← Book details Imaan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 292

Sashe 87

Imaan Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Mikewa tsaye Aunty tayi tana kallon Yusuf dake xaune gefen gadonta, shi kam bai yarda ya kalleta ba, Tace "What are you saying Yusuf?" Still ya ki cewa komai, aunty ta dinga kallonsa ko kiftawa babu, can ta ja stool ta xauna tace "Ka daga kai ka min magana malam" Sai a sannan ya daga kai ya kalleta, tace "Are you serious with what you are saying, or should i say are you on ur right senses?" Cikin sanyin murya yace "Sure Mum" Tagumi Aunty tayi tana kallonsa with much surprise, can ta girgixa kai cike da damuwa tace "Kai ma kasan wannan ba abu bane da xai yiwu, ba abu ne mai sauki, haba Yusuf me yasa ka yarda xuciyarka ta yaudare ka da son abinda kasan da wuya ka samu, ko da kuwa kana tunanin xaka samu mai yasa baka tsaya kayi naxarin irin matsalolin dake tattare da samun ba? Wait tukun toh ita Hafsat din fa?" Ya girgixa kai cikin low voice yace "Ku ke tunanin ina son Hafsat, she is just a frnd, bani da intention na auranta...." Aunty ta xaro ido tana kallonsa, can tace "Ikon Allah, i really don't know what to say to you now Yusuf, ban san me xance ba gaskiya, amma ni da xaka bi shawarata ka bar wannan xancen it's something that isn't and will neva be possible, forget this pls son" Yana kallonta da mamaki yace "Why Mum?" Tace "Look Yusuf, Imaan is my daughter, her mother is my very close frnd as well, infact childhood frnd dita ce Aisha, don ta dalilinta na hadu da mahaifin ku har muka yi aure, but... ni xan fi son mu ci gaba da xumunci da Hajiya Aisha as just the frnds we are, and marrying into same family, I mean relationship din mijinta da mijina, amma bana son xumuncin mu ya koma na in-laws, its somehow, that aside Yusuf, kusancin inna da Imaan.... don't misunderstanding me plss son, kai ma inna kakar ka ce, amma gaskiya akwai matsala daga bangaren inna ka bar ni ma in ji da headache daya...." Yusuf ya girgixa kai yace "Kiyi hakuri Mum, I don't think all this u are saying is enough da xai sa ki hanani auren Imaan" Aunty ta bude baki tace "Ni nace xan hana ka aure Imaan Yusuf, idan Allah yyi Ita din matar ka ce ni na isa in hana? Don't quote me wrong plss, amma kai kasan kana son ta me yasa ko sau daya baka taba nuna alamar haka ba?" Yace "That's bcos she is still young, har yanxu Imaan bata san meye rayuwa ba, bata san kanta ba har ynxu, I was thinking idan ta fara jami'a ta d'an yi hankali sai in fito da intentions dina toward her" Aunty tace "Toh Allah ya kyauta, I think it's best ka je ka samu abbanku, amma ni nasan da kyar ne...." Yusuf yyi kasa da kai a hankali yace "Ni dai ki daina cewa haka plss mum, support me sannan ki min addu'a" a sanyaye tace "Toh na daina cewa haka, Allah yayi maku xabi mafi alkhairi Yusuf" yace "Nagode mum" daga haka ya mike ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita, Tagumi tayi tana furta innalillahi.... A xuciyarta. Sake baki Abba yyi yana kallon Yusuf with surprise, shi dai Yusuf bai yarda ya kallesa ba, bayan few seconds Abba yace "Yusuf" Sai a sannan Yusuf ya daga kai da kyar yana kallon Abban nasa, Abba yace "Kana nufin Imaan kake so?" Yusuf ya sunkuyar da kai a sanyaye yace "Ehh Abba" Abba yace "Ikon Allah" Shiru ne ya biyo baya na kusan minti biyu, can Abba ya daga wayarsa yyi dialing number Mujaheed har ya gama ring ba a daga ba, Abba ya ajiye wayar sanin yana gun aiki, Abba yace "I am happy hearing this son, but at the same time I am disturbed coz I made a promise to someone earlier, all the same don't worry, Allah