← Book details Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 136

Sashe 10

Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na fada sannan na ratsa ta gefensa zan wuce.

“Ke kanki rayuwarki tana cikin hadari Halima, abunda zai fi miki kwanciyar hankali is ki raba kanki da wannan mutum, gashi yanzu dan'uwansa ya maida miki Namra babbar mace!”

Wani banza kallo na watsa masa.

“Kana tunanin akwai hikima abunda kake fada min a yanzu? Kana ji a ranka ya dace kai min wannan maganar a yanzu? Na kashe aurena na fito na bar yarana a can? Shine kwanciyar hankali da kake fada min? Ko kuma na zuba masa magani ya mutu shine zai nisanta ni da shi? Kullum burinka ka fada min wata bakar magana akan Aminu, kana tunanin dadi na ke ji? Ko kuma kana tunanin hakan zai saka na so ka ne? Hakan be kara min komai ba sai tsanarka Abdallah, ba yau na nake yiwa tanadi ba GOBENA, duk abunda nake ina yi ne saboda yayana da kuma GOBENA....”

Cikin fushi na fada mishi hakan sannan na fice ba tare da sake ce min komai ba. Tun daga yanayin tafiyata za ka gane cewa ina cikin fusata, wannan karon ba kuka ne a zuciyata ba, kuzari ne irin na neman hakki ga wanda aka dannewa shi, ina jin a raina zan iya kwatarwa yata hakkinta, ko da hakan zai zama silar mutuwar aurena. Mai napep na tara na shiga be tsaya da ni ko ina ba sai kofar gida, dari biyu na ciro na bashi ban ko tsaya karbar canji ba na shiga cikin gidan.
Yan matan gidan mu basa nan kasancewar ranar akwai scul masu zuwa aiki sun tafi masu makaranta ma sun tafi kuma a isa dawowo ba, Mama ta kawai na tarar tsakar gidan Inna na can dakinta tana bachi, tana ganin yanayi na ta san ba lafiya ba.

“Halimatu?”

Kusa da ita na zauna,sai na ji wani irin natsuwa da kauna ya shiga zuciyata irin na uwa da ƴa, ban shiga da kuka ba, kuma ban shiga dan nai musu kuka ba amman ganin mahaifiyata sai naji kamar ni ma din karamar yarinya ce a jikin uwarta a take na fara hawaye.

“Lafiya? Lafiya? Miya same ki Halimatu”

Wannan tambayar ce ta fito da Inna daga dakinta tana hamma.

“Lafiya dai?”

Wani irin abu na ji taya zan fada cewar kanen mahaifinta ya lalata? Sai da na ji na samu natsuwar ruhi da ta zuciya sannan na labarta musu komai.

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u”

Shine abunda dukansu suka fada, Inna ta dafe kai, Mama kuma ta daka kirjinta ido a waje tana ta maimaita Hasbiyallahu.

“Wallahi Mama ba zan kyale wannan maganar ba, sai na kai shi kotu sai an kwatar mata hakkinta”

Na fada cikin kuka, sai Mama ta nuna ni da yatsa.

“Kul....! Karki so ma, ki kai kotu? Ki tonawa kanki asiri? So kike a yada ki a redio da tv ke da yarki a buga ku a jaridu? So kike idan yarki tai wayo ta koma ganin laifinki? So kike yarki ta rasa mijin aure? Halima karki yi wannan kuskuren Halima, karki alata rayuwar yarki da taki rayuwar”

Inna ta karba mata.

“Lallai kam duk yadda za a kwato mata hakkinta, zai zubar da mutuncinta ne kawai, wanda be san ayi ma ba yanzu ya sani, suma waenda ake yi ma wa kika taba jin an yankewa wani dogon hukunci? Balle wannan da zai iya tsayawa ya kwaci hakkinsa ya barki nan ke da yarki a cikin mummunar rayuwa, kuma ki jawa kanki da yayanki tsana a gurin dangin mahaifinsu, sannan ki kashe aurenki domin akan wannan abun kin san Aminu zai iya rabuwa da ke daman igiya daya ta rage”

Mama ta gyada kai

“Ko ma be sake ta ba, ai Mahaifiyarsa zata iya saka ya saketa tunda daman can ba sonta take ba”

Hawaye ne suke min zuba irin zubar da bazan iya misaltawa ba, gaba daya kaina na kulle duk wani kuzari na kwatarwa yata hakkinta da nake da shi sai na neme shi na rasa, lankwafar da kai nai ina kallon Mama da abokiyar zamanta Inna hawaye na min zuba na ce

“Mutuwar aurena kuke ji ba abunda akai wa yata ba?”

Inna ce ta dawo gefena ta zauna ta juyo da ni.

“Halimatu, duk wanda zai ce miki be ji zafin abunda akai wa Namra ba to makiyinki ne, sannan kuma duk wanda zai baki shawarar zama a gidan mijinki ki rike yayanki hakika masoyinki ne, Halimatu kanenki mata nawa ne a gidan nan suma neman rabuwa muke da su kai kuma sai ki ce zaki kashe aurenki ki dawo? Kuma kisan auren ma ya zama akan fyaden da akai wa yarki? Ki tonawa kanki asiri? Irin wannan maganar sasantawa ake sai a dauki matakin dan gaba, sirrinki ne wannan ki rike abunki ko yan'uwanki karki ba ri su ji, ki haka rame ki saka shi ciki ki rufe, ko a familyn mijinki karki ba ri kowa ya ji, ki yi hakuri karki ce za ki kai wannan maganar a waje, shi ma Abdallah da yaji ki yi magana da shi ki roke shi ki ce kar ya fadawa kowa kinji?”

