← Book details Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 136

Sashe 31

Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ina jin lokacin da suka fita daga falon da kuma tashin motarsa, wasu hawaye masu zafi suka sauko min daga inda nake zaune, ban taba jin wulakanci da kaskanci kamar na wannan ranar ba, ban tana jin na tsani rayuwata kamar yau, ban tana jin kyamar kaina kamar yau ba, na dade ina kare mutunci da martaba da aurena ko babu amman a yau wani wulakantacce marar daraja ya kawar da duk wannan.
  Komawa nai a gurin na kwanta kamar gawa, numfashin da ke fita daga hancina ne yake tabbatar da rayuwata,  zuciyata na zafi da ciwo kamar an saka takobi mai kaifi an yanka ta gida biyu. Sannu a hankali na fara jin numfashin kamar baya wadatar da hancina hakan yasa na bude bakina ina fitar da numfashina a hankali.
Ina jin kukan Amal amman na kasa dagawa na je gurin da take, jikina ya mutu kamar wacce akai wa allura, wayata ma dake kitchen ringing take sai dai yau ba ta Amal na ke  ba balle wayar. Kukan Amal da ringing din wayata suka ba ni wani yanayi na dabam, yanayin da ya saka ni tausayawa kaina da kuma yata Namra, ina ta auna irin halin da ta tsinci kanta ko kuma wanda zata tsinci kanta a ciki nan gaba...
  Ina kwance a gurin har dare ya raba, a lokacin Amal ta ci kukanta ta gaji ta tayi bachin wahala, sai a lokacin Allah ya kawo min kuzari har na iya rarrafawa na shiga dakina da rarrafe na iss bandaki, ba karfin jiki na kawai abunda na rasa ba har da na zuciya wanda shine silar rasa na jikin gaba daya. Duk yadda nai unkurin mikewa tsaye sai na kasa kamar wacce bata da fafuwa haka na zama, ba ciwo ko nauyinsu na ke ji ba, jin su nake kamar babu su a jikina raunin da ke zuciyata yana sauka har cikin jikina, ba jimin yai ba, amman a yau ina jina kamar cikkakkiyar budurwar da aka fasawa budurcinta.
Allah nai ta ambata a zuciyata, bakina kuma yana da rawa alamar kuka be kara min ba ko ma nace ban fara shi ba, jin jikina nake kamar ba nawa, daker na iya mikewa tsaye ban san abunda ya same ni ba sai zamewa nai na fadi kasa, ban sake unkurin tashi ba, a gurin na kwanta ruf da ciki hawaye na ce min sallamu alaikum har aka fara kiran farko na sallah asuba. A lokacin ne na samu kuzari har na gwada tashi tsaye bayan an zauna na yan mintuna.
Allah kuma ya amincin min na iya kunna hitar da ke bandakin na zauna a cikin tub din na rafka wani uban tagumi, ina ta neman inda hawaye za su fito min na rasa. Sai da na hada ruwan nai wanka na tsaftace kaina sannan na fito na dawo bakin madubin gadon ana zauna ina ta kallon kaina. A zahiri kaina na ke kallo amman a badini GOBENA na ke hangowa ya zata kasance? Miyasa abubuwa mabanbanta suke ta faruwa da ni? Idan na fita daga wannan sai na fadawa wannan? Mijina ne ya fado min a rai! Idan Abdulhamid ya ji zai zauna da ni? Zai cigaba da so kamar yadda yake? Zai kaunace mi mu cigaba da zama kamar mata da miji? Wata kila kuma ya juya min baya waye zai so wani namijin ya kusanci matarsa balle irin wannan da kika fashi? Ban san lokacin da na dauki Vaseline din dake gaban madubi ba na jefi gaban madubi da shi a take ruwan madubi ya tarwatse wani irin kuka mai taba zuciya ya ziyarce ni, sai ga ni a kasa ina kuka da hargagi kamar mahaukaciya, kamar wacce aka tsakala sai na yi saurin tashi zaune ina girgiza.

“A a ba zan fada masa ba, wannan sirina ne ni kadai ni kadai ya dace na rufe abuna babu wanda zai sani, ba zan taba fada masa ba, ba zan iya rusa farincikin aurena da kaina ba, ban shirya fuskantar wani kalubalen na rayuwar aure ba a yanzu, ba zan fadi abunda zai saka Abdulhamid ya tsane ni ba, ba zan fada masa abunda zai saka ya kyamace ni ba, ko wannan bakincikin zai kashe ni ba zan fadasa kowa ba, wannan kaddarar Halimatu ce ita kadai”