xai shige mana gaba, tashi ka tafi" Mikewa Yusuf yyi ya nufi kofa Abba ya bi sa da kallo yana murmushi. Ko minti goma ba ayi da fitar Yusuf ba sai ga Umma ta shigo parlon Abba cikin shirin fita, har sannan Abba was still pondering at what Yusuf told him, kuma har ransa yake jin xai fi kowa murna da wannan hadin, Auren d'an sa da tillon 'yar d'an uwansa, tunanin yanda xai fara billowa al'amarin yake, first ya fara kiran D'an uwan nasa ya sanar masa sannan su tafi gun Mahaifiyar su ita ma su sanar da ita, yasan Daddy xai yi farin ciki da hadin shi ma, don fargabarsa a ko da yaushe gidan da only child din tasa xata fada da sunan aure, yasan Daddy na son imaan fiye da tunanin me karatu, he can do anything bcos of his only child, Umma Ta karasa cikin parlon tace "Alhaji kasan Mujaheed ya tura min kudi xan fara hada masa lefe, to yau xan fara shiga kasuwa" Abba na kallonta da mamaki yace "What? Lefe kuma? But he told me nothing about that" Umma ta d'an bude ido tace "Toh ba sae an gama hadawa ba xa a kinkimo maka ka gani, kar ya fada maka kayi tunanin ko so yake ka basa wani abun, wllh ban son ya daura maka ko wani nauyi ne kaga ba a dade da hidimar seeyama ba, tunda Allah ya hore masa xai iya komai shi sa kawai nace kada ya gaya maka sai na gama hada kayan a kawo maka ka gani, ba laifinsa bane shi ma ya so sanar da kai na hanasa, amma idan hakan ya bata maka rai kayi hakuri don Allah" Abba yace "Toh Allah ya rufa asiri..." Umma tace "Ameen, tun jiya naga kamar abu na damun ka, shine nace to mai kuma ya faru, idan ma inna ce don Allah a dinga hakuri, uwa ce... Sai ayi ta fatan a gama lafiya da ita, ya ci ace duk abubuwan inna ya xame maka jiki yanxu..." Abba yace "Haka ne" Umma ta xauna ganin maganganunta sunyi tasiri xuciyar Abba, murya can kasa tace "Toh me kuma take so Alhaji?" Abba yace "A'a wannan mun shawo shi tare da Sadeeq, Yusuf ne dai ya xo min da wata magana yanxu da ya kulle min kai... Am still trying to find a way out ne har yanxu" Da mamaki Umma tace "In ji dai lafiya??" Abba yace "Lafiya lau, yar uwarsa Imaan yake so da aure wai" Mikewa Umma tayi da mugun mamaki baki bude tana kallon Abba, can tace "Aure kuma Alhaji??" Abba yace "Kwarai, yanxu ma ya bar parlon nan" Umma tace "Ikon Allah.... Aure fa???" Juyawa tayi ta nufi kofa tace "Toh Allah yayi mana mai kyau dai, ya xaba abinda ya fi alkhairi, ae imaan yar uwar sa ce, Imaan ta mu ce..." daga haka ta fice, direct sama ta wuce ta bude dakin Yusuf ganin baya ciki ta shiga dakin Aunty, xaune ta samesa tare da Aunty, Umma tace "Amma Yusuf kayi asara wllh, ka kuma samu tabin kwakwalwa mai wuyar ganowa balle ayi maka magani, yanxu ka rasa warce xaka je kace ma Ubanka kana so sai Imaan, Yusuf me ya same ka ni Rukayya?? ina ita Hafsar da kake nema take??" Yusuf dake kallonta yace "Umma ni Hafsat ba aurenta nace xan yi ba" Salati Umma ta saki tace "Amma Allah ya isa tsakaninmu da kai, mu xaka ka ma bakin ciki Yusuf?? ka bar 'yar attajiri ka dawo kace mai lalura iri iri kake so? Anya akwai lafiya kuwa, mu xaka kwaso wa mugun iri, irin ciwo a xuri'ar mu? Yarinya mutu kwakwai rai kwakwai?? Toh wllh tunda an asirce uwarka ta kasa cewa komai ni kam ba a asirce ni ba sai inda karfina ya kare in sha Allahu, yanda xan ma Mujaheed haka xan maka don duk daya ku ke a gu na, in sha Allahu sai naje na gano tushen abun nan... Ba wanda ya isa ya ci nasara a kanka kamar yanda aka ci a kan kanin Ubanka, uban kuturu yyi kadan wllh balle na makaho" daga haka ta fice a dakin kamar xa ta tashi sama, Aunty da ta bude baki tana ta kallonta tace "Ikon Allah ya fi gaban haka...."
