← Book details Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 128 OF 136

Sashe 128

Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

“So kike mu je can mu taru mu lalace? No za ki tsaya a nan ki huta kamar yadda Hajiya tace idan sun ba ni gado bayan kin huta zan aiko a dauke ki, kuma zan siyo miki sabon line da zaki rika amfani da shi a nan so that ki kira Mama ki sanar mata mun iso”

Ya karasa tare da kissing dina sannan ya daga ni ya nufi akwatinsa ya rufe ya dauki abubuwan bukata ya saka aljihu,sai kuma ya sake nufo ni da kansa ya dago ni ya rumgume ni ya sake kissing dina sannan ya fita tana dago min hannu. Da kallo na bishi har ya fice ina mamakin hali da dabi'unsa idan aka fada maka Ahmad zai iya zanzarewa yai haka saka rantse da Allah karya ne kace ba zai aikata ba, ni a rayuwata ma ban taba auren namiji marar kunya kamar Ahmad ba, shi komai nasa kirkiri yake kuma da gasken gaskiya to wa ma zai ganshi yace shi aka kawo jinya?
Fitarsa da kamar minti bakwai aka kwankwasa kofar dakin
Tashi nai jikina nata kamshin turarensa na dauki rigata na saka sannan naje na bude, wata farar mace na gani dauke da tray din abinci ta miko min, sai na rufe dakin na juyo na dawo, burger burger and snacks sai drink da safafen kwai, ban kula abinba na nufi bandaki da murmushin daya kasa bari kumatuna, wanka nai sannan nai alwala na fito har lokacin murmushi nake ina jin wani irin shaukin kaunarsa a raina. Haka na bi na rama ko wace sallah sannan bude abunda aka kawo na ci wanda zan iya ci na bi lafiyar gado na kwanta bachi son raina nai ta bachi kamar dan ni kadai akai bachin.

Ban farka ba sai kusan la'asar shima kuma bugun kofar dakin ne ya tashe ni wannan karon wata makar mace ce mai zubin yarbawa ta kawo min tuwo da miyar taushe ga namomi a ciki na yi mamaki sosai ashe a acan ma ana samun irin abincin mu, sai da muka gaisa da ita na karba tana tambayar daga wani garin na zo nan.

“Gasau Zamfara”

Sai ta amsa min da ta san garin sannan tai min sallama ta tafi, duk da ban ji kiran sallah ba dana duba agogona ya nuna min hudu har da wani abu a lokacin, hanzarin shiga bandakin nai na yi alwala ya fito nai sallah sannan na ci abincin na koshi na sha ruwa na sake bin lafiyar gado na kwanta na cigaba da bachina.
Dana auna lokacin magariba yayi sai na tashi nai sallah sannan na jira isha'i itama nai, ina ta jiran Ahmad ya aiko a dauke ni be aiko ba har dare ya soma misalin tara matar nan ta sake kwamkwaso dakina ta kawo min doya da miya, ina ci ina lumshe ido domin doyar ta yi laushi sosai ga dan zaki zaki kana aji kadan wata kila sun saka madara ne dan alamu ya nuna haka yadda doyar tai fari.

  ‘To fa komai a nan banza ne, ko a nigeria da rayuwa take da tsada ai wasu na kan yi doya da madara da miya balle a nan da komai yake banza’

Na fada a raina ina ta kara auna doyar da miyar kifi, bayan na gama cin abincin ina kokarin kwantawa sai na ji an buga kofar, da kuzarina na nufi kofar ya bude, sai nai arba da Hajiya tana sanye da riga da wando sai karuwar rigar sanyin data dora sama kamar ba ita da dankwalin da tai rolling kanta da shi har da su gilas, kasa nai da kaina na gaisheta ta amsa min tana cire madubin idon sannan na bata hanya ta shigo ciki.

“Za mu je da ke can gurin Gwarzo ne”

“Jikin nasa da sauki ko?”

“Da sauki sosai ba su dai ba su dai babu wani result ba amman kana ganinsa ai kasan da sauki kan dan yace ya daina jin komai yanxu, ina jin dai har da addu'ar nan da muka hada masa da rubutu, kin san wani lokacin iska ma suna haka fa”

“Haka ne Hajiya Allah ya kara lafiya”

“Amin ki saka rigar sanyinki mu tafi”

Na mike na dauko rigar sanyin da Ahmad ya saka min na dora saman doguwar rigata sannan na dauki mayafin abayar na rufe kaina muka fita tare da Hajiya. Taxi muka shiga amman kamar wandanda suke a cikin motar gida haka muke a cikin taxin, ni kam bana aikim komai sai kallo ashe garin ya fi kyau da dare ko'ina haske ne ga mayan allunan talla kala kala har da na jaruman india.

“Halimatu?”

Hajiya ta kirani sai ya amsa a hankali na juyo na kalleta.

