← Book details Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 136

Sashe 42

Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Ba ni bace ni ban kai komai a page ba.. ”

“Ba ke bace wacece? Taya za asan da labarin idan ba ki fada ba? Har da sunan Namra? Da maganar School fees? Haka kawai ki dauki maganar da an riga an yi ta ki saka a media? Wace irin shawara kike nema? Kin san mutane sai zagina suke, a ina za su sama miki mafitar? Kina tunanin idan Halima ko Abdulhamid suka ga wannan ya za su ji? And look at the way da kika fadi labarin is like zargina kike ma? Kin ja ana ta tsina mana alrbaka ni da ita”

“Maganar kenan Halima Halima....”

Ya kara matsowa kusa da ita yana nuna mata wayarsa da ke hannunsa.

“Yes Halima Halima, Halima yar uwata ce, kuma ni ba mazina ce ba ne, ban nemai matan waje ba ma babu yadda za ayi na nemi yar'uwata yar'uwar ma matar dan'uwana, ko a lokacin da Halima take gidan Aminu ban neme ta ba balle yanzu da take auren dan'uwana, ni ba mahaukaci ba ne kuma na jahili ba ne ba zan taba neman aikata Zina da Halima ba har abada! no matter how much I love her, ki shiga hankalinki karna sake jin sirrin gidan nan a media”

Yana fadar hakan ya juyawa ya fice daga dakin cikin bacin rai. Second to last sentence na sa ya fi komai rudata ya yanke mata hanzari kuma ya jefata a duniyar tunani.

‘No matter how much I love her....’

Those that means Abdallah yana son Halimatu? Zargin da yan comments suke ya zama gaskiya kenan? Cewar da suke yana son ta ne wasu kuma na fadar cewar yana tarayya da ita ne ya zama gaskiya kenan? Ada kam sam ita bata kawo ma kanta wannan tunanin ba, ta fi zargin ko Abdallah yana son kanenta ne, amman yanzu kam gaskiyarta fito. Da sauri ta kunna data ta shiga page din da ta tura neman shawara ta shiga kara duba Comments din followers.

_Al-hamdulillah, mun dawo fatar dai Yan Team Halimatu da Abdullah da Abdulhamid da Ahmad har ma da Aminu ba su yi fushi ba 😊_
7/21/21, 10:44 PM - Buhainat: https://chat.whatsapp.com/C40KoSeXq9l35nIiFXS1Rz

*GOBE NA...*

By Khadeeja Candy

2️⃣3️⃣

Na kan dora komai a mizanin kaddara, na yarda dukan abunda ya same ni ko zai same ni rubuttacen al'amari ne daga gurin mahaliccina, wani be isa ya goge min ba kamat yadda ban iya na yayewa kaina ba.

Wannan ma yana cikin kaddararki Halimatu, haka zuciyata take yawan fada min kuma ina samun natsuwa sosai idan na tuna cewa ko wane abu da izinin Ubangijina yake samu na. Iyakar kokarin da nai na danne zuciyata ne daga kokarin aikata wani abu marar kyau wanda wani bangare nata yake hararo na ke ganin kamar mafita a gareni. Tun daga lokacin ba mu sake hada shimfida da Abdulhamid zai ba, ma'ana dai be sake leko dakina ba kamar yadda ni ma ban sake taka kafata dakinsa ba matukar yana a cikin gidan, ban fasa masa girki ba be fasa ci ba, ban kasa mika masa ko wace irin gaisuwa ba, sannu da dawowa, Allah ya tsare daman halina ne. Sai dai ban sake ganin walwalar fuskarsa ba kamar yadda walwalarsa ta hana tawa walwalar.
Idan ina zaune a falo baya zama, idan kuma yana zaune na zauna sai yai kamar ya tsargu a take zai tashi ya shige dakinsa.

Ban taba ganin laifin Abdulhamid min akan wannan ba, idan na saka kaina a matsayinsa ni kaina na san kwatankwacin abunda zan yi kenan, ba lallai ne ya gasgata ni ba, kamar yadda ba kowa zan fada haka ya yarda ba, sai dai abunda yafi min ciwo kallon da yake min na cewar na ci amanarsa.
Ina ji ina gani zaman gidan yaki yai min dadi, na kasa sakewa, kwanciyar hankali yai min kwara walwala ta yi min bankwana, kuka da damuwa suka kwankwaso min kofa.

Har ta kai bana iya bachi idan lokacin bachin yai, sai dai na raya dare da sallah ko kuma na zauna nai ta kallon sillin ko da kuwa bana tunanin komai bachin ba zai dauke ni, da rana kuma sai na tsargu ina ganin kamar ni ce kadai nake cikin matsala. Da kaina na fita chemist din dake unguwar na siyo maganin mura na ruwa a duk lokacin da na ji ina bukatar bachi sai na sha, wani abun mamaki a take bachi zai dauke ni kuma sai na manta da duk wata damuwa dake tare da ni.
Da dare kawai ba, da rana ma idan na ji damuwar ta matsa min na dan kan sha sai kuma na samu salama da natsuwa, na sani akwai illa abunda nakr sha, kuma na san ba abu ne mai kyau ba, mace kamar ni mai yaya hudu ace na buge da shan kayan maye domin na samu bachi, wannan ma yana saka ni damuwa sai dai babu yadda na iya idan ban yi hakan ba ban san abunda rashin bachin zai janyo min ba. Gaba daya yanayi na ya canja ni kaina na sani, bana sakewa kamar da ga ciwon ido ya saka ni a gaba har ta kai bana iya daga idon sosai.
Tun lokacin da abun ya faru ban sake fita da sunan zuwa unguwa ba ko wani gurin, Hajara ma ban sake labarta mata komai ba, a ganina duk wanda zan fadawa ba zai sama min mafita ba dan haka babu amfanin fallasa sirrin nawa.

