← Book details Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 117 OF 136

Sashe 117

Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Karki sake min irin wannan game din seriously bana son kina hawa Napep”

Uffan ban ce masa ba, duk kuwa da na san ba zan iya dauka ba taya za a ace kullum ya kawo ni aiki ya maida ni, ko da yake aje aikin ma zan yi na huta. Zaunawa yai a kujerar da ke fuskantar tawa yana kallon yanayina.

“Akwai damuwa a tare da ke, fada min minene”

“Ina son na aje aikina”

Na fada kai tsaye sai yai min kallon rashin fahimta mamaki karara a fuskarsa.

“As how...?”

“I want to resign”

“No i mean why?”

Na yi shiru kamar ba zan amsa shi ba.

“Saboda na ce zan rika kai ki kullum na dauko ki? Idan ba kya ra'ayi that's normal we can talk, kin san bana son bacin ran ki i won't force you”

“Ba Saboda shi ba ne, Abdallah ya bukaci haka.....”

Mikewa yai tsaye yana murmushin da zan iya kiransa da dariya.

“That stupid guy ko?....”

“He's not stupid, Abdallah yana da muhimmanci a rayuwata...”

“How dare you.......!”

Ban karasa ba ya daka min wata mahaukaciyar tsawa ya ture desktop din dake saman teburina ta fadi kasa har wani zaro ido yake kamar mai aljanu yana maida numfashi da karfi. Tsorata nai garin na mike tsaye kujerar da ke kai ta kade ni na fadi ni da ita, kamar yana jira sai ya zagayo inda nake ya risino kusa da ni ya nuna da yatsa.

“Ba a maganar wani namijin a gabana matukar ina son mace, ina da kishi ki kiyaye wannan, bana lamuntar ki kira wani namijin da muhimanci a rayuwarki idan ba mahaifinki ko dan ki ba”

Sai da ya fada min hakan sannan ya mike tsaye ya fice daga office din a fusace, nikam daman jira nake yana fita na tashi tsaye na dauke wayata da jakata na fito daga kamfanin gaba daya na dawo gida. Da daren ranar sai ga shi ya kira ni yana ta bani hakuri akan abunda yai min, na yi zaton ko zai yi magana akan aje aikin da nace zan yi ko kuma Abdallah amman be min ko daya ba sai da zamu yi sallama sannan yace min.

“Ki yi ma Mama magana, ta fadawa wadanda ya kamata sai su saka mana rana da za su zo”

“To”

Shine abunda na ce sannan ya aje wayar, na fada mata kamar yadda ya bukata sai dai maganar yarana na kasa masa ita kuma abun ya tsaya min a rai.  Da aka fadawa kanen mahaifina sai suka nuna jindadinsu suka tambaye waye shi miye sana'ar shi a ina iyayensa suke duk na fadawa Mama ta fada musu, the following day suka saka musu rana assabar wato jibi kenan.
Kamin ranar Ahmad ya zo shi da abokansa biyu suka gaishe da Mama da Inna suka kawo musu alheri mai yawa da kudi. Tun daga ranar a kowa wane karshen dare wato misalin hudu da rabi ko hudu na kan tashi nai alwala nai sallah nafila raka biyu raka ta farko zan karanta fatiha da kulya'ayu sau goma, a raka ta biyu kuma na karanta fatiha da kulhuwallahu sau goma sha daya, bayan na sallame sai na sake sujada na yi salati sau goma, nai Subhanallahi walhamdulillahi har zuwa karshe sau goma, sai rabbana attina fidduniya hasana wafil'ahherati har zuwa karshe sau goma sannan na fadawa Allah bukatata na auren Ahmad idan akwai alheri a cikin Allah ya tabbatar ya bani ikon amincewa kuma ya saka min natsuwa, idan kuma babu alherin Allah ya kawo min mafi alherin shi ma ya zaba masa wata. Haka na jera rana ku nan kullum sai na yi sallah nan na roki Allah.

A iya tunani idan sun je za su gaishe da iyayene kawai wato kanen mahaifina da yayyensa, da kuma neman izinin zuwa fira kamar yadda ya fada min ashe ba haka ba ne. Da goma suka ce masu za su hadu misalin sha daya saura sai ga kiran kanen mahaifina ya shigo wayar Mama, be ce mata komai ba kawai yace ta ba ni wayar.
Na karba na kara a kunne ina masa sallama sai ya amsa min yai na mika masa gaisuwa ita kan be karba min ba yace.

“Ba ki fada mana idan sun zo za ayi daurin aure ba? Haka nan ake abu ba a fadawa sauran yan'uwa ba ba ayi komai ba? Gasu nan sun zo da mota kusan biyar da mutane da goron daurin aure da alawa da dabino”

Kasa magana nai, sai na ji abun wani iri wai daurin aure haka nan kawai daga zuwa tambaya sai kace na fado daga sama, to me ni ma zan ce? Nace a a karya yake ban ce a daura auren ba? Ko kuma na ce ban amince da hakan ba? Ban gama tunanin abunda zan fada ba na ji muryarsa yana fadin.

“Ke nake saurare Halimatu”

“Baba duk yadda kuka yi daidai ne”

“A a ke muke saurare, ke kika turo shi ai idan kin amince sai a daura ni ba mu da matsala idan kuma ba ki amince ba sai ya nemi sasanci a gurinki”

Gaba daya sai na zama kamar wata kurma, na kasa cewa na amince ko kuma a a ban amince ba, zuciyata tai wani irin nauyi kamar wacce bata tana aure ba.

