← Book details Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 136

Sashe 81

Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Ta ina za ki bi? Na sauke ki”

Kamin na bashi amsa Ahmad din ya tari numfashinsa sound so serious fuskarsa babu alamun wasa.

“Shi kuma wacan aikin wa zai yi?”

Nikam daman ba shiga motar zan yi ba, hakan yasa kamin ma Yunus din ya bashi amsa na ce wa Yunus din.

“Na gode ranka ya dade zan fi sakewa idan na hau napep”

Daga haka na juyo na fito daga office din ina mamakin irin kiyayyar da Ahmad ke min akan abunda har a gurin Allah bana da laifi domin ban aikata ba, wato yaji haushin da Yunus din yace zai rage min hanya ko waya fada masa ma shiga zan yi oho.
Da tunanin hadarin na fito hakan yasa ban wani tsaya canja tufafi ba yafa mayafina na dauki kayan na saka riga a handbag dina domin ita kadai zata iya shiga sauran kuma na rike a hannu na bi hanya domin tuni abokan aikina sun wuce har wasu sun karbi duty.
Ina tafiya aka fara yayyafi ban yi zaton zai yi karfi ba, hakan yasa na kara harama da zimmar kamin ruwan yai karfi na samu abun hawa, da ganin hadarin ba irin wanda idan an fara ruwan nan ba ne a daina, wata kila za a dade a na ruwan.
Ko da na fita gate babu masu Napep sai achaba su ma kuma kowa da goyonsa, sai gudu suke ni kuma na maida himma sai tafiya nake ina waige waige ko zan samu abun hawan, ban nisa sosai da kamfanin ba aka sako da wani ruwa mai mugun karfi, hakan yasa ni cira kafa har da dan guduna na nufi inda wata yar rufar kwano wacce ke kusa da inda Kabir yake. Babu kowa a gurin hakan yasa na shige rumfar da sauri na fake, domin tuni ruwan ya fara jikani. Sai dai wani abun mamaki duk ruwan nan da ake Kabir na zaune a inda ya saba zama ruwan na duka kansa, ban san lokacin da tausayinsa ya rufe ni, da sauri na aje kayana da jakar hannu a gurin na fita a ciki a rumfar na nufi inda yake cike da karfin hali domin a yanzu kafar ta fi min zafi fiye da dazun. Da fari magana na fara masa akan ya taso ya bar gurin sai na ga yana ta kallona kamar be gane ni ba, hakan yasa na kai hannnu zan riko shi, aiko kamar jira yake sai ya hayayyako min yayi cikina yana zare ido abun be taba, ina baya baya yana cikina har samu sa'ar riko mayafina ya fisge shi gani a gafen titi hakan yasa nai unkurin gudu sai yai nasarar kai mun duka mai shegen zafi, ya kuma rikoni yana kokarin makureni.

“Ni ce ni ce Kabir.....”

Shine kawai abunda nake iya fada cikin ihu da daga muryar, tare da kokarin kwatar kaina amman ina karfin mace da namiji ba daya ba tuni ya samu sa'ar fara makurata, ga ruwan sama ana yi balle a kawo min agaji, ko ma ba a ruwan ba kowa ke shiga lamarin mahaukaci ba ballantana ma gurin babu jama'a sosai.
Kamar daga sama na ji ana kokarin taimaka, sai duka ake kaiwa Kabir ta ko'ina ban san ko waye ba har sai da na samu sa'ar kubucewa daga hannunsa, ruwan dake sauka da kuma makurar da na sha bata hanani gane cewar Ahmad bane, abunda ban tana zato ba, ban tana tunani ba balle har nai mafarki yau yake faruwa a zahiri. Nikam ban tsaya komai ba ganin fadan ya koma tsakaninsu yasa na dauki mayafina da sauri na nufi inda jakata take na dauka tare da kayana na fara tafiya kamar an koroni ko waige inda suke ban sake ba.
Sai da nai tafiya mai nisa sannan na soma tafiya a hankali ina cigaba ta taron Napep, cikin sa'a motar Abdallah ta wuce ni sai kuma ta dawo baya daidai ta tsaya daga can cikin motar ya bude min front seat. Da sauri na shiga jikina har rawa yake.

“Ina kika fito?”

Ni dai ban iya bashi amsa ba domin har yanzu ban gama dawowa daidai ba.

“Ina kika fito...?”

“Aiki”

“Aiki da wadannan kayan? Wando ne fa a jikinki da riga..”

Na dan kalli jikin nawa, ruwan da ya jikani yasa tufafin sun dan kama jikina.

“Karki sake saka su daga yau, idan ba barki ki saka tufafinki na hausawa ba, ki daina aikin”

“Am.... ”

“Ba shawara nake ba ki ba, umarni ne”

Ya fada yana daga min hannu fuskar nan tasa a hade kamar dai ba shi ba.

AHMAD POV.

