← Book details Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 136

Sashe 58

Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“It seems like kamar akwai abunda yake damunki”

“Yes alakarka da Halimatun nan ne ya ishe ni”

Juyowa yai gaba daya ya fuskance ta.

“I thought we talk about this issue kuma kin fahimce ni”

“No i didn't,and i won't”

Kai tsaye ta amsa masa da kamar fada, mikewa yai tsaye ya dauki wayarsa ya cire password din ya shiga call list ya duba mai kiran, bakuwar number ya gani a take ya aikawa Number kira, sai da tai ringing har ta katse ba a dauka sannan ya sake kiran layin aka daga cikin muryar kuka Salma take magana.

“Hello.. Ya Abdallah”

“Miya faru?”

Ya tambaya ba dan ya san mai maganar ba, sai dai ita Salma tana da number sa.

“Anty Halima ce sume”

Gabansa ya fadi.

“Ta suma kamar ya?”

“Dazun ba Anty Halima ta kira ka ba? daman muna asibiti wannan Namra ce ta fada rijiya shine babanta yanzu ya mari Anty Halima ta suma”

“Kuna ina?”

“Muna asibitin Fmc”

Be saka cewa komai ba ya katse kiran, zuciyarsa bata bashi kowa ba sai Namra ta ya akai ta fada rijiya ita tambayar da ta fado masa a rai, and why Aminu zai saka hannu ya daki Halimatu bayan ita take dawainiya da yarta, saboda kawai ya mayarda ita wata banza shine yake ta yi mata yadda ya ga dama.

“Miyasa bata kira wani ba a family sai kai? Bata fi kusa da Abdulhamid ba shi da ya aureta ya saketa cikin mutunci? Ji yadda kake zanzana kamar.... ”

Kan ta karasa ya daga mata hannu.

“Please....”

Sai kuma ya juyo daga jikin wardrobe da yake tsaye ya kalleta yana gyara hannun rigarsa.

“Alaka ta da Halimatu ba ta yankewa matukar ina da rai, saboda haka ki sakawa zuciyarki salama, idan za ki iya yarda da mijikin fine, idan kuma aka samu akasin haka za ki wahalar da rayuwarki ne kawai, na fada miki kuma a yanzu zan sake maimaita miki hakan, for now on ba saboda na auri Halimatu nake wannan abun ba i just want to make her happy....”

Yana kawai nan ya nufi gurin da kananan abubuwansa suke ya dauka ya saka aljihu ya fice daga dakin cikin sauri. Kamin ya isa asibitin zuciyarsa ta cika, ransa ya bace sosai from now on zai rika defending Halimatu as her brother, taya wani can wai shi tsohon mijinta zai saka hannu ya daketa saboda kawai yarta ta fada rijiya.

“Ji wani irin zalimci”

Ya furta yana jin wani irin bacin rai an taba masa Halimatu, a take wani bangare na zuciyarsa ya aika masa tambayar da ya rasa amsar ta.

“Miyasa na damu har haka? What if mutane suka zargi wani abu? Miyasa nake ta zurfafa lamarinta a raina har yanzu....?”

Yayi farkin motarsa gurin da kowa yake fakin sannan ya fito ya nufi cikin asibitin yana kokarin sake kiran Salma dan sanin inda suke a cikin asibitin.

HALIMATU POV.

Ashe suma na tana da dadi kamar dai shan maganin bachi, ta kan mantar da kai duniyar da kake ciki da kuma duniyar kuncinka balle kuma wata damuwa da fargaba ko kuka da tsoro. Indai har haka itama mutuwar take to ni kam ina maraba da ita daga yanzu har zuwa lokacin da zata sallamomin.
Sannu sannu Halimatu.

Muryoyi biyu na ji wadanda ba zan iya tantancewa ba kamar na Inna da Mama kuma kamar ba na su ba, iyakar unkurin da nai na bude idanuwa ne sai na ji sun min nauyi sosai, a cikin kaina kuma kamar babu komai ina jinsa kamar fanko. Ban ankaro ba na ji numfashina yai nauyi gurin fita daga kirjina haka ma gurin shiga sai na yi da karfi yake wucewa. Da wani irin karfi na umkuro na tashi zaune tare da bude idanuwa har sai da Inna da rike ni. Tabbas Inna ce ga fuskarta nan ina gani kamar a mafarki bakina na motsi amman ban san mi nake cewa ba, kai na daga sama gaba daya komai kamar ba gaske ba nake ganinsa. Kamar a min shokin sai na ji na farko daga mafarkin da nake. A zahirin ma ga Inna nan rike da ni Sai Salma da Aisha da Fati tsaye a kaina, Salma ta rufe bakina tana kuka tana kallona kamar yadda Inna ma take kuka ita da Fati.

“Anty Halima...”

Aisha ta kira sunana tana kallona kamar a firgice.

“Na'am”

Na amsa mata ina kokarin tuna abunda yasa aka kawo ni a nan. Na tuna Namra ta fada rijiya muka kawota ko? Sai aka mare ni? Amman waya mareni? Miyasa aka mareni?

“Ina Namra take?”

“Babanta ya dauke ta”

Salma ta amsa tana share hawayenta. Daga lokacin ban sake sanin inda nake ba, sai na ji kamar wata tsotsa tana min yawo akai. A lokacin da hankalina ya dawo sai na ga Abdallah da wasu likitocin uku tsaye a kaina suna kallona. Wannan karon Salma hannu ta dora saman kai tana hawaye, Aisha ma kuka take.

