← Book details Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 136

Sashe 87

Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dariya nai sai ta soma tambayar dalilin rashin zuwana aiki kwana biyu. Ban boye mata komai ba na fada mata cewar wani dan'uwana ya hana ni aikin ne saboda uniform din be dace da ni ba. Dariya ta fara min tana ta mamakin wautata, wai ya zan daina aikin ban je ma fada musu dalilina ba idan ba su aminta su canja min kayan ba ko kuma gurin aikin ba sai na daina amman a haka ai ba ni da hujja kuma na bar damata ne. Ta yi tamin magiyar na je gobe na fada musu haka idan basu yarda ba sai n aje aikin, ni kuma na amsa mata da to duk da nasan ba za su yarda su canja min ba, amman yanzu na samu kudina zan iya yin sana'a ta kamin na samu wani aiki, tare muka jera muka fita tana fada min wata mata da ke yawan zuwa nemana tun da na daina zuwa aikin har number wayarta ta bari tace idan na zo a kirata. Ni kam mamaki ya cika kuma tsoro ya kama ni wacece kuma? Allah yasa ba wani karin damuwar ba ne, can kuma matar Kabir ta fado min a rai wata kila ita ce, dan nasan wannan mugun Ahmad din ba zai kyale shi ba, domin ko a yanzu na lura da kallon bakincikin da yake min, na ja masa fada da mahaukaci kuma ga shi na ci gasa na san hakan ba karamin zafi yai masa ba.
Idan na naje aikin Yunus din zan yi ma magana ko Tahir wanda shi ne shugaban sashen mu, shi kam na san ko kallo ban ishe shi ba kuma ba zai saurare ni sai dai ma ya fada min wata bakar maganar.
A ranar gidanmu ya cika da murna ba mu kadai ba har da makotan da suka samu barin sai da suka zo taya mu murna, Inna da Mama duk tsoro ya kama su wai kar a biyo dare ace sai an bada miliyan din, har ta hana a fadawa. Ba su kadai ba ni kaina na kwana da tsoro a ranar saboda halin tsoro da kasar nan take ciki abu kadan zai tsonewa wani ido.
Washe garin na tashi raina fes zuciyata kal babu damuwa ko kadan sai farinciki da annushuwa rabon da na samu kaina a haka har namanta, domin a yanzu bayan damuwata har da ta Abdallah tana damuna, tun daga wacan lokacin da yai min magana ban sake sakewa ba, su namra ma baki har kunne suna ta far'a, ban barsu sun je makaranta ba sai da nai kusu kashedi akan kar suje suna fadin abunda muka samo a school din, kuma su fadi gaskiya cewar kudin yana cikin account ba a hannu ba.
Bayan sun tafi nima na shirya cikin riga da zane na atamfa na saka hijabina, sannan na shiga dakin Mama na fada mata cewar zan tafi kamfanin na nemi alfamar canjin tufafi ko gurin aiki kamar yadda blessed ta bani shawara, daman tun da dare na labartawa Mama abunda ya faru da kuma matar da ke nema, har ta farara min kuiwa yin haka daman tana da complain cewar na daina aiki ba tare da na yi magana ba ban san ko za su aminta su canja min aikin ba.
A yau ban fita ba komai ba a hannuna da sunan kawai Kabir ba duk kuwa da kasancewar zuciyata na raya min na rika masa wani abu kamar yadda na saba, domin tun a lokacin da na daina zuwa aiki na daina kai masa abincin, haka ma take away da nake sakawa a kaiwa Abdallah na daina kasacewar hanya daya ce da gurin aikina a ko yaushe ina bada kudi na ce a kai masa idan 1pm ta yi ko 12,30pm.
Napep din da na tara akwai mutane biyu a ciki ni ce ta uku, a dole sai da ak saukesu inda za su je sannan aka kai no kamfanin wannan karon har bakin gate din kamfanin aka sauke ni, tsabanin da da ake sauke ni kusa da Kabir sai na bashi abincin sannan na wuce, babu irin dubawan da ban yi ba amman ban ga Kabir ba hakan kuma ba karamin haifar min da tsoro da zullumi yai ba, ina ta rokon Allah yasa ba mugun can yai masa wani abun ba.
As usual sai da na gaisa da masu gadin sannan na shiga ciki, kai tsaye reception na nufa fuskarta dauke da murmushi da sauri blessed ta zo ta rumgume ni.

“Oyoyo we miss you”

Ta fada sai kace wani dade muka yi muna aikin tare, ko da yake komai gamon jini ne. A nan fira ta kaure tsakanin na da su suna ta tambayar dalilin rashin zuwana aiki na fada musu sannan suka rika taya ni murna wai blessed ta basu labarin na ci gasa, a lokacin ne nake tambayarsu macen da take zuwa nema sai Rilwal ya ce

“Ai zata zo kullum sai ta zo nemanki a nan”

Na bukaci number wayar da suka ce ta bari tace a kirata idan na zo, sai Rilwal ya nuna min ita a wayarsa, na yi ta karanta number ban gane mai ita ba, sai kawai na zuba numbobin a wayata, ga mamaki sai sunan Suwaiba ya fito, miyasa take nema anan? Ba tasan gidan mu? Kuma tana number wayata idan har son ganina take? Wata matsalar ce? Ko wani abu ya faru da Abdallah? Haka zuciyata tai ra raya min abubuwa kamin na basu amsar cewar na gane mi number, nan suke fada min cewar babu wanda ya shigo a cikinsu daga sarkin girman kan har Yunus din da Tahir, hakan yasa na nemi guri na zauna dan na jirasu, ni kaina na san na yi sammako sai dai na zo da wuri ne saboda gudun na na zo suna tsaka da aiki a hana ni ganinsu tun da komai an kamfanin a tsare yake.
Ban yi minti goma da zama ba naji ana nuna domin sam ban lura da mutane da suke shigowa ba hankalina yana ka ce wayata, ina dago kaina nai yi arba da Suwaiba ta nufo inda nake rai a bace tana tafiya kamar ta fadi abun ka da siririyar mace.