Yau ma kamar jiya ta kama weekend sai dai yau Sunday ba Saturday ba, Abdulhamid tun safe ya fita kamar yadda ya sabawar kansa yanzu da fita ranar weekend ya wuni a wani gurin sai dare zai dawo, bayan da can ba haka ya saba ba. Lamarinsa na ya bani tausayi ta wani bangaren kuma sai ya bani tsoro na kan yi tunani anya ko wace mace zata iya sadaukarwar da nai? Auren mutum kamar Abdulhamid a lokacin da tawa kaddarar ta same ni sai ya juya min baya? No be kamata nai wannan tunanin ba, shi ai ba shi da lafiya rashin lafiyarsa babbar damuwarsa ce sai kuma ni na kara masa wata, ya fa kamata na gane wani abu a duk lokacin da wani ya rabe ni sai wani abu marar kyau ko kuma na bakinciki ya same shi, misali kamar Kabir ko yana ina ma yanzu?
Ni kadai nake zaune a falona ina ta sake sake da tunani kala kala wasu masu amfani wasu kuma marar amfanin. A tsorace na kalli kofar falon saboda knocked din da akai, haka nake yawan tsorata ko iska ya kada sai gabana ya yanke ya fadi. Sai da na sake jin an kwankwasa kuma na ji kamar hayani a waje sannan na tashi na nufi kofar na bude. Kanwata ce Hafiza tare da Namra da Aiman da Adnan da Amal da kuma wata yarinyar da ban waye ta sosai ba. Da gudu suka rumgume ni su dukansu wani kalar farinciki na ji wanda na dade ban ji irinsa ba, lallai ya'ya rahama ne, a take idona ya cika da kwalla ni kaina na san na yi kewar ya'yana, dukawa nai na dauki Amal muka shigo falon tare da su.
Bayan sun huta na dauko musu abincinmu, sannan na shiga dora wani domin ban san da zuwansu ba kuma nasan wanda za su cin ma ba isarsu zai yi ba, ina cikin kitchen din Hafiza ta same ni da zancen siyayyar da Aminu yake ta musu Namra a kwanakin nan, daman kuma Mama ta fada min a waya a duk lokacin da ya zo sai ta fada min domin ita ma mamaki abun yake bata kamar ni. Daga ni har sun mun rasa dalilinsa na nunawa yarana kulawa a yanzu, bayan siyayya ma duk bayan kwana biyu sai ya zo ya fita da su ko kuma ya duba lafiyarsu.

“Ni kaina Hafiza na rasa ganene dalilin Aminu na yin haka, mutumen da can ma be kula da yaran ba, har cewa yake na tara masa yara har hudu da kurciyarsa, yanzu kuma shine yake nuna musu kulawa abun yana bani tsoro”

“Ko ma minene nufinsa ba zai samu nasara ba, matukar dan ya cutar ke ko su zai yi”

“In-Sha-Allah, ba zai samu wata dama ta yin wani abu ba”

“Amman Anty miyasa kika daina zuwa gida? Baba ma kwana biyu ciwon kafafuwansa sai tashi suke?”

A take gabana ya fadi hankali kuma ya tashi abunka y'a da uba.

“Subhanallahi amman shine ba a fada min ko a waya ba?”

“Ba ke kadai ba ko su Anty Murja da suke nesa ya hana a fada musu wai za a daga musu hankali kawai, kin san ciwon nasa idan ya tashi yau ciwo gobe lafiya haka yake masa shiyasa”

“Allah ya bashi lafiya”

“Amin, Mama da Inna sai zancen ki suke su suka ce na zo da su Namra ma mu duba ki lafiya kike? Kuma gaskiya na ga alamar ba lafiya ba”

“Kamar ya?”

Na tambaya ina kokarin kirkiro murmushi.

“Haba Anty kalle ki fa, duk kin rame kin koma kamar ba ke ba, ke da kika da jikinki mulmul ma sha Allah amman yanzu ko ki na fi ki ki ba, duk kin yi baki kin lalace Gaskiya akwai abunda yake damunki”

“Babu abunda yake damuna Hafiza”

Ina fadar hakan na juyo na fito daga kitchen din domin bana son ta cika ni da tambayoyi. Ina fitowa Namra ta fara bani labarin Daddynsu yana zuwa gurinsu yanzu har ma siyayyar da yai musu, tana cikin lissafa abubuwan da ya siyo musu sai Adnan ya karbe daga nan sai Aiman har da Amal ma labarta min take abubuwan da Daddy yake musu, wani irin farinciki da annushuwa nake ganin a fuskar yayana, da alama hakan da yake musu a yanzu yana musu dadi, ko ni da nake babban na so mahaifina a kusa da ni balle su da suke kanana kuma babu ni a kusa da su. A nan Namra take nuna min new friend dinta mai irin sunanta.

“Momi kin tuna lokacin dana bata a gidansu aka kai ni, kin suna ita ce yarinyar gidan”

Sai a lokacin na tuna har na wayi fuskarka.
Chapter 42 · 0% Book details