← Book details Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 136

Sashe 15

Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga kaina nai na kalleta, ban san abunda take hango min ba na kokarin hanani yin komai akan abunda akaiwa Namra, na san tana gudun zaman gida a gurina kuma tana jin kwatankwacin zafin da nake ji na baro yayana a wani gidan, amman har yanzu na kasa gane dalilin na son boye maganar, indai na janyo ma yayana tsanena ina ganin kamar ba hujja ba ce.

“Ko wace Uwa Mama tana goyon bayan abunda yayanta suke aikatawa ko da kuwa abun nan marar kyau ne, na kasa ganin kuskure abunda nake son aikatawa, na san kina min tunanin mutuwar aurena ne, amman tabbas aurena mutu ko da ta wannan dalilin ba, duk yadda kike jin zafi idan wani abun ya same ni haka nake jin zafi idan ya samu Namra, saboda nima uwa ce, kin taba fada mana cewar saboda mu kika zauna da Abbah a cikin lalurar da yake ciki ta rashin lafiya, mama ya dan Allah ki fahimta nima saboda Namra ne, kuma ba dan bana son aurena ba sai dan ganin kamar mutuwar auren a yanzu zata fi sauki sama da idan yayana suka girma, Mama Aminu ya sake ni akan be yarda da abunda na fada ba, ba wai ma ya roki na boye sirrin ba ko kuma ya roki kar na kai kotu ba, mahaifiyarsa har ikirarin cewa tai sai an kaiwa Sadi Namra ya rikata sai dai na mutu, Mama ina kuke son na saka kaina na ji sanyi? Me kuka son nai a duniyar nan?”

Wannan karon hawayene yake zuba a idon Mahaifiyata, na sani kalamaina sun ratsata matuka kuma ta fahimci inda na dosa.

“Kwatarwa yarki hakki abu ne mai kyau Halimatu, amman kwatar hakki a inda kwatar yafi rashin kwatar alheri to barin shi ya fi, idan kika kai maganar nan kotu kin sani Sadi da yan'uwansa ba yarda za su yi ba, kuma za su yi komai dan su wanke shi ciki har da mijinki tunda kin ce be yarda da abun ba, daga haka maganar zata tashi sama kanki ankaro an fara buga ku a jaridu ana fira da ku, kamin a kwato miki hakkin ki sai kin sha wahala, idab kikai nasa a hukunta na shekara daya ko watanin kadan me akai kenan? Idan kuma ba ki yi sa'a ba sai a kori kararku bayan na gama fadar kin batawa yarinya suna, irin wannan abun Halimatu rufewa ake saboda rayuwar yar ki a nan gaba wa zata aura? Wa zai aureta? Mi zata je ta tarar? Ina hango miki abunda zai zame miki matsala ne nan da wadansu shekaru masu zuwa wanda ke ba zaki gani ba a yanzu, zaki batawa yarki sunane kawai a cikin kawayenta yan'uwanta da kuma wandanda zata hadu da su nan gaba, ke da Hafiza da Doc Abdallah kun kasa fahimtar abunda nake nufi ne kawai wata kila sai nan gaba, shi ma abunda ya zo yana min magana akai kenan? Wa be kamata a kyale wannan maganar ba, ni kuma na fada masa indai da yawuna za aje kotu da wannan maganar a matsayina na mahaifiyarki ban yarda ba!”

Kamar wacce aka saka da mashi haka magana Mama ta ratsa kirjina ta shiga har cikin kaina, tsakanin maganar fyaden da sakin da Aminu yai min da kuma maganar Mama sai na rasa wane yafi yi min zafi a kirji.

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u”

Na fada ina jin kirjina kamar zai fashe zuciyata ta fito waje, muna haka Baba ya shigo dakin yana turo wheelchair dinsa Inna na bayansa tana hawaye shu kuma fuskarsa na nuna tsantsar damuwar da ke tattare da shi. Ina kallonsu sai ya tuna min da wacan lokacin na baya lokacin da aka dura aurena da Aminu, lokacin da ko wace fuska take dauke da murmushi da annashuwa da jindadi.

“Halimatu ya akai hakan ta faru?”

Ban boye masa komai ba ciki har da ikirarin da Hajiya tai na kaiwa Sadi Namra ya rika.

“Wannan maganar banza ce! Taya zai sake ki ba tare da sauraren gaskiya ba kuma be yi bincike ba sannan ya ce zai dauki yaya ya kai wa kanensa? Babu wanda ya isa ya rabaki da yayanki a nan za su zauna tare da ke idan kuma yayi musu kotu zata rabu mu da shi, domin yanzu babu sauran mutunci a tsakaninmu da shi, duk abunda yake takama da shi sai na gani!”

Baba ya fada cikin fushi da daga murya kana kallonsa kasan ransa ya bace sosai, wanda ban yi zaton haka ba domin yana da wahala ka ji bakinsa maganar zamana da Aminu bayan ki yi hakuri aure sai da hakuri, na ji sanyi sosai kuma ina jin na samu kwarin guiwar rike yayana da kyau domin na samu mai goya min baya.
Sun dade suna da maganar aurena da Aminu tun daga kan haihuwa ta ta fari har zuwa yau abubuwan da sukai ta faru da kuma abubuwan da suke gani ko ji, ni dai ban ce uffan ba domin har lokacin da kennana suka shigo suka saka baki ana yi da su ban ji ina furta ko da sunan Aminu ba a zance balle kuma har nai wata firar abunda ya shafeshi, sannan suna yi an saboda su nuna min kar na damu akan abunda ya faru.