Wannan karon a fili nai maganar ina ta karfafawa kaina guiwa, duk kuwa da ina jin wani bangaren na jiki da zuciyar ya son sauya min tunani daga boyewar zuwa fadawa Abdulhamid gaskiya. Wani irin kuzari da karfin hali ya zo min a take nemi rashin karfin na rasa, tawul din jikina na cire na saka doguwar riga na fito falo da zimmar duba Amal sai na samu kaina da duba bayan kujerar na kasa dauke idona daga barin kallon gurin ina ta aina abunda ya faru hawaye na min zuba. Ba tare da tsoro ko fargabar komai ba na fito harabar gidan ina ta kalle-kalle kamar bakuwa, dubun asuba be hanani ganin ko'ina a gidan ba, ba su fasa mana komai ba bayan gate din da suka bar mana bude. Ba tare da tsoron komai ba na nufi gate din na da kaina  na rufe, ba tsoro ba, a yanzu ina jin ko mutuwa na shirya mata balle kuma tsoro. Falo na dawo na zauna na zubawa Amal ido kamar ance min ita ce maganin damuwata, wayar da ke kitchen din ce ta fara ringing cikin sauri na tashi na shiga kitchen din sai na tararda wayar kife a kasa hannu na kai na dauko wayar sai screen din wayar na gani a tsage sai dai hakan be hana ni ganin kiran Abdulhamid ba da sunan da nai saving din numbersa ✨🔐Final choice❤😍 tare da aljanun da nai yi ma sunan kwaliya da su. Samun kaina nai da kasa daukar kiran har ya katse wani ya sake shigowa ya katse sannan sako ya biyo baya.

“Baby na kira tun jiya ba ki daga ba ina son jin muryarki na isa lafiya. Pls ki kula min da kanki”

Ina gama karanta sakon na narke cikin wani sabon kuka na rumgume wayar a kirjina, ina ta jin kamar ba zan iya boyewa Abdulhamid, idan na boye masa ban masa adalci ba.

“Amman kuma idan na fada masa zai yarda? Zai gasgata ni bayan ba su dauki komi ba? Ba su fasa mana gate ba balle kofa, ba su harba bindiga ba balle na ce makota su ne shaida ta?”

A fili na ke ta aiko tambayoyin ina mai jin kamar akwai wani a kusa da ni ya amsa min su. Waya turo su? Da gaske kudin suka zo karba ko kuma daman can mutunci suka zo yagawa? Turo su aka ko su suka turo kansu? Ina suka ji ko suka san cewa Abdulhamid ya samu kudi ko zai samu kudi? Ban ankara ba na ji an tayarda ssallah Asuba hakan yasa nai hanzarin baro kitchen din na dawo dakina, alwala na fara yi sannan na gabatar da sallah asuba, na sani sarai ba kyau kukan da ba na tsoron Allah ba a sallah amman na kasa tsayarda da hawayena har nai sallah na gama, babu komai a addu'a ta sai tarin Allah ya isa da neman tsarin Allah daga shiga wata damuwar.

Misalin bakwai na fito falo jikina na min nauyi kamar ba nawa, gurin Amal na nufa na dubata har lokacin bachi take sai dai jikinta da zafi kamar jiya, hannu na saka na dauke ta na nufo daki da ita kamin na shiga dakin ta farka da kuka tana kiran sunana, amman na kasa amsa mata sai kokarin rabata da tufafin jikinta nake. Wayata ce ta sake ringing haka yasa na aje Amal na nufi inda wayar take, Final choice ne rubuce akan wayar har na yi kamar kar na dauka sai kuma wata zuciyar ta hanani hakan yasa na danna picking na kara wayar a kunne ina hawaye.

“A ka'ida idan kika daga wayata sallama kike fara min cikin nishadi da walwala, sannan gaisuwa ta biyo baya amman yau babu ko daya”

Ya fada bayan ya dauki lokaci yana sauraren numfashina, lumshe ido nai na bude hawaye na sauko min har lokacin ban samu kwarin guiwar fada masa damuwata, idan na fada masa ban san iya halin da zai shiga ba ban san ya zamantakewar aure zata kasance ba! Ban san ya zamu rika kallon juna ni da shi ba.

“Tabbas akwai damuwa a tare da ke matata, sai dai bana da tabbacin damuwar ta rashina ne a kusa da ke ko kuwa wani abun ne dabam, na ji ba dadi gaskiya domin har ga Allah bana son abunda zai bata miki rai a yanzu Haima, bana son wani abu ta zai taba zuciyarki saboda ina matukar kaunarki.....”

Wasu zafafan hawaye ne suka sauko min ban san lokacin da naja dogon numfashi na sauke ba.

“Fada min waya taba ki?”

Ya sake tambaya, sai na girgiza masa kai kamar yana gabana, sannan nai saurin share hawayena.

“Babu komai babu komai I'm fine”

“No you're not pls....”

“Trust me babu abunda ya faru kawai dai ya farka ne jikina babu dadi kuma i miss you so much”

Daga can cikin wayar ina iyo jiyo sautin murmushinsa tare da aje numfashin jindadi a lokaci daya.

“Karki damu yau zan dawo ai ni kaina i miss you alot, fada min me kika ci?”

“Yanzu zan karya ban farka da wuri ba”

“Haima bana son kina zama da yunwa fa, ace har yanzu ba ki karya ba? Pls ki daina haka bana so okay”

“Yes ba zan sake ba”

“Je ki karya zan sake kiranki, i love you”

Kai kawai na iya gyadawa na sauke wayar daga kunne na hawaye na min zuba kamar ba gobe, a hankali na zauna a gurin ina jin wani abun marar dadi yana ratsa zuciyata.

“Wani ya taba ni Abdulhamid wani ta taba maka mata, wani ya keta haddin matarka wani ne ya rusa raguwar farincikina, wani ne ya saka ni a dakin da ake dandana dakin fyade da ke da ke tarbar ko wace mace mai aure ko budurwa wacce namiji ya keta mata haddi, an yi ma yata jiya kuma ni akai yi wa? Right.... ”
Chapter 31 · 0% Book details