← Book details Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 113 OF 136

Sashe 113

Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

“Abokina ne more than 11 years, na hadu da shi a Lagos, a lokacin da naje gurin hutu, a hotel din da na sauka daki daya muka zauna a lokacin, kasancewar babu dakuna da yawa a hotel din, kasancewar ana bikin nada sabon sarki a garin, and hotel din da muka sauka kusan duka an kama dakunan ciki kasancewar ta babbar hotel, we share the same room and he is the one da ya biya komai, ya sake min sosai we exchange our numbers, lokaci zuwa lokaci mu kan hadu, some time kuma a waya, saboda shi police ne yana yawo gari gari, shakuwarmu tasa muka fahimcin juna sosai duk kuwa da kasancewar ba Addininmu daya ba, shi ya fara dorani akan sana'ar siyar da motoci, shi ya nada min jari duk da a lokacin ba wai bana da kudin ba ne, kawai dai bana ra'ayin abun ne, bayan mun fara sai ya sake nuna min wannan hayar, ban dubi hadarin da ke ciki ba sai na kalli yawan abunda zan samu, sannu sannu na fara tun ina yi ina jin tsoro har na daina, sai duk irin alakar da ke tsakanina da shi, ba kowa ya san muna abota ba, saboda abu ne da ke bukatar sirri idan aka ga alakar ta yi aminci sosai za a fara zarginmu, that's why idan zamu hadu sai dai mu hadu a sirrice, har Allah yasa ya dawo garin nan da aiki”

Yayi shiru tare da kawardar da fuskarsa.

“Amman ka san cewar  Abraham ne mutumen da yai min fyade?”

“Na Sani, ko da Abdallah ya fada min na sani”

Ya amsa ba tare da ya kalleni ba.

“After na rabu da ke, na gano cewar shine saboda ya fada min yasan wandanda suka kashe Alhaji Sama'ila na yaddo, and you told me on that very night suka keta miki haddi, and guess what a wannan daren ya shirya kashe ni ne, saboda babu amana a tsakani, wanda ni ba zan iya hakan ba, shi yana ganin kamar na karbe masa jama'a na fishi samun kudi, domin shi wasu mutanen suna tsoron mu'alama da shi ganin cewar Jam'in tsaro ne, kai tsaye na tuhume sa da cewar shi ya keta miki haddi kuma ya amsa min da cewar yes shine, and now yana neman inda zai same ki ne, saboda kin ci ciki bayan shi be taba kwantawa da mace tai ciki ba, and he already know ni bana da lafiya”

“Amman baka taba fada min ka gano shi yai min fyade ba, baka nemi afuwar kazafin da kai min ba, ba ka wanke ni a idon mahaifiyarka ba”

“Komai ya riga ya lalace Haima, a lokacin na gano cewar Abdallah yana son ki, Hajiya tana kin ki, kuma na san ba zaki tana dawowa a gareni ba, saboda ni ba zan iya komai da mace ba, shiyasa na bukaci boye soyayyarmu tun farko bana son wannan sirrin ya bayyana, gano cewar Abdallah yana son ki shi yafi komai bata min rai, kuma lokaci ya kure Haima komai ya lalace, na kasa yarda da ke na rabu da ke, and silata abokina ya keta miki haddi”

Hawaye ya fito daga idonsa.

“A lokacin ne na gano cewar na rabu da matar da ba zan taba samun irinta ba har na mutu, na rasa komai ba ni da mata ba ni da yaya, babu irin neman maganin da ban yi ba amman na kasa samun lafiya saboda Abdallah”

Ya karasa yana murmushin bakinciki wanda hausawa ke cewa yafi kuka ciwo, sai ya kalleni.

“You got lucky za ki auri mutunen da zai ba ki abunda ni da aminu muka kasa ba ki.... And the way da ya dage da neman tona sirrinmu i know yana son ki sosai”

Waiga nai da zimmar na kalli Ahmad amman sai ban ganshi a gurin ba.

“Ba so na yake, abunda kai min kai da Aminu ya tsorata ni daga son wani ko aure a yanzu, murum data na yarda da shi a rayuwata Abdallah shi kadai nake da tabbacin na zai cutar da ni ba....”

“And you can't marry him....”

Ya fada kai tsaye yana kallona da murmushi a fuskarsa hawaye na sauko masa.

