← Book details Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 136

Sashe 86

Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Sai a lokacin ya tuna ba shi kadai yake a motar ba, Hajiya tana baya tare da shi.

“Gida za mu je”

“Na ga ka dauki wata hanyar ne”

Sai a lokacin ya lura, bakinsa ya cikawa iska ya busar sannan yace.

“Zagoyo zan yi”

“Okay, bikin nan ya kayatar sosai fiye da yadda aka saba yinsa a shekara, wai ka gane wacce ta ci gasar nan kuwa?”

Hajiya na yin maganar zancen yaranta ya fado masa, na cewar idan ta ci zata biya musu kudin makaranta.

“Wow....”

Ya furta a fili yana jinjina irin jarumtarta da karfi zuciya. Hajiya kuma sai ta dauka da ita yake sai kawai ta cigaba da shimfida masa labarin.

“Wannan ce fa mahaifinyar su Namra yarimyar da ke tare da Baby Namra, ashe har yanzu bata manta da ita ba, tace idan ta ci sadaukarwar ta Baby Namra ce”

Be ce komai ba sai tukin yake a hankali yana jin wani abu na masa yawo a zuciya na rashin jindadi har suka isa gida.

“Labarin ma da aka karanta ina kyautata zaton na mahaifiyar yarinyar nan ne Halima.... ”

“Halima...... ”

Ya maimaita sunan yana kokarin juyowa ya kalli Hajiya, be taba sanin sunanta ba sai yau, duk kuwa da aikin da take a kamfaninsa, sunan da ya fi ko wane suna yi masa dadi a duniya, har yanzu yana ganin yadda ya wulakanta a kamfaninsa a lokacin da ya bukaci a canja mata position sai a yanzu yake ganin hawayen da take da irin rokon da ta soma masa tana kuka tana fadar dan Allah kar ya koreta tana bukatar aikin nan, and in the restaurant a vip 1 a lokacin da ta zauna a saman kujerar sa matarsa take zama, he remember wadansu kalamai da ta fada, wacce take nan ta yi sa'ar ba kamar ita ba, daman duk wannan take nufi?

“Oh ya rabb”

Ya furta a fili gaba daya zuciyarsa ta daure ta yi nauyi da tausayin Halima. Can ya tsinkayo Hajiya na kokarin fita motar tana fadin.

“Domin labarin da mahaifiyarta ta ba ni, yayi daidai da abunda aka fada a gurin nan kuma ga shi taje tare da yaran, ina jin labarin na gane ita ce, cikin ma uwar bata fada min duka ba, tun da wani abun sai a yanzu na ji, amman matar nan ta ga rayuwa Wallahi ban san lokacin da nai kuka ba”

Fitowa yai daga motar yana kallo mahaifiyarsa wacce ke sanye da tsadadden lace.

“Amman Hajiya ba ki taba fada min ba”

Hajiya ya kalleshi da kyau.

“Ina zan fada maka labarin makiyiyarka? Matar da kace baka son jin komai nata”

“Da kin fada min ko da a tsawace ne, ko kuma ki cilasta min saurare ai dole zan ji, wani mai imani ne zai ji labarin matar nan be ji tausayinta ba?”

Ya fada yana hade yatsunsa fuskarsa dauke ta tausayi.

“Duk lokacin da nai unkurin fada maka sai kace ba zaka saurara ba, tausayinta ne yasa na hana ka kaita kotu ai, ko lokacin da aka fada maka bata cikin hayyacinta ba cewa kai karya ne ba, saboda kawai ta kashe maka ya ne? Ni ko na san mai imani ba zai kashe rai ba sai idan wata kaddara ta fada masa, sai a yanzu da Allah ya kaddara ya bude maka zuciya ka ji komai”

Yes he remember an fada masa she's unconscious ya ki yarda, and he remember how her father beg him akan case din amman be saurareshi ba, and the slap a lokacin da ta kawo Baby Namra asibiti ya mareta har sai da ta fadi..... Ji yai wani irin abu na rashin jindadi da kyautatawa ya mamaye shi, be taba jin tausayin wani abu mai rai kamar a yadda ya ji tausayin Halima ba a yau, a waje daya kuma yana ta jinjina karfin hali da dakiyar zuciya.
Part dinsa ya nufa yana ta tunani kala kala yes hak rayuwa take zaka ga mutum kawai sometimes a cikin farinciki amman ba san abunda yake zuciyarsa ba, ba zaka iya fassara damuwarsa ko nasararsa ba, da ace be ji labarin Halimatu ba da har yanzu be daina mata kallon makiyiyarsa ba, wata kila da Allah kadai ya san irin abubuwan da zai mata....
A dare kwana yai da tunanin abun a ransa, duk kuwa da yasan condition dinsa rage yawan tunani yana ciki.

HALIMATU POV.

Labarina ya taba zuciyar mutane da yawa a guri kuma nima ya taba ni a karan kaina, domin sai rayuwar da tunanin gobena ya dawo min sabo. Iyakar kokarin da nai kar nai kuka a bainar jama'a ne, sai dai na zubar da hawayen da ban san adadinsu ba, an rayuwata ta lalace kuma an bata ta yata, amman na yarda da wani abu daya, ko dan yayana zan rayu, zan kara jajircewa zan tsaya tsayin daka na amsa sunan da Ummulkhar ta kira ni da shi wato Jaruma.
Rai na ya kwadaitu da zancen kudin da ta ware min a cikin albashin kamar yadda ta fada, sai dai ina tunanin karbarsu abu ne mai wahala a gurina domin zai iya zama silar da zata saka a gane ko wacece ni wanda hakan zai hanani sakewa cikin mutane.
Ba mu tashi daga taron ba na ji alert a wayata, na naira miliyan daya, aiko a take na nemi damuwata na rasa farincikin ganin kudin ya maye gurbinta.
Cikin murna muka fita daga taron wani abun burgewa sai muka zama abun kallo har da masu dauka hoto a tare da mu da award din da aka ba mu, ina yin gaba kadan na hadu da blessing abokiyar aikina, sam ban san ta zo taron ba sai da tai min magana mun gaisa da ita ta tayani murna sannan ta gaisa da su Namra tana fadin ashe ina da yara. Sai nai murmushi.

“Ke ma ai kin san ina da yaya”

“Eh amman ban dauka har hudu ba, kuma kyawawa da su har sun fiki kyau”
Chapter 86 · 0% Book details