← Book details Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 136

Sashe 77

Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da gudu ta nufi bandakin da ke tsakar gidamu tai fitsari sannan ta dawo ta zauna tana zaro ido.

“Dan Allah ki ce kin yafe masa mana, Wallahi zai iya fusata ya zo ya halbemu, kin ga dai ni ko dan karatun ban gama ba, balle na ci moriyarsa, ga yaranki kanana, Baba Lafiya ma bata isheshi ba, dan Allah ki yafe masa kar ya zo ya halbe mu dan Allah kema zai iya halbeki Wallahi...”

Da farko dai na dauki maganarta serious daga karshe kuma sai ta bani dariya domin na lura tsoro ya gama cika mata ciki, ina cikin dariya Baba ya shigo bakinsa a haushe yana da far'a.

“Kun ji abun Allah yanzu fa sallamar da kai min ina fita wani ya bani 100k kyauta”

Ni da Hafiza muka hada ido kamin su Inna da Mama su fito daga dakin da murnarsu, gaba dayan gidan sai ya kaure da murna abunka da talaka mai neman na yau da gobe ya samu kyautar 100k a rana daya ina bakin yan gidanmu zai rufu, ni kaina na nuna murna kuma na jidadi ganin yadda Mama da Baba da Inna suke ta murna suna masa addu'a, sai dai ni na san mutum daya zai iya wannan abun wato Abraham.

“Amman Baba kai kadai ya bawa kyautar?”

“Gaskiya bani kadai ba ina tsaye da Malam Isuhu ya min sallama ya miko min 100k shi kuma Isuhu ya ba shi 5k”

“Baba yaro ne?”

“Aa dattijo ne amman ba zai kaini tsufa ba gaskiya, yana cikin wata bakar mota mai kyau kana ganinta ka san mai kudi ne sosai, shi dai mai ja masa motar ne matashi”

“Uhmm”

Na fada ina rafka uban tagumi tare da kallon Inna da ke fadi.

“Allah mai iko sai ka ji wani yayi kyautar abu kamar banza yanzu har dubu dari ka bayar kyauta, wasu Allah yai musu arziki”

Mama ta taya ta.

“Ina jin dai zakka ce, ko kuma irin masu kudin nan da ke bin gidajem talakawa suna ba su kudi”

“Ko dai minene mun gode Allah shi kuma Allah ya saka masa da alheri, daman an kwana biyu ba mu girki da nama ba gobe da safe idan Allah ya kai mu sai a samu mana nama mu ci”

Cewar Baba, sai duk suka dariya ban da ni da ke ta wani tunanin na dabam. Har aka isha'i babu abunda nake sai tunanin yadda zan bullowa lamarin nan, wata zuciyar na fada min cewar na sanar da police kawai n huta ko kuma na sanar dasu Mama idan kuma nai hakan hankalinsu zai tashi, idan kuma na kyale shi abun nan kara gaba zai yi.

Misalin takwas da rabi yaro ya shigo wai an sallama da ni ba waje, da farko na dauka Aminu ne domin shi ma yana min hakan ganin bana daukar wayarsa sai kawai ya aiko kirana kai tsaye sai idan na fita na ganshi, sai dai mafi akari Abraham ya fi min haka, domin shi be tana kirana a waya ba ma, be tana ce min na bashi number ta ba.
Aiko kamar jira nake na zari hijabi na saka na bi bayan yaron da ya aiko kirana, ko da n fita yana can nesa da gidanmu kamar yadda ya saba tsayawa, hango ni yasa shi fitowa daga motar ya rike gambun motar yana ta kallona har n karaso.

“Me kake so? Kana ta bibiyar rayuwata, na fada ka fita daga hanyata, bana kaunar ganinka Abraham kai ne silar lalacewar aurena ba baka aikata abunda ka aikata min ba da har yanzu in zaune tare da mijina... To me kake nema a yanzu?”

“Yafiyarki mana, na rasa gane wace irin mace ce Halimatu, me zan yi ki yafe min? Fyaden da nai miki kuskure ne, na yarda na lalata miki rayuwar aure, amman haka ba ya kara fito da kalar mijinki ne kawai, na nuna miki cewar ba zai iya zama da ke idan wani abun ya same ki ba, and I'm here for you, na ji na aikata laifi amman yafiyarki nake nema, and i promise you zan dauki nauyin yaranki da iyayenki da kanenki, zan inganta rayuwarki”

“Da kudin haram? Kudin da kuke tare mutane masu hakki ku karbe musu abu? To bana so kuma karka sake bawa mahaifin kudinka na haram”

“Su waye muke tarewa muna kwace musu hakki? Halima har addinina n ce zan bari na shiga na ki saboda kawai ina kaunarki amman kin ki aminta why? Daman haka musulmai kuke?”

“Karka kuskura ka kasa zancen addinina a ciki maganarka, kuma tirr da kai ni ba zan auri dan fashi ba dan fashin ma wanda ya keta min haddi”

Ya gyara tsayuwarsa yana kallon.

“Waya ce miki ni dan fashi ne?”

“Miya hada ka da bindiga a wacan daren?”

“Saboda kawai n rike bindiga sai ya nuna ni dan fashi ne, a yanzu ma ina da ita a mota, ke dai ba kisan komai a game da ni ba, ba ki san waye ni ba, iyakar abunda kika sani na miki fyade sai sunana sai kuma bibiyarki da neman yafiyarki da nake”

“Idan na yafe maka zaka daina kula ni zaka daina bibiyata zaka daina zuwa kofar gidan nan zaka daina bibiyar yarana?”