“Ba zai yiyu ki aure ni ba, kuma ki auri twina brother dina, bayan kuma ina raye, Hajiya ba zata yarda ba, hakan kuma na zai kara min komai ba sai tsanar Abdallah, and i know duk yadda za ki so shi ba zaki so shi kamar yadda ni kika so ni ba, I'm your first love i know ko yayana wata rana sai kin ji so a zuciyarki kamar yadda ni ma ba zan iya cire soyayyarki a raina ba, so you can't marry my brother kuma ki rayu da so a zuciyarki, no matter what Abdallah zai baki Hajiya ba zata tana son ki ba, saboda tana ganin kin shiga tsakanin yayanta”

Mikewa nai tsaye sai shima ya mike.

“Ban sani ba ko zan sake ganinki ko a a, ban sani ba ko za su yanke kin hukuncin dauri rai da rai ne ko kuma za su halbemu ne i don't know, but i wish you all the best in your entire life, and I'm sorry for what I did”

A lokacin ne hawaye ya fara sauko min kamar ba gobe, tausayinsa ya rufe ni ya sadakar ya san cewar kashe shi za ayi kenan, maganganunsa suka rika min yawo a cikin kai, cewar ba shi da mata ba shi da yafi komai tsaya min a rai, kasa tafiya nai sai kallonsa nake ina hawaye kamar yadda shi ma ya rika waigena yana kuka kamar ba shi ba. Har na nufo inda motar Ahmad take na bude na shiga ban daina hawaye ba, yana kallona hankalinsa ya tashi.

“Me ya faru? Mi yai miki?”

Kasa magana nai sai kokarin saida hawayen nake, hakan yasa shi fusata ya bude motar sai fita nai saurin riko rigarsa ina girgiza masa kai.

“Be min komai ba”

“Then why are you crying?”

Na yi saurin share hawaye.

“Ba komai”

Kallona yai for a moment sannan ya rufe motar muka kama hanya, sai da muka hau titi ya dauko ruwa ya miko min, na karba na bude ya sha ruwan sosai sannan na rufe na aje. Har muka isa gida ban ce masa komai ba shi kuma be fasa kallona ba, bayan yayi farkin na fita cikin motar.

“Thank you”

Na furta ba tare da na jira abunda zai ce ba na shige cikin gidan, a wunin ranar sai na kasa sukuni cikin abunda nake tunani har da zancen samun lafiyarsa wanda yace Abdallah ne, kamar ya? Shi ya masa wata allurar ne ta zame masa haka? Amman Abdallah ya san da da wannan kuwa? Mi zai saka yayi masa haka?
Kamar ya san ina tunaninsa sai akai sara ka gaba, kiransa ya shigo wayata, sai dai wannan karon kasa daukar wayar nai har tai ringing ta katse sai ya sake kira sannan na dauka. After mun gaisa yace min.

“Abdulhamid yace kin je gurinsa yau”

“Eh”

Na amsa masa a takaice duk da na san ya kira ne saboda ya san dalilin zuwana.

“Okay”

Har zai aje wayar na ce.

“Abdallah zan iya tambayarka wani abu?”

Shiru nai na wani lokaci har sai da yace.

“Ina jin ki”

“Da gaske kai ne silar ciwon Abdulhamid?”

Shiru yai daga can cikin wayar sannan kamin ya aiko min da tambaya.

“Kamar ya?”

“Ya fada min kai ne sila, taya?”

“Magana ce mai tsawo Halima zan na same ki gida daman akwai maganar da nake son yi da ke”

“Ka fada min dan Allah, zuciyata ta kasa yarda kuma na kasa natsuwa”

Ina jin yadda ya sauke ajiyar zuciya sannan yace.

“Abun ya dade tun muna samari ne, na tashi da son yara musamman maza, and Abdulhamid ya san da haka, kamar wasa wata rana muna magana nace masa zan riga shi aure, shi kuma yace ko na riga shi aure ba zan haifi namijin da nake da buri ba, ni kuma na ce masa shi kuma ba zai ma taba haihuwar ba har sai na haifi namijin, and na gano haka ne after Suwaiba ta fara haihuwar Mata, and last barin da tai ma macece, yayi min kofi ne and after that Hajiya ta ba mu maganin kare kofi saboda abubuwan da suke faruwa, na shi ya kare nawa kuma ya rage kaifi that's what i know”

***
( Wannan abun ya faru a gaske, Hasana da Husaina, Husaina tai ma Hassana kofi cewar ba zata taba aure ba, ita kuma Husaina tace mata ko tayi auren ba zata taba haihuwa ba, har yau kuma suna nan da rai sun fara manyanta Hassana ba tai aure ba Husaina kuma bata haihu ba)

***

Ajiyar zuciya na sauke ina mamakin yadda sukai wa junansu illa.

“Zan zo gobe akwai maganar da nake son yi da ke”
Chapter 113 · 0% Book details