“Na amince Baba”

Na fada hawaye na sauko min ina numfashi daker.

“To Ma-sha-Allah, Allah yasa alheri sadakin fa nawa za a yanka masa?”

“Baba duk yadda kikai daidai ne”

“To Allah yai miki albarka”

“Amin....”

Na amsa ina fashewa da kuka, ji nake kamar ban taba auren ba gaba daya abun ya zame min bakon al'amari, da gaske kuka nake sosai kamar wata karamar yarinyar da akai wa auren dole, Mama tai yi ta tambayar dalilin kukan nawa na kasa fada mata saboda kukan da nake ji nake zuciyata kamar zata fasa kirjina ta fito waje, idan aka tambaye ni dalilin kukana ba zan iya fada ba domin nima ban san abunda ya saka ni kukan ba.
Abu kamar wasa bayan minti talatin Kanen mahaifina ya kira ya fadawa Mama cewar an daura aure ne, ijiyar auren Ahmad uku ta hau kaina, a lokacin ne kuka yace dazun ban ci komai ba yanzu zan yi shi, kowa ya cika da tsananin mamaki a gidan sai dai dukansu suna murna sanin cewar alheri ne wannan karon yai musu bazata ba sheri ba, duk wanda ya tambayi mi nake yi ma kuka sai na ce ban sani ba domin har ga Allah ni kaina bansan dalilin hawayen ba.
Bayan kamar awa daya kanen mahaifina suka kawo goro da alawa da dabinon dauren aure sannan ya ciro dakina a aljihunsa ya rika hannuna ya danka min.

“Ga sadakin nan Halimatu, mun ce su bada 30k sai suka ce one million za su biya, babu yadda ba mu yi ba akan su rage amman suka ki, ina addu'a wannan aure yasa ya sanya nasa albarka ya saka alheri yasa gidan zamanki ne”

Da gaske miliyan daya nake gani a matsayin sadakina, ni Halimatu abunda ban tana gani ba ban kuma tana ji ba an biya sadakin bazawara har haka kuma bazawarar ma mai aure biyu da yaya hudu. Dana karba sai na bawa Mama na ce ta aje min, ita kuma ta kulla goron da alawa da dabino ta bada aka kai makota wai a fada musu an daura auren Halimatu yau.
  A lokacin da su Namra suka dawo daga islamiya sai ta dame ni da tambaya.

“Momy aure kika yi?”

Na gyada mata kai.

“Momy da wa? Da wa? Da wa?”

Sai na kasa masa nata ita kuma ta kasa daina tambaya har sai da Aisha ta daka mata tsawa.

“Haba Namra wannan tambaya haka?”

“Momy Daddy kika aura?”

Na girgiza mata kai alamar a'a sai ta fashe da kuka sosai.

“Momy tafiya za ki sake yi?”

A gurin ta fadi da uniform dinta na islamiya tana ta kuka. Babu wanda ya rarrashe ta sai Hafiza ita ta fada mata wanda na aura kuma ta fada mata wannan karon ba zan tafi na bar su ba ne tare za mu tafi.

  Har akai sallah la'asar ban daina ganin kamar mafarki nake ba, kuma ban daina hawayen ba, ina zaune saman carpet din dana kare sallah ina yi ma Allah godiya kuma ina kara rokon ya tabbatar da alheri a tsakaninmu, sai ga kiran Abdallah ya shigo, rawa jikina ya fara yi na fara kallon wayar kamar na ga wani dodo, na kasa daukar kiran har ya katse, lokaci daya na fashe da kuka marar sauti, na san duk inda yake a yanzu ya samu labarin daurin aurena wanda hakan ba zai masa dadi ba.
  Bayan sallah magariba aka daf da sallah isha'i wani gurin ma har an fara yaron ya doko sallama ya shigo gidanmu da manyan ledodi.

“Wai gashi in ji Ahmad kuma yace yana sallama da Halima a waje”

Wani irin faduwa gabana yai sai naji kamar ban taba arba da shi ba, kamar wani bako na ji shi, har nai kamar ba zan je ba sai dai yadda Mama ta matsa min yasa dole na zari Hijab dina na saka na nufi kofar fita jikina ba kwari gabana sai faduwa yake. Can nesa da gidanmu na hango motarsa a fake sai da na sauke ajiyar zuciya sannan na doshi gurin, kamin na karasa na ji an rumgume ni ta baya ya dora kansa saman wuyana.

“Al-hamdulillah...... Lims you're finally mine....”

“Mutane za su iya ganinmu”

Na fada ina hango daidaikun mutanen da ke can nesa da mu suna sha'aninsu wasu kuma na alwala. Sai ya sake ni ya juyo da ni yai kissing goshina kana ya hade goshinsa da nawa yana goga min hancinsa a hankali sai kallon cikin idona yake.

“Why are you crying?”

Ban ma san da hawayen sun zubo min ba sai da yai maganar, shiru nai ban amsa shi ba.

“Lims do you love me....?”

“Ban sani ba...”

Na fada da iyakar gaskiyata, wasu hawayen na sauko min, halshensa na ji a saman kunci na yana lasar hawayena.

“Wannan hawayen mai sanyi ne, ni na san kina so na Lims....”
Chapter 117 · 0% Book details