Hannunsa ya kai ya ciro chewing gum din daga bakinsa sannan ya mike tsaye ya nufi window ya jefar da cingan din yana cigaba da yatsinar fuska.
  Ai tun farko be kamata ya ci cingan din ba ko da ba ita ta aje masa ba balle kuma a hannunta ya fito macen da babu ta biyunta a gurinsa gurin tsana. Yawun bakinsa ya tofar a window Yunus dai be ce masa komai ba bayan kallon da ya bishi da shi sannan ya fice.
  Haka ya wuni yana tofar da yawu kamar wani mai sabon ciki, yaba ta jin haushin tauna cingan din da yai, daga bisani ya koma jin haushin Siyama wacce ta bukaci ayi masa abun, kamin jin haushin ya koma gurin Yunus wanda yake ganin shi ya biye mata.
  After sallah azahar Yunus ya shigo office din yana sanar masa cewar bakinsu sun iso.

“Amman Dahir ya zo”

“No yana kan hanya dai”

“To ya za'ayi communication da su”

“Karka damu da wannan, yanzu dai kaje ka gaisa da su”

After haka ya fice, Ahmad ya bata minti biyar a zaune sannan ya nufi freezer dake office din ya bude ya dauko sweet ya bude ya saka a bakinsa, dan yasan ba zai je can yana tofe tofen yawu ba sai kace mai sabon ciki, idan ma be sha sweet din ba tashin zuciyar da yake ji ba ba zai bar shi ba. Sai da ya dauki rigarsa ya saka sannan ya nufi dakin taro, yana shigowa suka mike tsaye tare da bashi hannu ya gaisa da su da halshen nasara ya fara yi musu barka da zuwa duk kuwa da yasan ba lallai ace suna jin wani abu bayan welcome da kuma gaisuwa ba.
A gurin daya saba zama ya nufa ya zauna, yana kokarin ciro wayarsa daga aljihu aka turo kofar dakin Yunus ne ya shigo, Halimatu na bayanshi ta tsaya daga jikin kofar har sai dai Yunus din yai mata iso, wani irin bugawa zuciyarsa tai, duk sai yaji ransa ya bace sai dai ba damar ya nuna a gaban mutanen a dole ta sa ya shanye, sai dai yana mamakin abunda ya kawo ta dakin taron. Takawa ta fara yi tana juya yai arba da mazaunanta sai yai saurin runtse idonsa duka biyu, can kuma ya bude dayar yayinda dayar take a makkale ya rufeta, sai kuma yai saurin rufewa yana jan tsaki a ransa. Be bude ba har sai da yaji ta fara magana da su alamar ta juyo kenan sannan ya bude ido, kallo daya yai mata yaga yadda kayan suka karbe ta sai kuma ya dauke kai. Har akai meeting din aka gama be bari ta san yana kallonta ba, ba ma ita ba ko Yunus da ke kusa da shi ba zai iya gano ya kalleta ba ko a'a domin ta kasa kasa yake kallonsa irin na munafukai.
After sun gama ta bukaci fita sa Yunus ya nemi rage mata hanya a take Ahmad yai karaf ya hana shi, yana ta mamakin shisshigi irin nasa, after ta fice ya tabe baki ya tashi tsaye ya face daga kamfanin, office dinsa ya nufa yana kara jin bachin rai na kama shi, zaunawa yai saman kujerarsa ya rufe laptop dinsa sannan ya fito daga office din ya nufi gurin motarsa da sauri, so yake ko da za a sako da ruwan yana gida ko banza yau ai ranar birthday sa ne.
A hankali yake tukinsa, sai dai kamar yadda ya kusan zame masa ibada kallon gurin da mahaukacin nan yake zama a kullum saboda abincin da Halimatu take ba shi yasa shi kallo a yau, yana tunani a yau kam ba zata tsaya ba tun da ta fita tana sauri kuma gashi garin har ruwa ya fara sauka, to his surprise sai ya hangota a gurin tare da shi, at first ya dauka ko wani abu ne mai kama da wasa daga baya ya fahimci kokuwa ce suke wanda be san dalilinta ba.

“Ashe dai itama bata da hankali, daman can ba tai kama da masu hankalin ba”

Ya furta sannan dan karawa motarsa wuta, kamin ya sake kallonsu da kyau ya fahimci dai fada suke, sai kawai ya faka yana ta kallon yadda mahaukacin ya kai mata duka kamin ya hango mahaukacin ya makureta har tana neman taimako. Cigaba yai da kallonsu, har sai da ya fahimci da gaske mahaukacin kasheta zai yi sannan yai unkurin bude motar, a take wata zuciyar ta hana shi, then ya fara tunani ai shi human being ne not like her, ba zai iya kallo ayi kissan kai ba. Cikin sauri ya fita daga motar ya nufi i da suke ya fara dukan mahaukacin ta baya har Halimatu ta samu sa'ar kubuce a hannunsa ta ranta a na kare sai fadan ya dawo tsakaninsu da mahaukacin shi da mahaukacin aka rasa mai hankali kowane kai wa wani duka yake, a cikin rashin sa'a mahaukacin ya naushi idon Ahmad ai take ya ji kalar garin ta canja, be san lokacin da wani karfin ya zo masa ba ya saka kafafuwansa ya buge Kafafuwan mahaukacin ya fadi kasa, a take Ahmad ya ranta a ciki na kare yana dafe da ido daya ya nufi motarsa a rikice ya bude motarsa ya shiga saboda wani azababben zugi da idon ke masa, @360 ya fisgi motar da ido daya da yake gani da shi.
7/21/21, 10:46 PM - Buhainat: *GOBE NA...*

By Khadeeja Candy

4️⃣2️⃣
Chapter 81 · 0% Book details