Daddy couldn't help it but laugh bayan Abba ya xo har part dinsa ya sanar masa intention din Yusuf a kan Imaan, Daddy yace "Ikon Allah, nayi farin ciki sosai sai dai kar ka mance da alkawarin da kayi a baya barrister, ko ya xa mu yi?" Abba yace "Sure ina sane, shi ma ba wai xa a dakatar da shi bane Sadeeq din, abinda xai faru yanxu kawai mu fara xuwa gun Inna mu je ta bakin ta kafin a yanke ko wani decision" Daddy yace "Gaskiya ne wannan" Part din inna suka tafi a tare, Inna ta fito daki tace "Tun safe in gaya maku nake aiki ban xauna ba, ku leka bandakina ku ga ko tuwo ya xube kasa xa a iya xaunawa a cinye tass, ba ku ji bayana ba kamar ya balle ni dai in huta" Murmushi duk suka yi suka xauna, Daddy yace "Gwara dai ki dinga hutawa haka inna, gashi kince baki son mai aiki balle a samo maki ko yar dattijuwa ce" Inna tace "Ni ko ina xan so masu aiki mutane duk wari, sannan su cinye ma mutum abinci, A'a ba ruwana ni ko da rarrafe ne xan yi aikina, 'ya yanku ne sun xama abun tsoro banda haka Imaan ko Maimoon ko Ummi baxa su dinga xuwa min d'an share share ba banda karshen duniya da lalacewa ta xo" Abba yace "Inna ke fa kika ce baki so, ai da suna xuwa..." Inna tace "Ehh ni nace bana so, don ba abinda suka iya gaskiya, basa min yanda nake so, ni dai nace na yafe su daina xuwa" Duk suka yi shiru basu ce mata komai ba, ganin ta dauko tsintsiya Abba yace "Inna daxu Yusuf ya sameni kan wata magana da naga ya dace mu sanar maki kafin mu yanke hukunci...." Ajiye tsintsiyar tayi ta xauna kan kujera da sauri tace "Me ya faru kuma??" Abba ya d'an yi murmushi yace "Wai yar uwarsa Imaan yake so da aure...." Inna ta gwalo ido ta saki baki tana kallonsu, saukowa kasa ta yi a hankali ta xauna kan rug ta fashe da matsanancin kuka tana tafe hannu tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, LA haula wala kuwata illa billahil Aliyul Azeem, la ilaha ilallahu Muhammadurrasulillahi sallallahu alaihi wassalam, hasbunallahu wa ni'imal wakeel.... Na ga abinda ya isheni ni patuuu" Daga Abba har Daddy kallonta suka dinga yi da mamaki, inna ta dakatar da kukan da take tace "Toh da kyar idan Imaan bata ta6a shan nonon Amina ba ma, yo ta ma sha ne kawai... Idan xa kuyi ta kanku kuyi ta kanku"
Chapter 87 · 0% Book details