Sashe 25
Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sati daya nai ina raya ko wane dare da sallah da salatin Annabi, na mikawa Allah zabina a tsakanin zama a gida nan ba tare da aure ba da kuma yin auren, domin ni ba dan Abdulhamid ba da ban kawo maganar aure a kusa ba, a da na yi planning akan na cigaba da aikina na rike yayana har zuwa wani lokacin domin ban shirya fuskantar wani kalulen zaman aure ba a yanzu saboda wahalar da na sha a gidan Aminu, sai dai yadda Mama da Inna suka tsaya kai ta fata wajen ganin na cire wannan burin a raina yasa na sassautawa kaina, ga kuma rokon Allah da nai sai ya saka min son auren a raina fiye da lokacin da nakr budurwa ma. Na roki Allah ya zaba min a tsakanin yin auren a yanzu da kuma hakura da auren har na wani lokaci, amman ban roki Allah ya zaba min a tsakanin yan uwa guda biyu ba wato Abdallah da Abdulhamid, a iya ganina da fahimta Abdulhamid ya fi Abdallah cancantar aure a yanzu domin shi be taba auren ba gaba daya a rayuwarsa, kuma ni ya so tun a lokacin da nake budurwa yanzu kuma da auren ya mutu ya dawo min. Ko ba komai ya hade kwadayinsa na furta min kalmar so ko cancantar zama da Aminu be taba fadin wata mummanar kalma akan Aminu ba, duk kuwa da irin sanin da yai na irin zamantakewar auren da muke da halayensa, be taba daga waya ya kira ya fada min wani abun marar dadin ji ba, idan har ya kirani sai idan wani babbab dalilin ne ko kuma idan mun gadu da shi a gida. Tsabanin Abdallah da yake yawan fada min abubuwan da Aminu yake aikatawa a waje bayan yabon surata da yake da nuna yana sona tun daga lokacin da ya dawo daga kasarsa ya saka ni a idonsa. Wani lokacin har mamakin yadda Abdallah yake min wasu abubuwan na ke domin an tabbatar da ace shi ne a matsayin Abdulhamid da ya so ni tun ina budurwa da Allah kadai ya san irin chabar da za ayi.
Na fi jin natsuwa da Abdulhamid fiye da Abdallah, wata kila saboda zuciyata ta taba son sa ne, ko kuwa dan ina tausayinsa ne oho, ga shi ya dage sai kai kawo yake, domin idan be zo yau ba, to zai zo gobe tun ina fargabar kar wata rana Abdallah ya tarar da shi har na daina, ko da yake Abdallah ma tun daga wacan ranar da ya min koho wayata ta fashe be sake dawowa gidan ba, kuma be sake gwada kiran sabuwar wayar da Abdulhamid ya siya min ba, hakan kuma ba karamin dadi yai min ba, domin ya bani damar sakewa da kula Abdulhamid a duk lokacin da yai min sallama.
Ta wani bangaren kuma ina yabon Abdallah sama da Abdulhamid, domin shi mutum ne mai son yara ko na ce mutum ne mai son yayana tsabanin Abdulhamid da ko fuska baya sake musu daman can kowa ya sani Abdulhamid ba a mutum ne mai son yara ba, sai dai ban dauka har da nawa ba ganin kamar ni din ta dabam ce a gurinsa. Yes yana nuna min so da kulawa irin wadanda na rasa a gidan Aminu, shi tun a yanzu ya fara nuna min su sai dai a duk lokacin da muke waya be taba cewa ya yarana ko ya gaishesu balle kuma har ya riko musu wani abun taba. Ba kamar Abdallah ba da har saman jikinsa suke hawa su karbi wayarsa su yi game, rashin sakewa da yarana yana daya daga cikin abunda yake daga min hankalin bayan maganar daina aikina da yai min idan har na amince zan aurenshi. Ya nuna min cewar shi yana da kishin da ba zai iya barina nai aiki ba, kuma yana da halin da zai iya dauke min komai, daga lokacin da yai maganar daina aikina zuwa yau na kasa yanke hukunci kuma na kasa zaba na kasa shawara da kowa, ba dan komai ba sai dan na san duk wanda zai shawarce ni zai ce na daina aikin na yi zaman aure. Na san dole ne Abdulhamid ya ji tsoron naje nai aiki saboda kar na hadu da wani namijin ya burge shi bayan shi baya iya komai, wai da gasken ne baya iya komai din ko kuwa dai gwadani yake ya ga idan zan iya zama da shi? Ko kuma karfin soyayyar da nake masa? Ni dai na san ba dan soyayya kawai zan aure shi ba har da tausayin halin da ya samu kansa wanda na so yin wannan jihadin tun a baya.
Yana yawa fada min sai na ji na ki ji, saboda za ayi ta kananna maganganun akan mu, ganin ni bazarawa ce har da yaya hudu shi kuma saurayi, ko da yake ba irin yaran samarin nan ba ne irin tazuran nan ne da suka dade ba su yi aure ba, amman duk da hakan na san sai yi magana, ban kawo zancen rashin lafiyarsa ba saboda na san ba kowa da ya san da matsalar ba.