“Kashedi na zo nai miki, ki fita hanyar mijina”

Ta fada cike da masifa tana daga murya iya karfinta, hakan yasa hankalin kowa ya dawo kaina.

“Ki fita hanyar mijina, yafi karfinki”

“Ba ki isa da mijin na ki ba ne shiyasa har kika zo baina jama'a kike min ihu, da ni nake auren Abdallah Wallahi idan na hana shi kallon wata macen ya hanu.... ”

“Ina zan isa da shi kin masa magani kin malleke shi bakar bazawara.... Yar duniya mai bibiyar mazan mutane, aure biyu kika kashe kina bibiyar mijina, marar mutunci kin zubar da yara hudu kin bar ubansu kina bibiyar nawa mijin, dan kawai ba ki san darajarsu ba...... Wani irin karuwanci ne da zaki rika aika masa abinci kullum..... Mijinki ne ko danki?”

Kalmar bazawara bata taba min zafi ba irin yau, ashe akwai ciwo idan aka maka gorin zawarci, a take na ji muzanci ya kamani tace na kashe aure ina bibiyar mijinta ko da karya ta fada wasu zasu gasgatata, na ci mutunci na a bainar jama'a ta gama da ni. Duk yadda na so na ki yin kuka sai na kasa hawaye suka fara min zuba bakina ya kulle gam na rasa me zan ce mata jikina sai rawa yake ina jin kamar na dake ta.

“Securities arrest her...”

Kamar saukar aradu haka muryar Ahmad ta dira a kunnena, da juyo idonw da hawaye na kalleshi yana tafe cikin kamfanin tare da Yunus, a lokacin da Security kamfanin suka nufo inda muke tsaye na yi zaton ni za su rike, sai na ga su kama Suwaiba macen cikinsu ta fisgeta da karfi.

“Ku rufe min ita a kamfanin nan sai ga uban waye mijin naki da za ki zo cikin kamfanin mu kina mana hankali how dare you”

Ya sake fada, a rikice na kalleshi ina hawaye. Sai ya karaso cikin kamfanin yana kallon amsu kallon fadan mu fuska a hade.

“Ku kuma me kuka tsaya yi kuna kallo ana insulting dinta instead of ku yi wani abu kowa ya saki ido fools”

Yana fadar hakan sai kowa yai saurin kama gabansa, shi kuma ya wuce ta gabana ba tare da ya kalleni ba ya bi hanyar da zata sada shi da office dinsa.
7/21/21, 10:47 PM - Buhainat: I think you'd like this story: "GOBE NA (My Tomorrow)" by KhadeejaCandy on Wattpad https://www.wattpad.com/story/247701926?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=story_info&wp_page=story_details_button&wp_uname=KhadeejaCandy&wp_originator=ZkyWKvWuHXhIRzZDEluZ%2BuUXayIbDBikXAQA%2BM4xeAsJY%2Fh9rtovTCoQphCdFYUPM4K1nHTquOLcFfifZUhwZ0RRyERddTi4AY1OYORg8gUhN9fNU%2FLr6t3SMGO9O8M2

*GOBE NA...*

By Khadeeja Candy

4️⃣4️⃣

Rasa nai abunda zan yi, na bishi nai masa magana ko kuma na zauna ko na tafi gida? Ya Abdallah zai ji idan aka ce wani ya tsare masa mata saboda kuma a kamfaninmu, no ba saboda ni ba ne saboda ta yi hayaniya ne dan haka babu ruwana a ciki.
   Akai akai mutane suke ta kallona, har na soma tsarguwa, tashi nai koma can wani gefe da ba a ganina sosai na zauna, wata zuciyar na fada min cewar naje nai maganar aikina sai dai kuma idan na yi maganar aikin aka koreni ba tare da an gama maganar Suwaiba fa?
  Na kusan awa daya a gurin ina ta tunanin abun ne naje nai masa maganar Suwaiba ko ta aikina, amman ina ruwana da matar da ta ci min mutunci a bainar jama'a, ai kara a kira Abdallah din domin na san ba da saninsa ta zo nan ba.
Ban raba daya biyu ba, aka aiko wata mai sanye da suit kirana, haka ta saka ni a gaba ina baya har muka isa office din Ahmad. A one of visitors chair na tarar da Abdallah zaune, ni kuma sai na tsaya daga bayansa tun da ba a bani izinin zama ba, juyowa Abdallah yai ya kalleni sai kuma ya kawardar fuskarsa ba tare da yace komai ba.

“Look man aiki bake fa zaka tsayar da ni anan for more than 20 minutes, ba kallo office dinka na zo yi ba”
Chapter 87 · 0% Book details