← Book details Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 136

Sashe 6

Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na fada tare da kiran Aminu da babanta kamar yadda take kiransa kasancewar sunan mahaifinta ne.

“Babu namijin da yake da dama Halima, ni kin ga mijina Wallahi zan iya tafiya wani garin na kwana iya kwanakin da naji sun min na dawo be isa ya ce min komai ba”

“Too ku manya ne Sa'adatu”

Na fada cike da sha'awa da kuma jinjina abunda ta fada, ko bata fada min da bakinta ba na san zata iya domin ta saba zuwa wani gari da sunan biki ko ganin yan'uwa ta bar masa yaransa sai ranar data ga dama ta dawo kuma ba zai yi komai ba. Abun har burgeni yake ni da wani lokacin ko makota sai Abban Namra ya hana ni zuwa.

“Wai ya kika ba ni ruwa zalla a tsirara ba masu kala ne?”

“Baban na ki ne be siyo masu kala ba”

“Aa Babana fa komai kawowa yake karki cutar da shi, daman kin saba bakin sherinki ni bari ma na tashi daman bankwana na zo nai miki zanje Kaduna gobe In-Sha-Allah”

“Kaduna kuma? Gurin me?”

“Wallahi wani abun bikin ne ya taso mana zanje na kwana hudu ko sati ma a can”

“Da yaran zaki je kenan”

“Aa ni kadai zanje na shakatawata abuna yara su zauna gurin Babansu”

“To indai baki yi hankali ba sai ya dauko miki wata”

“Ai be isa ba Wallahi wa? Ni? Hmmmm ai na bashi wannan ya shanye”

Ta fada tana wani turo dankwali tare da nuna min kasan kafarta.

“Haka fa, na ji ance ana yi ko?”

“Au tsayawa ji kikai? Ba ki ma aikata ba”

“Ina ganin kamar akwai rashin dacewa a haka”

“To yar sarkin Malamai”

Dariya nai zan sake magana sai jin tsayawar motar Abban Namra mu ka ji, a take gabana ya fadi domin na san zai tambaye shi yaransa gashi tun da na aikasu basu dawo ba, kamin ya shigo falon hankalina ya tashi sosai saboda aiken da nai musu ga kuma fita kai Namra asibiti da nai ba tare da izininsa ba na san zai iya yi min fada a gaban kowa, ni kuwa abunda na tsana kenan ayi min fada a gaban wani musamman kawayena.
Fuska a hade ya shigo falon ni kuma nai saurin mikewa tsaye na nufi inda yake ina masa sannu da zuwa tare da kai hannu na karbi jakarsa.
Da kamar ba zai amsa min sannun da nai masa ba, sai dai yana gada ido da Sa'adatu sai ya sake fuskarsa.

“Yauwa, a a diyata ce da kanta a gidan?”

“Nice Babana ya garin ya gararin garin?”

Ta amsa tana wani karkada ido, na yi zaton ko zata ja mayafinta ta rufe kirjinta ne kuma ta gyara ture kaga tsiyar da tai na dankwalinta amman ba ko daya, zama yai a kujerar da ke facing din tata yana murmushi.

“Fatar kin zo lafiya?”

“Lafiya kalau matarka ta bani ruwa masu sanyi amman ba masu kala na yi magana tace Babana be siyo ba”

Sai juyo yai ya kalleni ina kokarin zama kusa da shi.

“Ah ah drinks ya kare ne daman? Ai baki fada min ba”

Kasa ce masa komai nai bayan kallon mamaki da nake masa rabon da ya siyo mana wani abu mai sunan lemu mu sha a gidan har na manta, amman yau saboda ya nuna yana siya har yake tambayar yaushe ya kare? Haka yake min idan ya ga mutane ni kuma bana iya karyata shi.

“Jiya ya kare”

Na fada ina hade yawun bakina.

“Okay bari sai gobe a siyo ai ban sani ba, ina fatar kin ci abinci?”

Ya karasa yana naida dubansa gurin Sa'adatu.

“Aa ban ci ba”

Sai ya juyo kaina.

“Miyasa ba a bata abinci ba? Ko ba a gama ba? A kawo mata abincin mana”

“Aa ni tafiya ma zanyi”

Ta fada tana janyo mayafinta ta rufe jikinta tare da gyara dankwalinta. Sai shi ma ya mike tsaye da sauri yana ta kallonta.

“Bari na rage miki hanya, ina takardar maganin take?”

“Tana daki”

“Je ki dauko sai na siyo daga can”

Har na bude baki nai magana ganin da gaske yake zai wuce da ita sai kuma wata zuciyar tace nai kawaici na kyale shi. Dakina na shiga na dauko takardar maganin na kawo masa sai ya karba yana duba sannan ya kalleta ya ce.

