← Book details Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 136

Sashe 28

Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Cikin muryar da ke bayyana rashin jindadinta tai masa maganar hakan kuma ba karamin mamaki ya ba Abdallah ba, domin be taba ji ko ganin ta hana su yin wani aikin alheri ba musamman abunda ya shafi yan'uwa.

“Akan me mace zata nuna maka kiyayya kuma ka dauki nauyin hidimarta? Har da wani daukar yara ka saka su makarantar kudi ina ruwanka ba su da uba ne?”

A karon farko ta yi masa maganar a tsawace tana dire kofin tea da ke hannunta da karfi.

“Ban yi dan wani abun ba Hajiya, a gaban ki Alhaji ya bar mana wasiyar taimakon yan'uwa da mabukata, kuma tun ba yau ba idan za ayi biki a gidan Baba Karami mu na yi masa abu mai nauyi saboda mun tashi mun ga Alhaji na yin haka kuma ya mana wannan wasiyar, ba hidimar aure kawai ba har abincin da za su yi ke da kanki kin sha daukar abu daga nan ki aika musu balle kuma mu da muke jininsa”

“Ba alheri na ke hana ka yi ba, wannan karon ka yi alherin ne a gurbin da be kamata ka yi shi ba, akan me mace zata nuna maka kiyayya kuma ka nuna mata kula har da duniyarka”

“Hajiya idan Halimatu ta auri Abdulhamid kamar ni ta aura, ni da Abdulhamid duka daya ne kuma.... ”

Hannu ta daga masa.

“Na fika sanin wannan kai da shi duka ni na haife ku, ina magana ne kawai akan abunda yake bayyane ni na san Abdulhamid ba son Halimatu yake ba, ita ta janyo ra'ayinsa ba kuma saboda kowa ba sai dan kai”

“Haka ya fada miki?”

“Ba sai ya fada min ba, ni na san waye ďana, be taba zo min da maganar wata mace ko son yin aure a wannan yanayin da yake ciki ba sai a wannan lokacin, mutumen ma da neman lafiyarsa ya saka a gabansa? Rana tsaka ya zo min da zancen auren nan idan ba ita ta nuna masa ba taya za ayi ya kawo wannan tunanin a ransa? Kuma ya rasa mace aure sai Halimatu bazawara? Mai yaya hudu yana saurayinsa bayan kuma ba iya komai yake ba Allah yasa dai tsakani da Allah zata zauna da shi”

Murmushi Abdallah yai ganin yadda Hajiyarsa take ta bude wuta.

“Ban da abinki Hajiya Abdulhamid ai ba yaro ba ne da zata nuna masa hakan ya yarda idan har ya san baya son ta ko kuma zai cutu”

“Ko dai minene Husaini be dace Halimatu ta auri Hassan ba bayan ta san kana sonta ban goyi bayan Abdulhamid ya auri Bazawara ba a aurinsa na fari na kyale shi ne kawai saboda na lura da ra'ayinsa na son yin haka kuma bana son na karya masa guiwa saboda ya dade yana mafarkin aure be samu ba, kuma na tabbatar shi kansa be san kana son ta ba Wallahi ba zai aure ta ba, amman ita ai ba yarinya ba ce ya kamata tai tunani indan har ba zata aure ka ba to be kamata ta auri dan'uwanka ba, ko da kuwa shi ya nuna mata son da gaske sai da ta fasa aurenku duka, Hassan ya ji da wanne yayanta guda hudu ko kuma lalurar da take gabansa? Da gangan tai wannan saboda ta bata zumunci kuma ya batu”

Abdallah ya shafa kansa tare da hade yawu sannan ya kalli Hajiya a raunana ya fara magana muryarsa kasa kasa.

“Jikina yana yawan ba ni haka, ina yawan jin cewar kamar Halimatu ta jayo soyayyar Abdulhamid ne ba shi ya kai kansa ba, sai dai zuciyata ta kasa yardar da hakan, tun daga lokacin da kika fada min Abdulhamid ya zo miki da maganar auren, ko wane dare sai na lalubo na ga ko zan hango wani abu da zai saka na zargi Halimatu amman Wallahi Hajiya na kasa ganin laifinta, a maimakon haka sai tausayinta ya kara kamani saboda na san Abdulhamid ba kamar ni ba ne baya son yara a rayuwarsa, ko da ma yana son yara ba zai kaunace su a lokacin da yake saurayinsa ba ita kuma take a bazawara ta zo masa da yara, ga mahaifinsu be kula da su ba, and yan gidansu gaba daya mata ne mazan uku duka kanane da ba su yi wani wayo da za su iya kula da tattalin kanensu ba, balle ma yayan yayyu, abu ne mai wahala ta samu mai kula mata da yaranta yadda ya dace”

