← Book details Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 136

Sashe 24

Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A bakin gate din gidan ya tsaya da kekan Namra da ke gaban keken ta sauka, sannan Barra ta sauka suka nufi yar karamar kofar gate din sukai knocked mai gadin ya bude musu suka shiga sannan ya budewa Ahmad gate din gaba daya ya shiga da keken ciki. Katon gida ne plate mai dauke da shuke shuke gaban gidan kamar bayansa yake domin za kai tai kallon fuskar gidan amman ka gagara gane kofar shiga har sai idan an nuna kama ka, daga fentin kofar har fentin gidan har mayan motocin da ke harabar gidan duka farare ne tasss, irin farincikin nan mai burgewa da dare da rana kuma ya kawata maka ido idan kuma ya hadu da hasken rana sai ka dauka ba a Nigeria kake ba.
Bangaren da aka faka motocin ya nufa ya sauka daga kan keken ya kai hannunsa ya bude gareji ya saka keken ciki sannan ya maida garejin ya rufe, sannan ya soma tafiya cikin wani irin taku da ba na sarauta ba kuma bana kasaita ko ci da kai ba, sai dai duk wanda zai kalli yadda yake dora kafarsa a kasa zai yi tsammanin tausayin kasar yake ko kyamarta, wata kila ma a iya fassarashi da mai nuna isa da dagawa.
Zagayawa yai can baya inda ya sama kamar dabam da gidan kofarsa ma a can baya take, tun kan ya karasa ya saka hannunsa ya kwance daurin jacket din dake kugunsa, sannan ya kai hannunsa ya tura kofar ya shiga. Sanyin ac ne da hasken garin gulub tare da dadadden kamshi suka fara masa lale marhabun, katuwar plasma kuma na ta aikinta, remote ne farkon abunda ya fara dauka ya canja channel din daga Al Jazeera zuwa Tvc news. Sannan ya nufi hanyar dakinsayana shiga ya rana jikinsa da tufafin da ke jikin nasa ya daura tawul, a take farin fatar jikinsa da siffarsa ta zati ta bayyana, cikin wani irin ya na saka su a washing machine sannan ya shiga ya bawa jikinsa hakkinsa sai da ya tabbatar komai na jikinsaya wanku sannan ya fito ya shirya cikin wata farar shadda mai kyau da haske zanen jikin shaddar ma abun kallo ne balle kuma aikin da ke jikinta.
Wani tsadden turare ya dauko ya saka bayan ya saka wani a cikin jikinsa da vest din da zai saka. Murmushi yai yana kallon kansa a madubi, shi kansa ya san yayi kyau balle kuma da ya dora hular da ta dace da shaddar. Sajen fuskarsa ya kwanta gwanin sha'awa har wani shining yake.
Wallet dinsa ta fara ziyartar aljihunsa kamin makulin mota da sababin kudade su biyo baya, sannan ya dauki agogon hannunsa ya saka, for the second time ya sake duba kansa agaban katon madubin da ke dakin madubi da mutun zai iya ganin har kasansa da takalminsa. Cike da annshuwa ya fito daga dakin zuwa falonsa sai ya duba agogon hannunsa sannan ya zauna a saman manyan cushion din ya kalli labarai na yan mutuna kamar mai jiran ciron lokaci domin tsadadden agogon hannunsa na nuna 9pm ya mike tsaye ba tare da ya kashe tv ba ya fice daga falon.
Bangaren mahaifiyarsa ya nufa wacce ta zame masa dole a duk lokacin da zai fita ko da zuwa nan da kofar gida ne sai ya sanar mata, hakan ya saka cousins dinsa da yan'uwansa and friends suke kiransa da Mommy's Boy domin har time take ba shi na fita da dawowa matukar ba aiki zaije ba ko wani lalurar na dabam wanda ita ma kanta ta san mai muhimmanci ne, duk da kasancewarsa ya girma har ya haifi ya mace yar shekara tara bata daina masa haka ba, shi kansa ya saba abun ya bi masa jiki idan ya fita be sanar da ita ba sai ya ji kamar ya aikata wani babban zunubi, ita ce abokiyar shawararsa kuma abokiyarsa domin komai zai yi sai ya sanar mata ko da ko abun be taka kara ya karya ba, hakan yasa take sanin ko wane sirrin na zamantakewar aurensu, domin a cikin dabi'un daya sabunta da su a gurinta ko dankwali ya siyawa matarsa sai ya siya mata kuma sai ya fada mata tun kamin ya siya din, idan kuma ya siyo zai kawo mata ta fara gani ta zaba ko ta canja masa tukuna ya kaiwa matarsa.