Na gyada mata kai ina share hawayena.

“Na ji”

“Na ji”

Na sake maimaitawa ina gyada mata kai ido kuma suna ta yawo a tsakar gidan.

“Na gane”

Na fada ina cizon lisp dina, ni kadai na san abunda nake ji, ni kadai nake jin abunda yake min yawo a zuciya.

“Aminu ya san da maganar?”

“A a be sani ba”

Na amsawa Inna kamar ba ni ba.

“To a tsakaninku za ki yi wannan maganar karki nuna masa ma mun ji, kuma karki nuna masa kin kaita asibiti”

“To”

Na fada ina mikewa tsaye.

“Ina za ki je?”

Inna tace.

“Ai da kin zauna har a jima tunda yace zai kawo miki ita”

“Aa kara dai na je gida”

Na fada ina tafiya. Mama ta mike tsaye ta biyo bayana tana fadin

“Ki rike Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u, kinji? Dan Allah karki fitarta da maganar nan Halimatu”

“To Mama”

Na amsa mata ba tare da na jiyo ba, tafiya na fara yi a unguwarmu hawaye na sauko min ina saurin saka hannu na share, har na isa titi na tari napep mai mutum biyu na shiga nice ta uku, mai napep na tafiya ina hawaye har muka hau babban titi, ni aka fara saukewa sai na fito na saka hannu a jaka na dauko kudin mai Napep na mika masa sannan na tura kofar gidana zan shiga sai na jita a kunne, da alama mai gadin ya rufe daga can ciki har sai da na buga sannan ya bude min na shiga yana min sannu da zuwa. Yadda na bar gidan haka na same shi daman da zan fita ban rufe ba domin na fita hankalina baya jikina. Lokacin da n shigo falon sai na zauna a saman kujera kamar wata bakuwa na saka hannuna na dama cikin na hagu na fashe da wani irin kuka, zuciyata na ayyana min na sha wani abun na mutu kawai na huta.
Hakika na ci kuma kuma kuka ya ci ni domin ya san da zamana a duniya a wannan yau, ina zaune a gurin ina aikin kuka har aka kira sallah azahar idona ya kumbura sosai har bana iya gani da shi sosai, tun ina kukan a zaune saman cushion har ta kai na fado kasa har na kwanta a gurin na mulmula na buga hannayena a kasa. Sai da na ji tsayawar mota sannan na tashi da sauri na leka ta window bata bakar motace da ban wayeta ba, sai dai hango mai kama da Abdallah ya fito cikin motar da shadda nai ruwan kwai yasa ni koma na dauki hijabina an saka na bude kofar falon na fita, ko da na fito ya doso kofar rumgume da Namra a kafadarsa.
A bakin kofa na tsaya shi kuma ya karaso kusa da ni, tun daga yanayin tafiyar da kallon na fahimci ba Abdallah ne ba, domin mutun daya yake min irin wanna kallon wato Abdulhamid domin shi komai nashi a natse yake, saboda kara tantancewa na ce.

“Abdallah....”

“Abdulhamid”

Da sunansa da ya fada yasa na kara tantance shi din ne ta hanyar kallon da nai wa bakinsa a lokacin da yake furta sunansa, domin shi haurensa na gaba ya dan kaure kadan.

“Ya fada maka?”

Ya gyada min kai.

“Naje yin wani abun ne sai yace na biyo da ita zai shiga theater”

Ya mika hannu na karbeta ina hade yawu.

“Ki yi hakuri Halimatu, ko wane bawa da irin kaddararsa, kuma ko wane gidan aure da kalar nasa kalubale, duk wanda ya fada miki aurena da dadi 100% karya yake, akwai kalubale a cikin aure da rayuwa kala kala, dan haka ki yi hakuri, an rubuto haka zai samu Namra so no matter what you did ba zaki iya tare jaddararta ba, rayuwa ko da yaushe tana cike da kalubale so dukan abunda za ki yi karki yi shi dan yau ki yi dan Goben ki, ina rokon Allah ya zama a tare da ke kuma ya baki juriyar daukar wannan kaddarar”

“Amin na gode”

Na juya ina hawaye kamar ba wacce aka tsamo daga kogin kuka na shigo ciki jikina na bani kallona yake har na shigo. A saman kujera na aje ta tana ta bachinta da alama allurar bachi yai mata domin ko motsi bata yi. Wani sabon kuka ne ya zo min tausayinta da nawa ya rufe ni.

“Al-hamdulillah Allah duk abunda kai dai-daine, idan ka ga dama sai ka akashe mu mu duka kuma daidai ne, da baka so ba, da komai be faru ba, kai ka kaddara min auren Aminu, kuma kai ka kaddarar abunda zai faru a yau, komai a cikin ikonsa da yardar ka ne Allah, ya ka zama gatana ka zama tare da ni Allah ya min mafita ka isar ka isar ma yata, Allah ka zaba min tsakanin kwato hakkin yata da igiyar aurena ya Rahamanin Rahim....”

Na karasa cikin wani irin kuka da ban san da zamansa a cikina na sai yau....

________________
Chapter 10 · 0% Book details