← Book details Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 136

Sashe 80

Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mutumen ya dauko ya miko masa, sai ya karba yana dubawa agogo chewing gum diary na daya daga cikin abubuwan da his late wife Halima take bashi as a gift a idan yai birthday, tun kamin ta aureshi har bayan aurensu. Ji yai ba dadi tunawa da matarsa da yai, da kansa ya duka ya dauko cingon da wani karamin diary dake can gefe ya nufi kujera ya zauna.

“Kasan wa ya min kyautar agogon nan da diary nan da chewing gum din nan?”

“Wallahi ban sani ba ranka ya dade, su da yawa suka shigo kuma ban san waye ba cikinsu dan ba gabana suka aje ba”

“Okay take the rest”

Dorowarsa ya bude ya saka diary da agogon a ciki sannan ya bude chewing gum ya kai bakinsa. He can't remember when last na ci chewing gum sai yau hakan yasa ya ji ya masa tauri, or maybe saboda wannan karami ne ba irin mai tsada da ya saba ci ba. Haka nan kawai Halima ta fado masa a rai, did she deserved to work a kamfaninsa? Bayan dazu dazun nan ma ta gama zaginsa, ashe kuma ta san a kamfaninsa take aiko amman ta ci masa mutunci? Ko da yake shi ya kadeta kuma be tsaya ya dubata ba yai tafiyarsa, amman duk da haka ai be kamata tai masa rashin mutumci ba. Laptop dinsa ya janyo ya bude ya fara duba wasu abubuwan.
After like 40 minutes Yunus ya shigo masa da wasu takardu, after ya gama masa bayani yake tambayarsa.

“So ka biye shiriritar Siyama kasa am bata min office da gift ko?”

Yunus yayi dariya.

At least ai an saka ka farinciki, tunda birthday ka ne, ban saka kowa yayi ba amman dai na saka sabbin ma'aikatan mu ne su baka abunda ya samu”

“Nope ka san ba komai ke burge ni ba”

Har ya dauke kai sai kuma ya juyo da sauri.

“Sabbin ma'aikata? Har da wannan farar mata tana nan ciki....”

“Wace farar mata?”

“Wacce na saka aka canjawa position dazun baka nan?”

“Yeah amman na samu labari, har da ita dukansu na saka ai ita ta aje maka chewing gum da agogo”

Jimmm Ahmad yai.

“O.... Okay....”

Ta fada yana daina tauna chewing gum tare da yatsuna fuska...

I feel like na karo wani page anjima da dare 😝😝😝 amman ga masu comments kadai 🙄🙌
7/21/21, 10:46 PM - Buhainat: *GOBE NA...*

By Khadeeja Candy

4️⃣1️⃣

HALIMATU POV.

Ba laifi sai na ji kamar inda aka dawo da ni a yanzu ya fi na farkon dadin zama, domin a can rubuce rubuce ne, a nan kuwa kula da masu shigowa ne kawai gashi sai fira muke tare da sauran ma'aikatan, daya mace ce wacce ta kasance kabila ce sai ni ta biyi sai maza uku, ni kadai ce ba ni da uniform a cikinsu, domin ni tufafin gida ne a jikina.
   Ban yi awa daya a gurin ba aka kawo min wando da riga na kamfanin, irin na sauran ma'aikatan da suke gurin mai dauke da sunan kamfanin, tare da wani dan abu da ake sakawa a wuya wanda ke dauke da sunana sai kuma gurin saka hoto, har ga Allah bana son saka kananan kaya abu ga mai dan jiki balle ni da Allah ya horewa abun duk yadda zan so boyewaba boyuwa zai yi ba, na saka skirt ma suka bayyana balle kuma wando, na dade rike da tufafin ina da tunaninsa sakawa ko akasin hakan, sai dai na san idan har na ce ba zan saka ba zasu iya korata. Ba ni da wani zabi da ya wuce na saka din ai idan ina a reception din babu mai ganina tunda katon tebur din ya tare ni sai dai idan zan tashi kuma idan zan tashi zan iya canja tufafi ko kuma na saka mayafi. Bandakin kamfani na nufa na canja tufafi sannan na saka hijab dina na fito reception din a lokacin da na tsaya a inda ba a ganina sai na cire Hijab din na cigaba da aikina hankalina a kwance. Wani abun burgewa ashe na wadanda suke reception din har da abincin ake kawo musu da ruwa tsabanin da da sai dai yunwa da kashe ni.
   Mu uku muka je cin abincin tare da blessed da Walid, muna cikin cin abincin yake dauko mana labarin sabon kamfanin da za ake tunanin budewa a wata jihar sai dai suna tantamar garin da za a bude, mun dade muna tattaunawar har nake bayarda shawarar da ace za su yarda da sun bude a Kano domin can ne cijiyar Kasuwanci, ko kuma Jos duba da yanayin garin Walid kuma yace Abuja, a haka dai muka gama cin abincin muka tashi muka koma gurin aikinmu su biyun da basu ci ba suka koma ciki dan cin abincin.
  Ina tsaye a gurin sai ga wasu fararen mutune sun shigo, da fari dai na dauka turawa ne, a take hankalina ya koma gurinsu tun kan su karaso nake ta kallonsu cike da burge domin kusan sai nace ban taba ganin turawa a zahiri ba sai yau, sai dai na lura sauran abokan aikina ba kamar ni suke ba, wata kila sun saba ganin turawa ba kamar ni ba da na zama bakwaya har murmushi nake musu kamin su karaso.
  Ko miye abun burge a farar fatar ma oho sai kace ni din ba fara bace ko da yke nawa farin mai kyau ne, domin na su ba shi da kyau kallo farin yayi yawa har wani kashe ido yake.
  Suna isowa sa abokin aikinki ya tarebe su da yaren turanci su kuma suka masa magana da faransanci hakan yasa na fahimci cewar faransawa ne ba turawa ba kamar yadda nake zato. Hakan yasa na yi kaudin yin musu harbun da tambayar abunda suke bukata a dan abunda na iya na yaren faransanci. A take suka mayarda min da amsa, aiko nan dade ya kusa kashe ni wai ni na magana da wanda ba yare ba kuma ba yan kasa ta ba. Da suka fada min wanda suke bukatar gani wato shugaban kamfanin sai na fadawa Walid shi kuma ya nuna min yadda zan yi na kira na sanar idan bukatar irin haka ta taso, kamin na danna number wanda yace min shi ake fara kira a sanarwa, sai ga Yunus din ya fito daga cikin kamfanin ya tare su da far'arsa har ya basu hannu suka gaisa, sai dai shima na lura be iya faransanci ba kamar dai sauran abokan aikina. Godiya suka min da yarensu na mayar musu da godiyar nima sannan suka bi Yunus zuwa ciki. After like 15 minutes ya fito yana tambayar wai na iya faransanci ne sosai.