Ya shiga falon da fuskarsa da annuri kamar sabon ango, daman can yana da irin fuskar nan ta samarin aljanna wadanda zaka gansu kullum fuskarsu kamar suna murmushi ko da kuwa ba murmushin sukai ba ga haske fuska da haiba, ga natsuwa da kwarji kamar wani Zaki.
Hakimce take saman kujera sanye da wata holland yar ubansu wuyanta ya ji zinari kamar yadda hannunta ke amsa amo a ko wane motsi da tai, kallo daya za kai mata ka karanci sifofin da ke fuskar mahaifiyar sune a fuskar dan, kamanni na hanci baki da kuma ido a siffa da sura da hallita irin ta da'namiji kuma Ahmad Gwarzo kamar yadda mahaifiyarsa take kiransa.

“Momy barka da dare.... ”

Ta juyo cike da isa tana kallonsa, irin kallon nan na farinciki da kaunar uwa ta ga danta.

“Barka da Gwarzo irin wannan shiri haka ina zuwa?”

“Zance zanje mana Mom”

A yayinda kalmar zancen ta dira a dodon kunnenta sai ta za me mata kamar wata mummunar kalamar marar dadin jin, annushuwa da ke fuskarta ta sai ta gushe murmushin kamar na dole. Dauke kai tai kamar ba ita ya bawa amsar ba ta maida dubanta gurin plasma.

“Bari na je kai na saba alkawari tace na zo 9”

Ya fada yana shirin juya daman can tun da ya shigo be zauna ba.

“Karka wuce 10pm”

Ta fada bayan ta kalli agogon zinarin da ke jikinta fuskarta babu alamun wasa. Juyowa yai kamar zai ce wani abu sai kuma yai murmushi ya juya ya fice. Ita kuma ta bishi da kallo tana jin kamar ta hana shi tafiya zancen, Hajiya Uwani irin iyayen nan ne da ke kishin matan yayansu musamman Gwarzo da bata hada shi da kowa ba a duniya, ba tun ba ta saba kashe masa aure ta kan saka shi ya saki matarsa idan zamanta a gidan be mata ba ko ma ta sake ta da kanta wani lokaci, wasu matan ma da kansu suke neman fita idan suka ga matsuwar ta musu yawa, ba dan kuma babu arzikin ki akwai shi har na zubarwa amman haka take bi ta takurwa matan da Ahmad Garba Gwarzo yake aurowa har sai ta fitar da su a gidan, Hajiya Uwani na da wani irin hali da ba san mutanen Kano da shi ko ma na ce mutanen Gwarzo domin daga ida har mijinta yan asalin karamar hukumar Gwarzo ne, wannan dalilin ya saka daga abokan Ahmad har ita kanta Momy da duka familynsu suke kiran dan nata da Gwarzo.
Juwuriyya ce mace ta tara da Ahmad ya aura kuma ita ce mace da ta jajirce a wajen zama da shi har tai nasarar haifa masa ya mace wato Namra, duk kuwa da irin kin son haihuwar da Hajiya Uwani take yi, ta jure duk wani cin zarafi da muguwa daga uwar mijinta saboda kawai ta zauna da Ahmad, kuma ta zauna da shi ra rayu da shi na tsawon shekara biyar kamin tai hadarin mota ta rasu. Hajiya uwa bata yarda danta ya cire kudi mai yawa da sunan yi ma mace hidima idan ma yayi ta kan rage tace ta yi yawa, haka ta ke juya duk matan da Ahmad take aure kamar waina tana kishin matan Ahmad sosai.

Latest Benz ya shiga White color daman duk motocin da suke gidan farare ne, sai dai kawai sunanyensu da kudinsu su banbanta, tun kan ya kai gate mai gadin ya bude masa gate ya fisge motar kamar domin shi kawai akai titin GRA ring road.
in time ya isa kofar gidan Alhaji Yunusa Dan-Gaske, kamin ya danna horn ya ka kai hannunsa ya dauki iPhone dinsa da ke cikin motar ya kira Zainab.

“Hello Ina kofar gidan”

Ya fada kamar wani dan sarki sannan ya danna horn aka bude masa gate din ya kunna kai a harabar gidan..

HALIMATU POV.

*Bayan sati biyu...*
Chapter 24 · 0% Book details