Sai kuma sha biyu sannan kowa ya nemi gurin kwanciya, a lokacin Amal ta dade da bachi a kirjina, sai da na kwantar da ita a kasa saboda fitsarin da take sannan na fito falon Mama neman su Adnan.

“Ai tun dazun Abdallah ya tafi ta su gidansa, yace can za su kwana”

Mama ta fada.

“Har da Namra?”

“Eh har da ita”

“Akan me zai tafi da ita bana son tana rabar kowa a yanzu bari na kira shi...”

Ina juyawa Hafiza ta kirani.

“Anty Halima dan Allah karki kira shi yanzu, kin san dai indan kowa zai lalata miki yara ban da Yaya Abdallah, kuma saboda yana tausayin yaran yai so karki bashi kunya a yanzu”

“Bana iya yarda da kowa akan yarana yanzu, indai har kannen mahaifinsu zai iya yin wani abu na lalata da Namra, to kowa ma zai iya lalata da ita, rayuwar ya mace a yanzu tafi ko yaushe bukatar tattali, idan na nesa be lalata maka ita ba, na kusa zai iya samu damar hakan, idon kowa ya rufe a yanzu Hafiza, ba zaki taba gane abunda nake nufi ba har sai kin yi aure kin haihu sannan za ki gane tarbiya da tsare yaya abu ne mai wahala, ban son na sake aikata kuskuren da na aikata na barin Sadi da yarana har ya samu damar yi min tabon da ba zai gogu ba har na koma ga mahallincina, da na san cewar zuwa na gurin aiki zai haifar da haka da ban yi aikin ba, da na zauna da yayana a ko wane irin hali, a ko da yaushe ina aina yadda Namra zata ji idan ta girma ta samu irin wannan labarin, ida na kuma na sake bari wani ya sake faruwa? Laifin akan wa zan dora shi?daman tun farko be kamata na yarda da kowa akan yayana ba”

Na karasa tare da saka hannuna na share hawayen idona, sannan na kai dubana gurin mahaifiyata wacce ke kallona fuskarta da murmushi.

“Kinji kwatankwacin abunda nake ji a lokacin da kike budurwa ke da yan'uwanki da kuma yadda nake ji a yanzu da nake tare da kanenki, a kullum ina cikin fargaba da tsoron kar wani abun ya same su kar wani ya lalata musu rayuwa, ko daga nan zuwa gidanki suka fita hankalina a tashe yake har sai sun dawo sannan na ke samun natsuwa, shiyasa a kullum bana da burin da ya wuce ko wacce na ganta a dakinta, Halimatu kina jin abunda na ke ji a matsayina na uwa, ke ma uwa ce”

Dan murmushi nai kadan sannan na nufi dakinta na kwanta a kusa da Amal ina ta kallon fuskarta, kamin na sake tashi na nufi inda handbag dina take na dauko na danna number Abdallah sai na jita a rufe wata kila ya rufeta ne saboda ya san zan kira ko kuma ya saba rufe idan zai kwanta ne oho.
A wani abun mamaki a daren sai na kasa runtsawa har safe, bachi ya kauracewa idona ba dan kuma ina tunanin komai ba, domin ban ji tunanin kowa ya zo min rai ba a wannan daren sai Allah ya saka min saukin abun har na ke jin kamar bana da damuwa a tare da ni.
Misalin hudu saura na asuba na tashi na shiga bandakin domin yin alwala nai nafila kamin ayi assalatu, ina tsugunawa gurin fitsari sai jini ya fara min zuba a madadin fitsarin, sai da ya zubo min da dan yawa har da sare sannan nai fitsarin na wanke na tashi sai na ji abun be tsaya min ba.
A dole na nufi dakin kanena na tashi Marwa ta bani pad na saka sannan na dawo na zauna na dauki carbi Mama ina ta ja, marata na dan murda min kadan-kadan.

Haka nai ta dauri har kusan takwas da yan mintuna na safe, ina bawa Amal koko wayar Abdallah ta shigo.

“Hello Assalamu Alaikum”

“Wa'alaikissalam Momy ina kwana?”

“Lafiya kalau Namra an tashi lafiya?”

“Lafiya Kalau”

Ta amsa min da muryarta radau har tana yar dariya.

“Momy ga maman su Nabeela”

Ta mikawa matar Abdallah wayar muka gaisa, sannan ta bawa su Adnan da Aiman, daga bisani ya karba ba tare da ya min magana ba ya kashe wayar. Number Hajara na kira na labarta mata abunda yake faruwa sai ta saka salati da sallami tana fadin sai ta zo. Bayan na gama da matsalar Amal na aika yaro aka siyo min pad da pants a shago na shiga nai wanka na fito na saka tufafin jiya, sannan a shiga dakin Baba na gaishe shi tare yi masa ya jiki.

“Al-hamdulillah, na yi waya da Almu direba, zai zo anjima kadan sai aje kwaso miki kayanki, makulin gidan yana gurin Aminu ne?”

“Eh dayan yana can daya yana gurina”
Chapter 15 · 0% Book details