“Wai miya faru? Namra ta mutu ne?”

“Bata mutu ba... ”

Abdallah ne ya amsa min yana saka hannunsa a aljihu.

“Ina son na ganta”

Ina kokarin sauka daga kan gadon ya ce.

“Akwai drip hannunki ki zauna sai ya kare”

“A a ba zan iya ba ina son na ganta”

“Ba mu san inda ya kaita ba”

Ya amsa min fuskarsa ba yabo ba fallasa. Hakan yasa na koma na kwanta sai kuma na ji yana maganar hoto.

“Idan drip din ya kare Mama za ta kaita ayi mata hoto”

“Ba ni da lafiya ne?”

Na tambaya sai yai saurin ba ni amsa.

“Lafiyarki kalau”

Bayan ya amsa min ya cigaba da kallona kamar mai tunani.

“Ina son ganin yarinyar nan ina son ganinta ta mutu bata mutu ba ban sani ba i need to see her!”

Na fada a tsawace kamar ba a hayyacina ba.

“Idan ka san inda take a kaita ta ganta”

“Ban sani ba amman zan bincika”

Yana fadar hakan ya juya ya fice daga dakin sai sauran likotocin suka bi bayansa. Ni kuma na lumshe idona ban bude ba har sai da na ji motsin shigowar mutum, Hafiza ce ta shigo hankalinta a tashe tana sharar kwalla.

“Sannu Halimatu”

Haka take kirana yana da wahala ta ce min Anty indai ba mutane sai arzikin ke saman kanta ba.

“Yauwa, yarinyar ta rayu”

“Ance tana da rai, mahaifinta ya kaita wata asibitin aka ce”

Ban sake ce mata komai ba, har sai da Abdallah ya shigo da kansa ya karaso ya cire min drip sannan ya ciro wayarsa ya kira wani likita da ban san wanene ba ya ce.

“Zan dauketa na kaita ta ga yarinyar yanzu idan mun dawo i will call you”

Daga haka ya maida wayar aljihu ni kuma na sauko daga saman gadon na biyo bayansa, a harabar kofar shiga Ward din inda mutane suke shinfida tabarma suna zaunawa na hango Inna sai ta taso ta tare ni.

“Halimatu kin taso”

“eh zan kaita ta dubo Namra ne idan mun dawo sai a je da ita gurin hoton”

Abdallah ne ya bata amsa a madadina sannan tai mana Allah ya tsare ta bimu da kallo, yana gaba ina biye har gurin motarsa, da kaina na saka hannu na bude motar na shiga na zauna daga lokacin kuma ban sake sanin inda nake ba. Sai can na farka na ga yana kallona.

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un”

Shine abunda ya furta, kallonsa nai kamin na kalli titin sai a lokacin na lura da motarsa fake take a gefen titi kuma ba a cikin asibitin muke ba, Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya tashi motar muka hau titi, SJT hospital muka shiga, babbar asibiti mai zaman kanta a zamfara, asibitin masu kudi domin ko katin ganin likita kawai ya isa siyen wani maganin a yadda nake jin ana fada domin ban taba zuwa ba.

Agurin da aka tanada domin faka motoci ya faka motarsa sannan ya bude ya fita, ni ma na bude na fita sai wani irin sanyi baibaye ni sanyi ba na wasa ba, a take hakorana suka fara haduwa da juna.

“Koma cikin motar ki zauna”

Ya fada min sannan ya ciro wayarsa ya kira Hafiza yai mata kwatancen inda muke, tun da ya soma wayar na ke kallonsa har ya gama ya cigaba da latsa wayarsa, sak Abdulhamid nake gani a sura da hallitarsu sai dai shi ya dan fi Abdulhamid kwauri kadan, a hallaya kuma sun banbanta, tunawa da Abdulhamid sai ya haifar min da wata kalar damuwa a cikin raina.

“Abdallah”

Ni dai na san na kira sunansa har ya dago ya kalleni ban kuma san dalilin kiran nasa da nai ba, bayan ga wannan ban sake sani ko jin abunda ya fito daga bakina ba, kamar an min shocking dai na ji na dawo normal, amman a kasa nake zaune fuskarta har da hawaye da ban san yadda akai suka zubo ba, saurin tashi nai zaune na saka hannu na share hawayena a lokacin da na kalli Abdallah sai na ga idonsa cike da kwalla yana ta min kallon tausayi.

“Miyasa nai hawaye? Mi yake faruwa da ni...?”

Na tambaya ina kokarin fashewa da kuka, sai ya busar da iskar bakinsa

“Ba komai”

Da kansa ya kai hannunsa ya bude min motar.

“Shiga ciki ki zauna na ce”

“Ina son ganin yarinyar”

“Idan Hafiza ta zo zamu shiga ciki ki ganta”

Zaunawa nai cikin motar sai a lokacin na tuna da yata.

“Ko ina Namra take? Ko har da ita ta fada rijiyar? Kamar bata fada ba ko?”

Na tambayi kamar ya san amsar.

“Tana nan lafiya kalau”

Ban sake cewa komai ba, har Hafiza ta isa sannan na fito daga motar daman kafafuwa na waje suke, shi kuma ya rufe motar yai gaba muka bishi, mun yar tafiya mai dan ni sa sai dai ba sosai ba har muka isa bakin wasu dakuna, daki na hudu ya tura kofar ta bude sai ya tsaya be shiga ba yai min alama da na wuce. Ni na fara shiga sannan Hafiza sai kuma shi.
Chapter 58 · 0% Book details