“No ai yafen min da za ki yi shine ki aure ni, ki haifa min yara.....”

Da sauri na rumtse idona ji nai kamar ace akwai wani makami a kusa da ni na daba masa a kirji ya mutu a gurin, saboda zafin da maganarsa tai min, taya mutun zai keta min haddi da aurena kuma yana kafiri ina yar musulma sannan yanzu ya dawo yana min maganar aure har da haifar masa yara, saboda kawai ni Halimatu ai komai nawa dabam ne.... Ji nai an haska fuskata hakan yasa na bude ido ashe wayarsa ce ya haska min a fuska ganin ina hawaye yasa shi ce min.

“I'm sorry ban zo nan dan na saka ki kuka ba, zan tafi see you at Children's Day”

Yana fadar hakan ya koma cikin motarsa yai mata key ya bar ni a gurin tsaye ina hawaye.

“Ba zan je ba, saboda kai ka siyo min ticket din”

Na furta a fili ina ayyanawa a raina cewar ba zanje din ba....

_____________

Wai ashe Abraham yana da team 🤐
Who can guess what will happen next? 🤗

Ni dai ina Team Aminu 😝😝😝
7/21/21, 10:46 PM - Buhainat: *GOBE NA...*

By Khadeeja Candy

4️⃣0️⃣

Hakan nan yau yake sha'awar zuwa gurin aiki da wuri, daman kuma ya tashi ya ji jikinsa sai a hankali so yana bukatar yai aiki da wuri ya dawo gida if possible. And he like to wear a suit today like always sai dai wani lokacin yana saka shadda dan yafi jinsa more comfortable fiye da suit.
  Bayan ya gama shiryawa ya shigo bangaren Hajiyarsa still ya same ta tana aikin hada masa breakfast sai dai yau ba ita kadai ba har da Siyama. As he already knows siyama bata tashi da wuri sai idan makaranta zata je, amman ga a kitchen tare da Hajiyarsa da mai aikinsu har ma da cousin dinsa Khadija wacce kwararriyar banker baker ce. 

“Yau me kuka hadawa haka ne?”

Da sauri dukansu suka juya suka kalleshi domin ba su san da zuwansa ba sai ganinsa da kai a kofar kitchen yana ta kamshin turare.

“Amman Bro you wake early”

Cewar Siyama tana nufo inda yake. Agogon hannunsa ya duba wanda ya nuna masa bakwai da yan mintuna.

“Yeah ina son naje aiki da wuri ne”

“Oh bro i wanted to surprise you.....”

Ta fada tana bata fuska, sai Khadija ta tari numfashinta tana murmushi.

“We can still surprised him dear... ”

Ya kalli Khadija da fuskar rashin fahimta. Sai ta jango masa kujerar kitchen din ta aje bayansa.

“Dan zauna”

Be zauna ba be kuma nuna alamar zai zauna din ba balle har ya furta wani abu. Siyama know him well, he is no nonsense at all, hakan yasa ta hade hannayenta.

“Pls”

Sai da ya kalli Hajiyarsa wace ita ma tai masa alama da ya zauna din sannan ya zauna yana binsu da kallo. Da gudu Khadija da Siyama suka fita daga kitchen din, like 6 minutes suka dawo sai Hajiya ya fita.

“Close your eyes pls”

Be musa ba tunda Siyama ce tai masa maganar, a take ya rufe idon sai ta kama hannunsa yana masa jagora a hankali har suka fita daga kitchen din, gaban dinning area ta nufa shi sannan ta saki hannunsa.

“Now open your eyes....”

A hankali ya bude idon, by surprise yai arba da katon birthday cake mai hotonsa.

“Wow”

Ya furta yana kallon mahaifiyarsa da ke Murmushi kamin ya rumgumi Siyama wacce ke ce masa happy birthday.

“Thank you Blood, Thank you Mom, thanks Sis”

Ya fadawa Siyama Hajiya and Khadija wacce tai masa respond da murmushi.

“So duk kun san yau birthday na kenan, ni na manta sam”

“Taya za ayi na manta ranar da na maifi Ahmad Gwarzo...”

Cewar Hajiya tana murmushi, sai yai murmushi ya kai hannunsa ya debi cake din ya kaiwa Hajiya a baki.

“I love you Hajiya ta”

One after the other ya bisu ya saka musu cake din a baki har Khadija, sannan suma suka ba shi, daga bisani Siyama ta ciko hannunta da cake din zata shafa masa sai yai saurin rike mata hannu ya murda har sai da ta kai kasa tana ihu.

“Wayyo Hajiya....”

“Gwarzo karka kare min ya”

“Hajiya ba zan bari ta bata min tufafi ba today is special day for me...”

Sai duk suka saka dariya har ita Siyamar sannan ya sake ta ya dauki tissue ya goge hannunsa.

“Yau din nan ko? I very very special day for us, i call your friend on phone and i told him ya saka kowa yai surprise dinka da wani abu each and every person a kamfaninka, so karkaje ka dinga musu fada ni na saka su”

“Kina da hankali Siyama?”

“No sam sam Hankali wala gare ni a yau, la la la and in the laila akwai celebration... ”

Ta fada tana rawa.

“Hajiya yau yarki bata da hankali”
Chapter 77 · 0% Book details