“Muje”

“Matar Baba sai wani gamon kuma”

“To Allah ya kiyaye hanya”

Na fada ina binsu da kallon zuciyata na mugun tsoyuwa. Sai da suka fice daga falon na koma gurin windows din ina hangensu har suk shiga motar yaja sukai gaba, ajiyar zuciya na saki tare da sakin labulen falon sannan na dawo saman kujera ya zauna, na san Sa'adatu zata dauki hankalin Aminu saboda bata da jiki kamar ni kuma ita fara ce sosai kamar dai yadda yake yawan fada min yana son mace fara marar jiki ba irina ba. Tunanin yadda zan yi na rage kibar ne ya fara zuwa min a rai shi farin na san mai sauki ne zan iya siyen mayukan fari na shafa nai fari amman rage kibar ne zai ba ni wahala domin na gwada abubuwa da dama na rage kibar har yau ban dace ba, sai a yanzu na tuno da wani maganin rage kibar da na siye, tashi nai na nufi upstairs, ina shiga dakin na nufi gurin dana rataye jaka na dauka bude n dauko maganin na sauko kasa na shiga kitchen na zuba ruwan zafin da suke a filas na zuba maganin na kasa sugar kadan na fita shi, sannan na zauna ina sha a hankali, zuciyata cike da fatar ya karbe ni ni dai duk abunda zai shiryani da mijina mu yi zaman auren na jindadi da kaunar juna ina son shi, ina ji a raina inda har idan na kawarda kibar nan da ke jikina nai fari fes Aminu zai so ni to na shirya yi ko da kuwa zan kashe kudi da yawa.
Ina cikin sha na jiyo Namra tana amai da sauri na aje kofin na fito da sauri na rikata, amai take babu kakkautawa, a take hankalina ya tashi daman abu kadan ya saka ni faduwar gaba ko kuka. A cikin falon tai aman har ta gama sannan na rika ta na kaita bandakinsu na wanke mata jikinta na saka mata wasu tufafin.

“Momy sanyi na ke ji kum cikina ciwo yake”

Ta fada cikin kuka jikinta na ta kyarma. Rigar sanyi na dauko na saka mata na kwantar da ita saman gadonsu na lullube ta sannan na fito na gyara falon. Sai da na gama gyaran sannan Adnan da Aiman suka dawo daga aiken da nai musu tare da Kausar din.

“Ina kuke je kuka tsaya tun dazun?”

Na fada cikin tsawa a take tsoro ya rufe Adnan.

“Momy ko da muka je bata cikin gidan sai muka jira har ta dawo muka fada mata, ki yi hakuri dan Allah”

Abunda sukai min be kai ya saka raina baci ba balle har na dake su, amman sai zuciyata ta rufe a take a gurin na mari Adnan kamar wani babba na ciro wayar caja na saka na zanesu tas suna da kuka da ihu Aiman na ni yake ta kira amman nai kunne uwar shegu da ihun na su kuma na tirsasu su yi shiru.

“Kausar ki bar shi kawai daman magani za ki yo ma Namra kuma Babansu ya karbi takardar maganin”

Da to ta amsa min ta fice da sauri ganin kamar raina a bace yake. Ni kuma na koma kitchen din na hada wa Namra tea wai ko zata iya sha amman ta kasa sha, sai kuka take hakan yasa hankalina ya tashi na sake gwada kiran Abbansu wayar tai ringing har ta gama be dauka ba. Be kuma shigo gidan ba sai sha biyu da mintuna kamar yadda ya saba, ni kuma har lokacin ban yi bachi ba ina rumgume da Namra ga Amal a bayana wacce ta cilasta ni goyonta saboda bakar rigima irin nata.

“Sannu da zuwa”

“yauwa”

Ya amsa min fuskarsa ba yabo ba fallasa sannan na wulgo min ledar maganin ya nufi hanyar dakinsa, kwantar da Namra nai daga saman jikina zuwa jikin kujera na tashi na nufi inda ledar maganin take na dauka zuciyata nata soyuwa, na rasa gane wane irin zama na ke da Aminu, kamar waenda akai auren dole ko kuma basa kaunar junansu haka yake mu'amala da ni, ko za a yanka ni ba zan iya fadar abunda nai masa ba wanda ya saka yake min wannan wulakancin. Ta jikin kwalin maganin na duba yadda ake badawa na zuba na bata ta sha sannan na dauketa daga falon na sake maida ita dakinsu tare da yan'uwanta na kwantar da ita, kana na nufi gadon Amal na kwantar da ita ita ma nai mata addu'a na tofa mata sannan na janyo kofar dakin na fito. Dakina na koma na sauya tufafin jikina daga atamfa zuwa wani yadi mai kyau da kyalli na fesa turare na gyara fuska na shafa janbaki da dan man baki kadan dan yai kyali sannan na fito na nufi dakinsa. Da sallama na shiga ya amsa min yana cin abinci ba tare da ya kalleni ba. Sai na zauna gabansa ina ta kallon yanayinsa shi kuma hankalinsa na kan wayarsa.

“Ya akai?”

“Ba ni da hali na zauna da kai da sunan hira ko kallonka sai ka tambaye ni minene? Ban san abunda nai maka ba Abban Namra amman gaba daya ka canja min kamar ba kai ba, ni dai na san ba auren kiyayya mu kai ba amman irin zaman da muke da kai kamar na kiyayya”

“Da bakamar yanzu ba ce Halima, auren soyayya mukai kuma ai zaman soyayya muke ko? Ko na kiyayya ne? Ke kanki kin san da bana son ki ba zan zauna da ke ba, kuma rayuwa tana sauyasa ke kanki ai ba kamar yadda kike ada kike a yanzu ba kin canja”

Hawaye ne ya fara min zuba.
Chapter 6 · 0% Book details