← Book details Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 136

Sashe 97

Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya karasa yana kai kafarsa ya shuri motar Ahmad, har lokacin Ahmad be kula shi ba, sai da motar soja ta iso, da hannu Ahmad ya nuna musu Aminu.

“Ku masa shegen duka sai ya dawo hayyacinsa”

Ba ni kadai ba duk wanda ke a titi kallon motar sojojin yake, a yadda naga yana wayar na dauka police zai dauko ashe uban police ne, kamar sun samu nama haka suka ka kama Aminu, suka ci kwalarsa amman be daina bala'in ba.

“Ni zaka saka a ciwa mutunci? Sai na wulakanta ka wallahi, ka shirya haduwa da ni...”

Ko da suka saka shi motar har sun fara dukanshi. Mutane sai bin motar sojojin da kallo suke kamin su juyo kan mu kallo ya dawo gurinmu. Ba mu bar gurin ba sai da Ahmad ya kira direbansa ya tafi motar Aminu sannan ya shiga tashi motar yai mata key.

“Kin yi kokari haka kika zauna da mahaukacin nan? Be cancanci mata irinki ba, tun farko ya kamata ayi bincike kamin a aura masa ke, how will you face the world ki ce wannan uban yayanki ne? Wani irin hauka yake haka?”

Ni dai bance uffan ba bayan hawayen da nake.

“Shiyasa yake cin zalinki, komai akai miki sai kuka da abun dariya dana bakinciki ko wane kuka dai i wonder how your next husband will handle you”

Ya fada da kamar fada, sannan ya faka motarsa gefen titi ya fita, ya bar ni a cikin motar ni kadai. Tun ina hawayen da gaske har ya daina zuwa sai da ya leko ta gilashin motar ya kalleni sannan ya bude ya shigo muka cigaba da tafiya. Asibitin da aka taba kwantar da ni a lokacin da Baba ya rasu ya nufa da ni, sai da ya faka motar sannan ya zagayo side dina ya bude min motar ba tare da yace min komai ba, ni kuma na saka kafafuwana waje na fito sannan ya rufe motar yana gaba ina biye da shi har muka shiga cikin asibitin, har office din likitan muke da kansa yaja min kujera ya zauna sannan ya zauna a dayar kujerar ya risino yana kallona.

“Bari likitan ya zo yanzu kin ji? Sannu”

Ya kasa dauke idonsa a kaina ni kuma na gagara daga nawa idon na kalleshi.

“Ji yadda ya gusar da farincikin da kika ji dazun, cikin kankanen lokaci, ina mamakin yadda akai kika auri mutunen nan tun farko....”

Ya fada yana kallon likitan daya shigo office din, wacan likitan ne dai wanda ya duba ni a wacan karon. Sai ya daga fuskata ya duba goshin nawa sannan ya tambayi abunda ya faru.

“Buguwa tai ta murfin mota”

“Ayyah sannu”

Ya fada sannan ya juya ya fita, ba dade ba ya dawo dauke da wani karamin akwaiti sai ya hanyo dayar kujerar ya zauna.

“Cire Hijabinki”

“Ba sai ta cire ba”

Ahmad amsa masa tun kamin nai wani unkuri.

“Indai gyaran kake so a mata dole sai hijabin ya matsa daga goshinta”

Doc Nura ya fada yana kallonsa, sai ya taso ya karaso kusa da ni, ya daga fuskata sama ya saka hannunsa ya janyo hijabin nawa ya raba shi da fuskata kamar zai cire sai kuma naji ya yagashi, sannan ya maida min shi a jikina ya zamana kaina na iya wucewa hijabin ya sauko saman wuyana.

Murmushi kawai likitan yai ya dauko safar hannu ya saka sannan ya soma gyara min goshin, idan naji zafi sai ya rumtse ido and Ahmad na kusa da ni yana min sannu. Bayan likitan ya gama ya saka min bandeji sannan ya rubuta mana magani.

“Zaki iya jirana a mota”

Ya fada yana mikomin key din motar, ba musu na karba na juya na fito daga office din, ina tafe ina tunanin haukar Aminu har na isa gurin motar, amaimakon na bude na shiga ciki na zauna sai kawai na zabi tsayawa har ya fito, ya dauki lokaci a ciki kamin ya fito ya nufo inda nake tsaye jikin motar, hannu ya miko min na bashi key din ya bude ya shiga sannan nima na shiga.

“Kika yi ta tsayuwa waje? Ko baki iya budewa ba ne”

“Na iya”

Kallona yai kamar zai yi magana sai kuma ya dauke kai yai ma motar key muka kama hanya, ba kai ni gida ba sai da ya biya ta wani shopping yai min siyaya sannan ya shiga da ni cikin unguwarmu.

“Ban san ko kina son na kai ki har kofar gida ba ko kuma na aje ki a nan”

“Nan din ma yayi na gode sosai, dan Allah kai hakuri da abunda Aminu yai maka....”

“No karki damu, ni be min komai ba”

Ya mika hannunsa baya ya dauko ledodin ya miko min.

“Ki rikawa yara wannan, and ina son na yi miki maganar karatunsu?”

Na masa kallon rashin fahimta.

“I mean idan kin amince i will take them back to Gwarzo International school”

“A a suna makaranta a yanzu, da na yi deciding na canja musu sai kuma na yanke shawarar kara na bari har su kai Secondary school sai na nema musu private”

“Baki son makarantarmu ne? Then i will pay su shiga wata private school din”

“Ba haka ba ne...”