“Can ta matse mata ina ruwan wani? Ita yarinya ce da ba zata yi tunani ba kamin ta aikata abu? Ni Wallahi da tausayi take ba ni amman yanzu na natse ko ganinta bana son yi, ba dan kuma komai ba sai dan wannan wawanci da ta aikata, ni Wallahi bana son Abdulhamid ya auri bazawara kuma bazawarar ma wacce dan uwansa yake so kuma ita ta san hakan amman ta yarda”

Wannan karon wani dogon numfashi yaja ya sauke.

“Hajiya akwai wani kuskure da na aikata a can baya, wanda na ke tunanin wata kila saboda shi Halimatu take son hukunta ni kuma na cancanci haka”

“Haba Husaini wani irin laifine da zai saka ta auri dan'uwanka saboda kai? Ni ban ga cancanta aurenta da Abdulhamid ba Wallahi na san waye ďana”

“Hajiya na yi kuskuren furtawa Halimtu cewar ina sonta a lokacin da take da aure, tun da na dawo kasar nan na ganta sai ta ga ta canja min kamar ba ita ba sai Allah ya dauki son ta ya saka min a rai, a lokacin na yi ta kokarin ganin na haka zuciyata abunda take son cusa min amman na gagara, Wallahi Hajiya har ta kai idan zan kwanta ko ina wani abun sai tunaninta ya fado min a rai, musamman da na samu labarin yadda mijinta yake da kuma irin yadda take hakurin zama da shi, a lokacin shaidan ya yaudare ni kuma yayi galaba a kaina zuciyata tai ta nuna min cewar Halimatu bata dace da auren Aminu ba, ni ta dace ta aura a lokacin akwai good understanding tsakanina da ita, hakan yasa na fara nuna mata irin halayen mijinta da abubuwan da yake marar kyau, daga lokacin muka fara samun matsala da ita, a lokacin ne na fada mata kai tsaye cewar ina son ta.... ”

Shiru yai for few seconds ya shafa fuskarsa sannan ya sake sauke numfashin a karo na biyu.

“Na fada mata zan iya aurenta idan har zata iya kashe aurenta ta fito, kuma na yi ta aikata abubuwan da nake sa ran za su iya zama silar mutuwar aurenta, Astagafurullah ....Abubuwa da yawa Hajiya har ta fara fada min bakar magana tana min kallon wani shaidani yes ni kaina a ynzu ina jin na aikata ba daidai ba, amman a wacan lokacin sai na kasa gane hakan duk da na san bata dace da auren Aminu ba amman ai he dace na yi sanadin mutuwar aure ba ko?”

Hajiya ta gyada masa kai. Sai ya maida kansa kasa yana taba agogon hannunsa

“Yes i know... Kuma na san shi ya janyo min wannan matsalar a yanzu, so ko da ma ita ta janyo soyayyar Abdulhamid batai laifi ba inda dai ta hukunta ni tai i deserve it, and Abdulhamid ya fi ni bukatar aure a yanzu saboda yana a situation din ba ko wace mace zata iya aurensa a yadda yake ba sai mai hakuri da jajircewa kamar Halimatu”

“Babu wanda ya san da wannan matsalar sai mu, sai kuma ita a yanzu waya sani ko ta gagara zaman ta fita ta tona mana asiri kuma ta bayyana ma duniya halin da Hassan yake ciki bayan a da yana cikin rufin asirin Allah? Na fi tausayin Hassan fiye da kai na dade ina jiran zuwan ranar da zan ga Hassana yayi auri yana rayuwa ta farinciki kamar kai kamar kowa, amman na bana farinciki da auren nan, saboda yayi auren a lokacin da be dace ba kuma da wacce ba ta dace ba”

Mikewa tsaye Abdallah yai yana jin wani abu na rashin jindadi yana kawo masa ziyara.

“Haka Allah ya kaddara”

“Haka Allah ya kaddara kuma da son ranta ba, idan ma wannan hukunci ne take tunanin ta yi to kuskure ne babba”

“Zan je gurin aikin Hajiyarmu ba wani abun ko?”

“Babu”

Sai da ya kalli yanayinta sannan ya sa kai ya fice ransa ya susuwa zuciyarta na konuwa.

HALIMATU POV.
Chapter 28 · 0% Book details