“Gaskiya ba sosai ba gaisuwa kawai na iya sai dan abunda ba a rasa ba, ban iya sosai ba”

“Amman za ki iya kula da su kamin mai fassara mana ya iso?”

“Yes”

“Good zo muje”

Sai da na dauki gyalena na yafa sannan na bi bayanshi, sai dai a yanayin yadda yake tafiya ne yasa nai saurin cin masa duk kuwa da kasancewar ina tafe ina dingishi ne sai muka jera a tare muna tafiya a tare, ba laifi yana da sakin fuska da son magana ba kamar mugun gogan ba, a nan yake tambayar inda na iya yaren faransanci, na fada masa tun a secondary school na yaren yaren sosai lokacin da muna can sai dai shiga FUG yasa na manta da wani abu, ga kuma abubuwa na rayuwa sai na watsar da abun. Sai a lokacin da zamu shiga cikin office din ya bukaci na cire mayafin nawa, hakan yasa ni jin babu dadi wanda har ya bayyana a fuskata.

“No ba wani dadewa za ki yi ba, za ki yi tambaye abunda suke bukata ne kawai sai kuma fara gabatar musu da abunda zan nuna miki kamin mai aikinmu ya iso”

“Ba fa komai na iya a faransanci ba, ba zan iya wani dogon bayani sosai ba”

“I know saboda kar mu barsu shiru ne, tun mun zama kurame mu da su”

Ban musa ba na cire Hijab din kamar yadda ya bukata, daman can dankwalin atamfa ne a kai, ga farar riga da bakin wando na kamfani sai ya bada wani kala na dabam, na yi zaton su kadai ne a dakin taron, sai na tarar har da Angry Bird din ya wani shakimce a saman kujera yana ganina ya wani hade rai. Ni kuma na tsaya bakin kofa har sai da Yunus din yai min iso.
Na shiga ciki na tambaye su abunda suke bukata na sha suka bukaci ruwa kawai, shi ma kuma da aka kawo ba su sha ba, abunka da marar yarda, haka nan dai cikin rashin iyawa na rika dan nuna musu abubuwan da Yunus ya nuna min, wanda suke a katon wani abu mai kamar tv kuma shi ba tv ba, da removed din hannuna na rika nuna musu kalolin zinarin da suke a ciki, domin ya fada min abun nan ja na jikin remote din kawai zan taba su za su rika canjawa da kansu.

Muna haka sai ga mai fassarar ya shigo, na yi zaton idan ya shigo umarni za a bani na fice sai gashi ya saka ni cigaba da danna remote din shi kuma yana musu bayani da halshen faransancin, ina jin wani abu wani abun kuma bana gane komai, wani abun zai fada ma Ahmad da Yunus abunda suka ce ne sannan ya cigaba da yi musu bayanin, har akai aka gama Ahmad be ce komai ba, sai aikin tsutsar minti yake, ni kuma ban ma sake kallon inda yake ba. Sai da suka gaisa da shi sannan suka fice tare da mai fassarar, hakan yasa na aje remote din ina jiran a bani umarnin ficewa, amman Yunus din sai karin bayani yake ma Ahmad din. Ni kuwa hankali gaba daya yana gida ga garin ya hada bakin hadari kamar yadda nake hange ta cikin gilashin da ke gafenmu.

“Ranka ya dade zan iya tafiya”

Na fada ina kallon Yunus din a tare suka kalleni daga Ahmad din har Yunus ne.

“Sorry yau mun baki aiki da ba naki ba”

“Babu komai”

Har na aje remote din ina kokarin juyawa sai yace.
Chapter 80 · 0% Book details