← Book details Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 136

Sashe 94

Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Uba wani jigone na rayuwa, bayan Allah da manzosa, iyaye ne suke da muhalli na biyu a rayuwar ko wane dan'adam, daga lokacin da ka rasa uba za a fara kiranka maraya, saboda uba gangone na gingina, shi zai nemo ya kawo a ci, shi zai tufatar ya ciyar ya shayar ya ilmantar, uba wani jigone na rayuwa, gata ne, uwa kuma ita ce gaba daya rayuwar, idan babu uwa duk farincikin da zaka samu a duniyar nan ragaggene no matter what it's, uwa abokiyar tafiyar rayuwa ce, abokiyar shawara abokiyar kuka abokiyar dariya abokiyar farinciki abokiyar bakinciki, idan da yai kuka ka ji ba a rarrashe shi ba, to babu mahaifiyarsa a kusa ne, macen da zata dauki cikinka tun yana da second daya har yai wata tara ta haife ka ta jure kashi da fitsarinka ta rayu da kai a ciwo da ba ciwo, har ka mallaki hankalin kanka? Uwa ita ce gaba daya duniyar. No never... I can't imagine my life without one of them they are my super supporter's my everything”

Na karasa cikin kuka, ina jin wani irin shauki da kaunar iyayena ya kara kamami, iskar bakinsa ya busar ya jingina da kansa jikin kujerar motar yana kallona kamar bashi ba.

“Zan kai ki gida gurin Hajiya ki yi sallah”

Na share hawayena ina kallonsa.

“Mun tashi daga aikin ne?”

Na gyada min kai yana kokarin parking motar still idonsa na kaina.

“Idan haka ne ai kara na wuce gida kawai”

“No gurin Hajiya za ki yi sallah”

Bance masa komai ba sai na maida dubana gurin yan yatsun hannuna, ina jin faduwar gabana yana karuwa ga wani uban ciwon kai da ya saka ni a gaba, ban san miyasa yau Ahmad ya zame min wani dabam ba shi ba.
Key yai ma motar muka hau titi wannan karon ba mu yi tafiya mai nisa ba muka isa gidan, horn daya ya danna aka bude masa gate, ya kunna kai a cikin gidan, be yi farkin a ko'ina ba sai bakin kofar falonsu, fita yai shi kadai yace na jira shi a motar ya shiga cikin, be jima ba ya fito ya bude min motar yace na fito, haka na fito ina jin jikina ba kwari na shiga ciki, kamar dai wacan karon wannan karon ma Hajiyar da far'a ta tarbe mu sai dai yanayin yadda take kallon fuskata tana nuna alamar tausayi.
Bayan mun gaisa, tai ma Kanwarsa magana tace ta kai ni ciki nai sallah, da sauri yarinyar da aka kira da Siyama ta tashi tai min jagora har dakin Hajiyar, a bathroom dinta nai alwala ko da na fito an shimfida min carpet an dora Hijabi sama, sai kawai na dauka na saka na fara sallah azahar a lokacin uku ta kusa. Ina sallah shaidan ya fara yayo min tunani kala kala, kamin na gama sallah jikina har rawa yake, ina gamawa na cire hijabin na dauki veil din abayata na yafa na fito falon inda Hajiyar take na zauna, Ahmad ma yana zaune a falon ina son nai masa magana na kasa.

“Siyama kawo mata abincin”

Ya fada yana kallon yanayi gaba daya idona ya fito fuskata ta sauya.

“Wayata ina son magana da.... ”

Tun kan na karasa ya tari numfashina.

“Zan baki anjima”

Wannan karon kallonsa nai da kyau.

“Wa na rasa Ahmad? Uwa ko Uba, ko yaya? Ko kane? Fada min”

Mikewa tai tsaye yana kallona sai nima na mike tsaye. Can kasa kasa na jiyo Siyama na fadin.

“Ku fada mata gaskiya mana, dole ne ta sani”

“Siyama fita ki bar falon nan”

Ahmad ya fada mata a tsawace, kamar tana jira ta juya ta fice cikin fushi.

“Ka fada min wanda na rasa, ba zan iya dawo musu da rai ba, iyakar abunda zan yi hakuri ne”

“Muje na kai ki gida”

“Ka bani wayata”

Na daka matsa tsawa da wata irin murya daban taba sanin ina da ita ba, gaba daya jikina rawa yake.

“Ina da kanen, idan an rasa Uba sun zama marayu wa zai kula da su, idan na rasa Uwa wa zai maye musu gurbinta shikenan sun rasa gata”

Na fada ina rufe ido kamar mai nazari.

“Allah baya barin wani dan wani duk a can muka fito iyayenmu sun tafi sun bar mu, kuma a can zamu koma gaba daya”

Mahaifiyarsa ta fada idonta cike da hawaye, takawa na fara yi sai na ji kafar ta malgwade ina neman faduwa har sai da tai saurin rike ni, a hakan na sake unguri takawa kafafuwan suka fara rawa sai ta na tsaya cak, da nai unkuri na uku sai na tafi zan fadi har sai da Ahmad ya rike ni da kanshi ya zaunar akan kujerar.

“Ki natsu sai na kai ki gida”

“Ka kaini yanzu”

Na fada kai tsaye tare da mikewa tsaye na fara tafiya cikin karfin hali, ba shiri na ji numfashina yai sama wani hudu ya baibaye idona, jikina kuma yai arba da kasa.....