*** *** ***
Yau dai na yanke shawara ba zan je aiki ba sai na sake gwada nemawa yarana wata makarantar ko Allah zai saka a dace idan kohin Abdallah ya janye daga jikinsu ko kuma jikina zance tun da ni ce mahaifiyarsu kuma ni ce sila.
A Napep na saka su muka kama hanyar Gwarzo International School, babbar makaranta ce da babu irinta a garin Gusau makaranta ce da ta amsa sunan makaranta kamar yadda na ke jin ana fada babu kamar dalibansu, sai dai makaranta ce mai tsada sosai ba kowa ke iya saka yaransa a makaranta ba saboda kudin da ake kashewa.
Ni kaina na san ba lallai na iya jurar biya musu kudin ba, zan dai gwada ne kawai idan an karbe su sun fara karatun sai na canja musu ni dai burina kohin da Abdallah yai mana ya karye kawai. A lokacin da mai napep din ya faka bakin gate din makarantar na ji wani iri ganin irin manyan motocin da ke kawo yaran makarantar. Sai dai ban yi kasa a guiwa na biya mai Napep din kudinsa na kama hannun yarana muka nufi cikin makarantar, wani abun da zai kara burgeka da makarantar yadda aka tsaurara tsaro domin sai da aka gama bincikamu sannan aka bar mu muka wuce a nan na soma ganin malaman makarantar har da turawa.
Da tambaya na isa office din principal din dake can hawa na biyu, office ne da aka kawata shi da kayan alatu kamar ba a cikin scul ba, guri na samu na zauna daman tun kan na shigo office din sun fada min cewar yana gurin Assembly.
Su Namra suka zauna a a doguwar kujerar da ke kusa da kofa ni kuma na zauna a kujerar da ke kallon teburin principal din. Bayan kamar minti goma zuwa shabiyar aka turo kofar office din aka shigo. Mutumen nan ne da ya kade ni da kekensa yana rike da hannun yarinyar da wacce ta sha kitso mai kyau kuma take tsananin kama da shi, shadda ce a jikinsa ita kuma tana sanye da uniform din makaranta dan guntun skirt ne blue da farar riga sai takalmin makaranta da Scul bag a bayanta mahaifinta, sai wani babbata fuska take da alama wani abun akai mata shi kuma yana ta sham kamshi sai kace wani hege😏
Ni dai kallo daya nai musu daga shi yar sagartacciyar yar tasa na dauke kai shi ko kallon inda muke ma be yi ba.
“Ke tashi ta zauna...”
Fuskata na gabas na jiyo munafukar muryarsa yana yi ma Namra magana wai ta sauka ta bawa yarsa guri ta zauna, juyo nai ina masa kallo uku saura kwata na dakartar da Namra da ke kokarin tashi ta bar yar tasa guri...
“Ke karki tashi, ai da be fi da ba yadda ka kawo yarka a makaranta haka na kawo tawa, dan haka ba zata sauka daga kujera ba tun da kujerar makaranta ce ba da gidan kowa ba”
Yadda kasan ina fada da mutum mutume haka yai min, yana ta lasa wayarsa kamar ba da shi na ke magana ba, ni ma haushi na ji na bawa banza ajiyarsa ina gyara gyalen abayata dake kaina. Muna haka principal din ya shigo, wani abun da zai baka haushi yana ganin mutumen ya fara rawar jiki da shi har da janyo masa kujerarsa ya zauna.
“Ai na san abunda ya kawo ka ranka ya dade daman na san sai Karamar Hajiya ta tsokano mana kai”
Principal din ya fada yana ta washe hauro, da alama dai wannan mutumen yana dan ba shi lashi ne shiyasa ya ke ta masa far'a yana yin kamar be gam mu ba.
“Karamar Hajiya tace kun dake ta”
“Wallahi ranka ya dade bulala biyu ne kawai akai mata ita da yarinyar da sukai fadan”
“Amman kasab ka'idar makarantar nan ba a duka? Then why za ku dake su daga ita har wacan yarinyar?”
“A yi hakuri ranka ya dade dan horo ne kawai ba wai wani abun ba”
“To wannan dai ya zama na karshe”
“In-Sha-Allah ranka ya dade In-Sha-Allah”
“Hajiyata wuce class kinji”
Yarinyar ta dan bata fuska.
“Daddy baka ba ni komai ba”
“Kin san ai bana baki kudi”
“Daddy pls”
Sai kawai ta saka kuka, tsawa ya daka da alama kuma tana tsoron fushinsa ba shiri ta ranta a cikin na kare ta fice daga office din. Sai ta fice sannan principal din ya kalleni.
“Hajiya lafiya dai?”
“Yarana na kawo ina son na saka su a makarantar nan”
“Su duka? Ina mahaifinsu yake?”
Na dan yi shiru na dakiku kamin na amsa masa.
“Baya kusa shi ya ce na kawo su”
“A ka'idar makarantar nan maza suke kawo yara ba mata ba, sannan ba ma karbar yara a irin wannan lokacin saboda an yi nisa da karatu ko wane aji akwai adadin dalibin da ake bukata”
“Dan Allah ku taimaka min zan biya kudin makarantar ko nawa ne In-Sha-Allah”
“Zancen biyan kudin makaranta ai wajibi ne, taimakon ne dai ba zai yi yu ba yanzu”