← Book details Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 136

Sashe 33

Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Gobe zamu je mu gaishe da Hajiya,ya kamata muje cikin daren nan mu siya abunda za mu rika mata domin da safe zan aje ki can idan zan wuce gurin aiki kuma ba lallai ace lokacin masu super market sun bude ba”

Tashi nai na shiga dakina na canja tufafi jikina a tsakanin shiryawa da na shi be wuce minti ashiri ba ya yan kai sannan mu ka fito, da kansa ya bude min motar na shiga sannan ya shiga mazauninsa ya tashi motar, da mu kai bakin gate sai ya fita ya bude mana gate din ya fita da motar sai kuma ya rufe ta muka kama hanyar jifatu.
Har muka isa zuciyata raya min take na fada masa gaskiya, ko ba komai ai shi mijina ne be kamata na boye masa ba, abunda ban sani ba ashe shi fira yake ta min ban lura ba sai da ya kira sunana.

“Na'am”

Na amsa da sauri a daidai lokacin da kiransa ya dawo da ni hayyacina.

“Me kike tunani?”

“Komai bana na tunanin komai”

Da hannu ya nuna min alamar na bude motar na fita yana ta kallon yanayi kamar mai tuhumar wani abu, a hankali na bude motar na fito kamar wata marar lafiya, a tare muka jera muna tafiya daf da za mu shiga cikin gurin wani mutume mai kama da mahaukaci ya miko mana hannu alamar mu ba shi, da na kalleshi da kyau sai na nemi damuwata ta da tunani na rasa, hankalina ya tashi har na kusan rikicewa. Kabir ne Kabir abokin aikina Kabir din da ya kamu da lalurar saboda ni ashe da gaske abun ya taba kwakwalwarsa, da gaske ya haukace. Ni yake mikowa hannuna yana ta kallona sai kuma ya juya yana kallon Abdulhamid ya mika masa hannu, Abdulhamid ya saka hannunsa aljihu ya ciro dari biyu ya mika masa, sai ya juya ya fara tafiya yana dingishi alamar kafar tasa akwai ciwo ko rauni a gurin.

“Haima kuka kike yi?”

A rikice na kalli Abdulhamid ba dan na san abunda ya fada ba sai dan sunana da na ji ya ambata.

“Kabirr...... ”

Na ambaci sunansa ina maida numfashi.

“Kin san shi ne?”

Wannan karo na ji abunda ya fada hakan yasa nai saurin gyada masa kai na juya da sauri fuskanci kofar shiga Jifatu din.

“Kuka fa kike”

Da na taba fuskata sai na ji hawaye masu zafi suna sauko min, da sauri na share hawayena na karasa ciki sai ya biyo bayana, har na yi zaben abunda za mu siyawa Hajiya ban daina hawaye ba, babu yadda ban yi ba dan na tsaida hawayena amman abu ya ci tura. Na riga shi dawowa cikin motar na zauna kamin ya biya kudin siyayyar, a front na zauna ina ta kallon Kabir da ke mikawa masu zuwa gurin hannu idan aka ba shi sai ya koma ya zauna, idan ya hango wani ya sake tasowa, kallonsa be haifa min da komai ba sai bakinciki da kuka mai tsanani? Rayuwarsa da baya ta dawo min, ina ta ganin murmushinsa da kulawarsa a kaina. Mutumen da ke da son kwaliya ga tsafta yau shine a wannan halin? Ina matarsa? Ina mahaifiyarsa? Ina danginsa? Miyasa suka bar shi haka babu kulawa?

Hango Abdulhamid tafe yasa na share hawayena na yi saurin gyara fuskata, gidan baya ya bude ya saka ledar sannan ya dawo mazauninsa ya tashi motar, har muka isa gida be ce min komai ba yana farkin na bude motar na fita ina shiga falo wani sabon kuka yai min lale marhabun hakan yasa na nufi kitchen da sauri na wanke fuskata.

“Ba zan hana zuciyarki tausayin wani ba, amman yana da kyau idan za ki ji tausayinsa ki yi a bayan idona ba gaban idona ba, na ji zafi sosai Halima ace hawayen nan saboda wani namijin kike zubar da su ba ni ba, abunda ba ki taba sani ba shine ina da tsananin kishi, ina kishin ace matata ta kula wani ba ni ba, I'm sorry to say yaran nan ma idan na tuna ba da ni kika haife su ba ina jin babu dadi, saboda ina tsananin sonki kuma ina kishinki, na san idan nai shiru zan cutu ne kuma na kwari kaina ke kuma kin kasa gane haka....”