“Ba haka bane minene?”

A yadda na lura Ahmad yana daya daga cikin irin mazan nan masu saurin fushi, kuma abun kankane kan iya bata masa rai, domin tun kamin na karasa ya tari numfashina cikin muryar dake nuna fusatarsa a fili, jin na yi shiru ina kallonsa sai yai sauke ajiyar zuciya ya fara magana slowly.

“Kin dai ga mahaifinki ba wani kula zai yi da su ba, ke kuma a yanzu kina neman mai taimaka kiki ne, to miye a ciki dan na dauki nauyin karatunsu? Uba kamar wannan? Zai tsaya ya damu da rayuwarsu ne ma balle karatu? Idan mutum ne mai hankali da natsuwa zai same mu a titi ne yana ihu and called you his wife? Imagine?,  i said idan makarantar ne baki gamsu da ita ba zan iya biya su yi wata makarantar, idan kuma taimako na ne bakya so then get out of my car”

Ya karasa fuskarsa babu alamun wasa, ni kan kallonsa kawai nake mamaki cika ni, to ana taimako dole ne? Idan ya maida su a makarantar wani abu ya faru sai kuma a sake ciresu? Bana son yawo da karatunsu a yanzu domin shine rayuwarsu. Bude motar nai nai fita.

“Okay fita kika yi? Fine...”

Jin ya fadi hakan yasa na dawo cikin motar na zauna cikin damuwa.

“Nace ki fitar min daga mota”

Yawun bakina na hade na na kalleshi a natse nace.

“Ba wai bana son karatun nasu ta dalilinka ba ne, bana abunda ya faru da su a baya ya sake faruwa yanzu, ko a da na dawo gida a lokacin da aurena ya mutu Abdallah ne yake kula da su ya saka su a makarantarku, daga baya kuma sai ya cire su wanda hakan be min dadi ba, a dole tasa na dawo da su makarantar gwannati”

“Sai kuma aka fada miki kowa kamar Abdallah ne idan na saka sun cire su zan yi”

“Shi ma ba da son ransa ya cire su ba, mahaifiyarsa ce ta cilasta shi saboda bata son alakar da ke tsakaninmu, bana son hakan ya sake faruwa”

“Babu abunda zai sake faruwa, Hajiya bata da matsala da ke, kusan ita ta fara min magana tun kamin na yi tunanin yin haka, so if you want zan aiko direba gobe ya dauke su, idan kin yi shawara pls let me know”

Ya karasa yana miko min katinsa. Na kalli kattin kamin na kalleshi na ce.

“Na amince”

Murmushin yai har lokacin be janye katin daga miko min da yake ba, wata kila son yake na kira so that ya samu Number na, domin tun da nake a rayuwata be tana kirana ba bamu tana waya ba.
Ganin na ki karba yasa ya maida katin ya aje, ni kuma na rufe masa motarsa, na kama hanyar gidanmu na barshi a gurin tsaye ni dai har na shige gida ban ga motar ta bar gurin ba.

  Ina shiga gida hankalin kowa ya tashi ganin goshina da bandeji. A falon Inna na zauna ina labarta musu a abunda ya faru.

“Kai amman wannan mutunen ya burge ni, ai daman Aminu daidai ne ya samu mai cin ubansa....”

Hafiza da fada cikin jindadi, kamar daga sama muka ji Namra dake sanye da uniform ta fashe da kuka. Husna ta nuna da hannu tana fadin.

“Kin ga wacan kin ga wacan munafukace, ke yanzu duk abunda ubanki nai muku har son shi kike?”

Mama ta tari numfashinta tana fadin.

“Karki ga laifinta a duk yadda uba ya lalace ko uwa ta lalace ko da ya lalace akwai kauna a tsakani kuma baka son wani abu ya same shi, amman dai yakamata ki masa magana kar ya saka su masa mugun duka fa su ji masa ciwo ko su kashe shi ma”

Sai a lokacin wannan tunanin ya zo min, kar su masa dukan mutuwa laifi ya dawo kaina, daman kuma ga halin da nake ciki, ko kuma shi Ahmad din na ja masa matsala.
Haka na wuni da tunanin abun, sai a lokacin na ji haushin rashin karbar number sa da ban yi ba. Bayan an sallame sallah magariba Mama take min wata magana wacce ban taba kawo ma kaina ba.

“Halimatu, ya kamata ki daina shiga motar maza haka nan, ba mutuncin ki ba ne, yanzu ne sai ki ji mutanen unguwa sun fara magana, ni kaina ba zan so ace yau kina cikin motar wannan gobe kina wannan ba inda ba ta kama dole ba”

Gaskiya ta fada min wacce babu mai fada min ita sai mai kaunata, be kamata ina shiga ko wace irin mota ba, na sani yanxu ne sai a fara magana a unguwa ana cewa na lalace ko kuma ina jaye jayen maza barka, wasu ma kan iya dogara da cewar ganin mahaifina baya raye ne.

“In-Sha-Allah zan kiyaye Mama, amman yana da wahala na shiga motar wani idan ba da wani dalilin ba, amman duk da haka zan kara kiyayewa”

“Hakan yayi, Allah ya fito miki da mijinki na gari ki yi aure”

“Amin”
Chapter 97 · 0% Book details