← Book details Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 136

Sashe 103

Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jin haka yasa na bude motar na shiga, ina kallonsa sai na ga idonsa sun kumbura sun yi ja sosai alamar ya ci kuka ba kadan ba har ya sauya masa kala. Mun dauki lokaci mai tsawo zaune a cikin motar be ce min komai ba kuma ya kasa kallon inda nake, ni kuma mamaki ya cika ni ina tunani yau kuma da wacce ya zo.

“Yau ce rana ta karshe Halima, da zan daina rokon ki dawo gareni, a yau kan na yarda na rasa ki har abada, a yau na yarda na yi kuskuren da ba zai taba gyaruwa ba, a yau ina rokon Allah ya baki miji na gari wanda zai taimaki rayuwarki, wanda zai baki soyayyar da kika rasa a gidana, wanda zai nuna miki kulawa, ya fifita ki ya tausaya miki, wanda ba zai wulakanta ki ba kamar yadda nai yi.....”

Yai shiru sai kuma ya kai hannunsa ya kama hijabi ya jimkeshi sosai a hannunsa.

“Wallahi ji nake kamar na bude bakina na dauke ki na saka a ciki na hadeye ki zauna a cikina har a bada amman babu wannan damar, na riga na rasa ki har abada, ina son ki Halima ina son ki san da wannan ko bana raye, duk abunda nake miki a baya ina yi ne kawai ba dan bana son ki ba, ina yi nw kawai saboda sharin zuciya da kuma ajizanci na dan'adam, dan Allah ki yafe min”

Wasu irin hawaye yake yana kallona numfashi na fitar masa daker, a take jikina yai sanyi.

“A lokacin da kike fada min illar abunda nake yi, da cutar dake na ke yi ban ga hakan ba sai yanzu da lokaci ya kure min, na tuba tuba na gaskiya, amman ba ni da tabbacin idan Allah zai yafe min abunda nai, kuma ina jin tsoron haduwa da shi, shin a yanzu idan nai jinya na mutu jinyar zata zama silar kankarewar zunubaina ko kari? Saboda ni na jawa kaina”

“Ban gane wannan maganar ba...”

Na fada muryata na rawa, dayan hannunsa ya kai ya dauko farar takardar ya miko min.

“Ba kawarki kadai nai mu'alama da ita ba, amman ina da kyautata zaton ita ta laka min ciwon, domin na naji labarin kawarki Sa'adatu tana dauke da cutar bayan na tuba na daina mu'alama da ita, ban yi tunanin komai ba ban kawowa raina komai ba, har sai da wannan abun ya faru dukan da sojoji suka min da aka kai ni asibiti, sai suka min gwaje gwaje, a ciki na samu wannan, bayan na warke na koma gida na sake zuwa asibiti biyu ina samu result daya, and do you know what? Da aka saka Sadi yai gwajin sai aka samu shi ma yana dauke da ita, haka ma Murja kuma ina kyautata zaton dukansu ta dalilina suka samu..... ”

Tuni hawayena ya jika takadar da ya kunna min wutar cikin motar ina karantawa.

“Hiv Aminu?”

Ya gyada min kai yana kara jinke hijabi hawaye ma sauko masa. Ban tana jin tausayin Aminu ba tun bayan rabuwar mu sai yau.

“Zina ba tai ba Halima, bata haifar min da komai ba sai bakinciki da talauci, na yi wa yar wani an yi ma yata, na yi da matar wani kanena yayi da matata, yanzu kuma ta jefani a ramen da babu mai ceto ni, daga ni har Sadi har Hajiya ba mu da kwanciyar hankali da natsuwa tun daga lokacin da abun nan ya faru har yau ko abincin kirki Hajiya bata iya ci......”

Ya karasa yana jingina kansa jikin sitiriyarin motar ya fashe da wani irin kuka mai taba zuciya.

_______________________

Wayyo Aminu ya bani tausayi 😢😭
To ita kuma Halima me take nufi da Ahmad? 🤔 ko da yake tana da gaske ance duk hadarin daya baka kashi..... 🤥

Har Gobe ina Team Abdallah 😘😘😘
7/21/21, 10:48 PM - Buhainat: *GOBE NA...*

By Khadeeja Candy

Ina godiya sosai Maman Sayyed,  sakonki ya riske ni, Allah ya bar kauna kuma ya ba ni ikon yi kullum 🥰