“Zan tunatar da ke wani abu ban sani ba ko kin sani ko kuma kina kan hanyar sani ne, mijinki yana da kishi sosai, dole sai kin yi hakuri da shi ta wani bangaren kuma ki yi kokarin kare masa mutuncinsa, mijinki yana son girmamawa, ya fada min cewar yana kaunarki kuma yana matukar tausayinki, ki yi kokari ki kare martabarki karki bari kaunarki da tausayinki da ke zuciyarsa ya gushe, sannan kuma mijinki yana da fushi sosai ba duk abu ne yake bata masa rai ba, amman idan ransa ya bace baya sauraren kowa har sai ya sauko, amman kuma baya riko daga fushin nasa ya sauka shikenan za ki ga komai ya wuce, ki yi ta hakuri da shi wani lokacin yana da wuyar mu'amala duk da na lura yana sonki sosai, sai dai kasancewar ki bazawara zai saka ki ga ya miki wasu abubuwan da za ki ga kamar yana kyamarki ko baya son ki, sai dai na san idan kika yi hakuri komai zai wuce, kanwarsa ma na nan Siyama, duk da tana da girma amman bata da hankali da natsuwa na magana da mu'alama wani lokacin, ita ma sai kin yi hakuri da ita, ni kaina da nake mahaifiyarsa sai kin yi hakuri da ni, nima wani lokacin ina da tawa matsalar kin san kuma duk wanda yace zo mu zauna to yace zo mu saba ne dole wata rana sai an samu rashin jituwa a zamantakewa, ina fada miki wannan ne sabod bana fatar wani abu ya hada da Mijinki har ya kai ga kun rabu Allah ya tsare, ina fatar ki zama matarsa ta har abada, matar da mutuwa ce kawai zata raba ku, ina matukar jindadin yadda nake ganinki ke da mijinki, sai nake jin kamar be tana aure ba sai a yanzu ne zan yi suruka”

Na natsu sosai na saurari each and every word da ya fito daga bakinta, a lokacin daya na ji hawaye na cika idona, a yau Hajiya ta yi min abunda wata uwar mijin bata taba min ba, ta nuna min lallai ƴa ta dauke ni.

“Kada Allah ya nuna min ranar da zan yi miki wani abu na bacin rai Hajiya”

“Amin”

Ya miko min line.

“Gashi yace a baki, na sa ne ki yi amfani da shi kamin a samo miki na ki”

Na karbi line ina dubawa sannan na ciro wayata na bude na cire dayan line na saka nasa. Katuwar asibiti ce mai kama da ma'aikata da dare ne amman ko'ina na gurin kamar rana, gata fes an gyara ko'ina kamar ka kwanta. Ni dai bana aikin komai sai rabon ido ina bin Hajiya sai jin nai an kamo hannuna ta baya a hankali da sauri na waigo sai na ganshi cikin rigar asibitin mai blue yai min alama da nai shiru sannan ya saki hannun nawa yai hanzari ya cin ma Hajiyarsa ya sha gabanta.

“Hajiya ga ni nan fa”

Tsaya tai tana masa kallon mamaki.

“Miye haka zaka fito daga dakinka kana a matsayin marar lafiya?”

“To ai na ji sauki Hajiya zaman daki ni kadai ba dadi”

“Allah ya kyauta ni zan koma na kwanta na gaji sosai”

Har ya juya sai ya rumgume ta yana mata godiya.

“Ya kamata kam tunda kika zo baki runtsa ba Allah ya biyaki”

“Amin Allah ya maka albarka ya baka lafiya”

Ya fada tana murmushi sannan nima tai min sallama ta juya daga ni har shi binta mu kai da kallo sai ta fice gaba daya sannan ya sake kamo hannuna ni ko na kalli jama'ar dake kai da kawo a wajen ina jin kunya.

“Ke nan ba ruwan kowa da kowa”

Ya fada yana nuna min wani dake rike da hannun matarsa, sai na dan matsa kusa da shi ina kallonsa uniform din sun masa kyau ya saje a cikinsu kamar wani bature cike da kulawa na ce

“Ya jikin ka?”

“Na ji sauki”

“Amman likitocin ba su fitar da result din ba haka Hajiya tace”

“Sun fito da result mana”

Na kara kallonsa da sauri.

“Da gaske?”

“Eh”

“Me suka ce?”

Sai ya kawo kunnensa kusa da nawa ya rada min.

“Sun ce wai ina da ciki ........”

Ban san lokacin da dariya ta subuce min ba haka na bude baki kamar mahaukaciya na fara dariya babu kakkautawa kowa sai kallona yake, shi ma dariyar yai ya rumgume cike da farinciki ya saka kaina a kirjinsa ya rungume ni tsantsan.

“I love you”
Chapter 128 · 0% Book details