fara kokarin shiga motoci, inna ta bude baki ta gwalo ido ganin wata katuwa cikin shiga ta alfarma da gwalagwalai na kokarin shiga daya daga motocin, cikin daga murya tace "Wayyo meye wannan kuma... Kee don Allah ki bar sirara su shiga, banda neman magana da tsokanar fada ina xa a dake a haka, kisa kike son yi cikin motar fisabillahi, wannan ai sai dai idan ke kadai xa aje a ajiye a dawo to ina kuma hakan xai yiwu tunda motar ba taki bace, fito don Allah mutane su shiga" Imaan ta boye fuskarta da Hijab kar tayi dariya, mutanen wajen wasu sai dariya suke kasa kasa, matar ta fito kamar warce ruwa ya cinye kanta a kasa, inna ta karasa kusa da ita tana kallonta tace "Haba baiwar Allah... ke ba kya tsoron Allah ne wannan abu haka kinyi wani bake bake bayan motar mutane, ina kike son a xuba sauran jama'a, ko ke baki ga irin ki bane" Wata mata ta karaso kusa da Inna tayi kasa da murya tace "Hajiya babban kawar uwar amaryar ce fa" inna ta bude baki tace "Babban kawar uwar amarya kuma sai a sa mata ido ta latse hanjin 'ya yan mutane a bayan mota, dama kisan kai ya kawota ba biki ba, wannan abu kamar giwa kice ta shiga mota, amma bakya tsoron Allah wllh" sum sum matar ta bar wajen, Inna ta ja tsaki tace "Kai sirara su shiga a wuce, ba ruwana a aje a tatse hanjin mutane daga kai amarya ace bikin jikata ga abinda ya faru, to banda gwalagwalan ma duk karya ne ya xa ayi kamar ta ace bata da mota, ke kuma imaan ga motar da xa mu shiga can da Seeyama nace ban son tukin kowa sai na Mujaheed haka kawai mahaukatan abokan angon su ja mu su watsar da mu a rami" Bude motar Imaan tayi ta shiga back seat tana murmushi, Maimoon xata shiga inna tace "Toh ina kuma wancan figaggiyar xata shiga ni patuu, ba ga motoci can ba" Maimoon ta sauka da sauri, Imaan ta dinga dariya har da kyakyatawa, Kamar yanda inna tace Mujaheed ne ya ja su, ita, Seeyama da kawayenta biyu sai Imaan, suna hawa main road inna tace "Toh yau dai Seeyama gashi xa mu kai ki dakin ki, duk da dai mijin naki wani ga6o ga6o ne kiyi masa biyayya iya yanda xa ki iya, ni baxan ce kiyi hakuri yaje ya kashe mana ke ba gaskiya, bbu xancen xaman hakuri, mu dai da aka cuta da hakan aje a haka, amma duk kika ga abinda baxa ki iya dauka ba yafa gyalenki ki dawo gida, ko ki tafi sashin ubanki ko ki tafi sashin kaninsa ko kuma ki yo sashina sai iya Inda karfin mu ya kare na kwatar maki hakkin ki, ni fa tun daga lefen da ya hada maki dama na raina masa aji...." Mujaheed da takaici ya ishesa yace "Haba inna yanxu fada kike mata ko hudubar tsiya?" Inna ta hade rai tace "Ka ji min yaro da aka haifa ina tsaye bakin kofar asibiti daga safe har dare, kai xaka koya min xaman duniya Mujaheed, ko ance maka ban san abinda nake bane, to bari kaji ko kai yau aka daura ma aure iyakar abinda xan gaya ma matar kenan don ni yar gaskiya ce, akan me xa ayi ta wani ce ma mace tayi hakuri gidan miji ana cutarta ana musguna mata, Allah kadai yasan me yasa ya halitto ni a mutan da ba na yanxu ba, kuma ai bance kada tayi masa biyayya ba kawai idan taga xai takata ta gudo gida, ina laifin wannan shawara tawa??" Kawayen Seeyama dai sai kallon inna suke k'asa k'asa, inna ta ja tsaki tace "Tun da shaidan duk na makale gefen xuciyar ku ba dole kaji haushin abinda na fada ba, maxa dai sun xama masifa yanxu, duk halinku daya dama, yo banda halinku daya ya wuce idan yace xai walakanta maka kanwa ka matse gantalalle ka nakada masa duka tunda ga irin sa kamar tsinken sakace, wllh xaka iya dukansa" Seeyama dake hawaye cikin gyalenta ta fashe da dariya, imaan na taya ta, shi dai Mujaheed bai ce komai ba yana mamakin warce Allah ya basu matsayin kaka.....
Chapter 55 · 0% Book details