__________________________

Allah ka jikan mahaifina kai masa Rahama ka saka aljanna ta zama makomarsa, Mahaifiyata kuma ka karasa mata lafiya da kwanciyar hankali da natsuwa ka yafe mata kurakuranta kasa ta cika da imani 🙏 da duka sauran iyayenmu musulmai 😭🙏

Rashin iyaye wani ciwo ne da ba a manta shi 💔💔💔 may Allah see us though. 🙏
7/21/21, 10:47 PM - Buhainat: *GOBE NA...*

By Khadeeja Candy

4️⃣7️⃣

A yau kam kamar an halittoshi ne kawai domin kallon Halimatu, ya kasa zama kamar yadda a tsayin ma ya kasa yin nesa da ita sai daf da gadon da take kwance, fuskarta yake kallo, be taba tsaya ya kalleta kamar haka ba, daman can ahali shi ba mutum ne mai tsaya ya kwankwace mace ba.
Amman a yau yana jin kwanciyar hankali da natsuwa a kallon Halimatu, dogon hancin ya fara kurawa ido kamin idanuwansa su sauka akan karamin bakinta, fuskarta circir bata da rama kuma bata kumbura sosai ba ta cike abunta gwanin sha'awa, farin fuskarta dana jikinta har wani shining yake, ga jikinta Ma-sha-Allah irin wanda ake so a mata, tana da jiki sai dai ba can sosai ba, akwai kurciya sosai da yarinta a siffarta da surarta amman ba irin ta under 20 ba, irin wacce zaka kalleta kai zaton Amal ce yarta ta farko ba Adnan ba, babu abunda ta rasa a siffar ya mace sai na tsuwa da kwanciyar hankali.
Ta saman idonta yake hango damuwarta, labarin abunda ya same ta ta kuma yadda yake tunanin Gobenta zata kasance, be san miyasa yake tausayinta da yawa ba, yes be taba jin labarin daya taba masa zuciya ya hana hankalinsa kwanciya ba kamar nata, sai dai be taba tunanin hakan zai saka wani kusanci a tsakaninsu ba, the way da ya daukota ya kawo gurin Hajiyarsa, yadda yake ta kokarin boye mata mutuwar mahaifinta and ya bata tahirin rayuwarsa a free, ko da yake yayi hakan ne saboda kawai ya nuna mata ko da ta rasa ba ita kadai ce a cikin jarrabawa ba.
Kansa ya daga sama ya sauke numfashi a hankali, hannayensa duka biyu na zube cikin aljihu, can kuma ya sauke kan yana cigaba da kallonta, wani sinadarin tausayinsa ke fita daga cikinta yana shiga zuciyarsa, tausayinta ta cika zuciyarsa makil, a yadda take ya mace ace tana cikin irin wannan kalubalen na rayuwa ita din abar tausayi ce matuka.
Hannunsa ya saka aljihu ya fiddo wayarta, hakan nan kawai yaji yana sha'awar kunnata, and he press the power button ya kunna wayar. Hoton yaranta hudu a screen din wayar, he found himself smile yana shafa screen din wayar.

“Beautiful kids”

Ya furta yana maida hankalinsa sosai gurin kallon Amal, a zatonsa ita akai wa fyaden tunda ita ce karama marar wayo. He was just imagine if ace shine mahaifinta, ya zai yi wa mutum yana jin aransa zai iya kashe wanda yai wa yarsa haka, but look at them a maimakon ma ya yarda da mahaifiyarsa sai ya karyata ya saketa akan hakan, tunawa yai da lokacin da Namra ta bata har ya tsinceta, yanzu ya gane duka responsibility na yaran akan mahaifiyarsu, shi uban babu ruwansa, zuciyarsa ta cika da tsananin mamaki ashe ana samun useless father like her husband? Wayarta ce tai ringing sunan Abdallah ne rubuce a saman wayar, haka yai ta kallon wayar har tai ringing ta katse be dauka ba, at the end yai deciding ya sake kashe wayar ganin wata Number ma ta sake kira mai sunan Hajara.
Yana kokarin mayardar wayar aljihunsa aka turo kofar dakin aka shigo, wata dattijitowa ce da ba zata gasa 50+ ba, ko tantama babu yasan yar'uwar Halima ce tun da ya aika direba a can gidansu a fada musu ta suma ya kawo ta asibitin kuma wani nata ya zo ya zauna da ita.

“Sallamu alaikum”

Matar ta fada da katon Hijabinta, sai ya amsa mata yana binta da kallo.

“Ke ce?”

“Yayar mahaifiyar Halimatu”

“Alright, ga wayarta aje mata Allah ya sauwake”

Ya fada yana mika mata wayar, ita kuma ta karba tana masa godiya.

“An gode Allah ya saka da alheri ya kara sutura”

“Amin, an kai shi ne?”

“Eh an kai shi gidansa na gaskiya tun dazun”

“Ok”

Juyawa yai ya fice, sai da ya biya ya samu Doc Nura a Office dinsa yana duba wasu marar lafiya, tsaye yai har sai da ya gama.

“Doc zata kai yaushe kamin ta farka?”

“Zata dauki lokaci, tun har bata farka na da aka kawo ta nan, kuma a gida ma kace ai kun saka mata ruwa ko”

“Yes a can din ma bata farka ba”

“Hakan na nufi zuciyarta ba kamar tawa take ba, gaskiya akwai damuwa sosai a zuciyata, irin wannan bugawan zuciyan wani lokacin ya kan so da ajali, kara ma naka idan rai ya bace yana nunawa duk da shi ma mai hadarin ne, amman irin nata yafi naka hadari domin irinta za a cigaba da bata mata ran ne, ba tare da an san tana da wannan ba, idan kuma zuciyarta ta cigaba da buga kamar haka zata iya mutuwa a take, kuma ina tunanin bata shan magani ko?”

“Ban sani ba gaskiya”

Ya amsa zuciyarsa na kara cika da tausayinta.
Chapter 94 · 0% Book details