Gaisuwa ga duk makarantan labarin Gobena, a duk inda suke Allah bar kauna 🥰🌸❤️

5️⃣1️⃣

Wani lokacin Allah yana mana talala mu yi ta aikata zunubi har sai idan ya tashi kama mu sannan yai mana damkar da zata saka mana nadama da dana sani, a duniya kenan da Aminu ya fara haduwa da sakamakonsu, to ina kuma a lahira? Sai dai ina kyautata masa zato kasancewarsa musulmi kuma ya gane kuskurensa ya tuba, Allah yana son bayinsa masu tuba.
Na shiga gida da tunanin Aminu a raina, ba ma ni ba a halin yanzu Aminu be isa ya tunkari wata mace yace yana sonta ba, sai idan mai dauke da irin lalurarsa ce ko kuma idan boyewa zai yi, wata kila ma yayan da yake aibantawa yana cewa na haifa masa yara da yawa zam tsofar da shi sune kadai yaran da Allah zai ba shi. A ranar na kudirta a raina cewar ba zan fada musu cewar mahaifinsu yana dauke da cuta ba, fada musu ba zai haifar musu da komai ba sai tashin hankali duk kuwa da kasancewar akwai kurciya a tare da su, ba lallai ne su fahimci komai ba.
  Har ga Allah na jidadin da cutar ta kama Sadi da Sa'adatu ko ba komai dukansu sun ci amanar aure kuma sun ci amanata, Sa'adatu kawata ce ta zabi tai mu'amala da mijina bayan kuma ita ma din tana da aure da yara, sadi kuma ya ci amanar dan'uwansa yai ma yar dan'uwansa fyade, ko da yake har da sakacina a wasan lokaci na barinsu da nake suna kebewa a tare yawan shige masa da take ban taba hanawa ba, saboda ban kawowa zuciyata komai a kansa ba, ko da yana zina ban tana ayyanawa a raina cewar zai iya lalata yar dan'uwansa ba, ashe duniyar ta dade da canjawa daga sanin da nai mata, a yanzu babu yarda a tsakanin yaranka da kowa, domin bayan Namra na yi ta ganin labarai masu sosa zuciya wasu uncles dinsu zasu lalata su wasu kuma ubansu na ciki ko makota, kai har malaman makarantar boko da islamiya ba a bari ba, hakan yasa na kara saka ido akan duk wani motsi na yayana ba mata kadai ba har mazan domin suma ba a yanzu ana lalata su, mun kai wani zamani da babu aminci a zukatan mutane kowa kokarin cutar da kai yake.
A washe garin ranar sai na tashi kamar wata marar lafiya, ba labarin Aminu kadai daya saka jikina sanyi ba har da tunanin Ahmad abunda ban tana ba, ko da dai rana ban tana kwantawa ko tashi da tunaninsa ba. Sai dai jiya na raba dare da tunanin abunda yai min da wasu alamomi da sai a yanzu nake fahimtar inda ya dosa.

“Hello Lims fatar kin tashi lafiya Happy birthday”

Shine farkon abunda ya fara shigo min a waya, kamin na bank dina su turo min. Ni kan har na manta da wani zancen birthday sai yanzu.
  Aje wayar nai na fito tsakar gida na debi ruwa na shiga daki na juna a electric kettle, haka na bi yarana na zuba musu ruwa sukai wanka sannan suka karya suka saka uniform. Zuwa nai na gabansu na risina ina kallonsu wani irin farincikin marar misaltuwa ya lullube ni lallai yara rahama ne, no matter how suke rashin ji ko suke cutar da junansu.

“Allah yai muku albarka ya shirya ku da duk yaran musulmi, ya tsare ku.”

Duka suka amsa da amin, daya bayan daya na busu da addu'a ina dafa kansu ina karantawa har na gama sannan school bus dinsu ta iso, da gudu suka fita daga gidan kowa yana kokarin ya riga dan uwansa gwanin sha'awa. Da kallon kauna na bisu zuciyata cike da shauki ina murmushin jindadi da yi ma Allah hamdalla. Ina juyawa sai ga Namra ta dawo tare da Adnan suna rike da wani katon kwali wanda daker ma suke iya daukarsa, an nade kwalin da fata jar leda mai kyale.

“Momy Momy gashi inji direban Bus yace wai a baki”

Jin hakan yasa nai saurin tashi na karasa na karbi kwalin.

“To Momy bude ki sam mana abunda ke ciki”

Namra ta fada jikinta har rawa yake.

“Kin san abunda ke ciki?”

“No”

“To kuje makaranta idan kun dawo zan ba ku nima ban san miye a ciki ba”

“Momy to waya baki?”

“Namra... Ba yanzu kika karbo sakon ba? Ni ina zan san wanda ya bani to?”

“Momy ai shi mai bus din mu ba son ki yake ba ko?”

Ta tambaya tana sako min ido, sai a lokacin na daka mata tsawa domin na fara gundira da tambayoyinta.

“Ban sani ba, wuce kuje sarkin gulma”

Dariya tai ta nufa kofar fita da gudu daman tuni mai bus din ya danna musu horn alamar yana jiransu.

“Daddy na yace idan wani ya zo son ki na fada masa, kuma sai na fada masa wannan”

Hafiza wacce ta nufo dakin da nake ta tari numfashinta.

“Tsohuwar munafuka ki ce tace masa i love you”

“Mama Hafiza i hate you”

Ta karasa fada sannan ta fice daman shi Adnan tun da ya aje kwalin ya koma ita ce dai ta tsaya gulma. Aje kwalin nai a tsakiyar falon Mama na gagara budewa, ko ba a fada min ba na san Ahmad ne yai domin shi yasan yau nake birthday gashi kuma direban motar scul dinsu ce. Hafiza ce ta bude kwalin sauran yan'uwana duk suka zagaye kwalin kowa yana son ya ga abunda ke ciki, katuwar kwalbar strawberry guda biyu ta fara fitarwa sai cake dan madaidaici wanda aka rubutawa happy birthday, a kasan cake din wani madaidaicin kwali ne, da kanta ta bude kwalin sai ta ciro wata farar takardar sannan ta ciro turare man shafawa da wata sarka wacce nake kyautata zaton zinari ne.

“Oh my god oh my god see love abeg duk Babban Baby Namra ne ya aiko ko?”

Ta tambaya tana kallona, sai na rasa me zan ce mata idan nace a a na yi karya tun da fa gaskiyar a bayyane, ban gama tunanin irin amsar da zan bata ba na ji ta fara karantawa wasikar dake tare da kayan.
Chapter 103 · 0% Book details