Magana yake min a yayinda yake tsaye a kofar kitchen din yana kallon bayana ni kuma ina kallon windows din kitchen wasu sabbin hawayena na sauko min. Ban yarda na jiyo ba har sai da na ji motsi ficewarsa daga kitchen din, sannan na dawo dakina na shiga bandaki nai kuka mai isa har sai da na ji amai ya taso min sannan na sassautawa kaina, sai dai ban samu salama ba har sai da nai aman sannan na hada ruwan nai wanka na shirya cikin kayan bachi na hau gadona na kwanta, a yanayin yadda ya nuna min bacin ransa ban yi zaton zai zo dakina ba, domin haka Aminu yake min a duk lokacin da muka samu tsabani, sai dai a mamakina sai ga Abdulhamid ya shigo dakina ya kwanta bayana yana sumbatata ya saka ni a kirjinsa ya rumgume ni sosai.

“I Love you”

Shine abunda na san ya rada min a kunne kamin bachi yai gaba da shi, ni kan har kusan biyu saura na dare ban yi bachi ba, babu komai a duniyata sai tunani da damuwa. Kiran sallah farko muka farka shi ya tafi masallaci ni kuma na nai sallah a gida, Misalin takwas muka karya sannan na shiga nai wanka shi ma ya shirya muka fito da zimmar zai aje ni gidan Hajiya ya wuce gurin aiki, ya lura da yadda na saka sakewa tun jiya damuwa karara a fuskata sai dai be min magana ba har muka isa. Tare muka shiga cikin falon sai muka same Hajiya zaune a kujera daya ita da Abdallah, tun da na kalleshi sau daya ban sake kallon inda yake ba har na zauna sai dai jikina yana ta ba ni cewar idonsa na kaina, ni kam na manta when last na saka Abdallah a idona ma dan ni har na manta da shi a duniyata.

“Hajiya ina kwana”

Ya mika mata gaisuwa ina dan risinawa, sai tai kamar bata ji ba ta maida hankalinta gurin Abdulhamid da ke magana da Abdallah.

“Lafiya kake karyawa a nan”

“As you know ko Madam tana nan ina karyawa a nan ai balle yanzu da tai tafiya”

Yadda Abdallah ya amsawa dan'uwansa sai da abun ya ban mamaki domin babu alamar shauki ko wani far'a a tare da shi.

“Matarsa bata nan taje Kaduna gurin biki”

Hajiya ta amsawa Abdulhamid, sannan ta kalli inda nake ta dauke kai kamar ta ga wata makiyiyarta.

“Hajiya ina kwana”

Na sake miki mata gaisuwa,wannan karon ta amsa amman sai da ta dauki lokaci, ban damu ba daman tun da na auri Abdulhamid na lura da Hajiya kamar bata na'am da ni, ledar siyayyar da muka mata na tura mata gabanta sai kawai ta kalli ledar ta mike tsaye ta nufi dakinta tana fadin.

“Kai ma ka karya ko na kawo maka abun kari”

“A a ni kam sai da muka ci abinci muka fito gida”

Ya fada yana kallona da murmushi a fuskarsa, ni ma murmushi nai masa kamin na maida dubana gurin roben da ke saman glass table din da Abdallah ya aje mug din hannunsa. Farin zobe ne mai kamar na silver da alphabet din A a ciki, alphabet din baka kamar na wacan zoben da na gani a daren bakinciki.

“Kin ji sai na dawo zan zo na dauke ki”

Abdulhamid ya fada min haka bayan ya mike tsaye, kai na gyada masa sai ya shiga dakin Hajiya yai mata sallama ya fice, kamar fitarsa na ke jira nai saurin kai hannu na dauki zoben da ke aje, da sauri Abdallah ya miko hannunsa fuska a hade ya rike hannuna.

“Ba ni zobena”

“A ina ka same shi?”

Nima na tambaya rai a hade cike da tsananin mamaki, a maimakon ya amsa min sai kawai ya watsa min wani kallo da ban san ma'anarsa ba, tunani be tunatar da ni cewar a falon Hajiya muke ba, ban kawo a raina cewar Abdulhamid zai iya dawowa ba, ban damuwa da rikon hannu da karfi da Abdallah yai ba saboda hankalina ya dauku akan zoben da son sanin dalilinsa, daman ya san za mu zo da har yasa ya cire zoben ya aje a inda zan gani ko dai na yi gamda da katar din ganin ne? Motsi muka ji daga bakin kofar shigowa falon alamar za a shigo hakan yasa yai saurin sakin hannuna ya sake miko min dayan hannunsa.

“Ba ni na ce”

Ya fada a tsawace wanda hakan yai daidai da shigowar Abdulhamid a falon.

“Minene?”

Ya fada yana kallon yanayi da nasa. Da sauri na saki zoben ya fadi kasa shi kuma ya mike tsaye ya kai hannu ya dauka ya fice zuwa dakin Hajiya, a sannan Abdulhamid ya karasa kusa da ni ya miko min wayata yana kallon fuskata.

“Ga wayarki”

Ya miko min yana aje mumfashi a hankali sannan ya juya ba tare da ya sake ce min komai ba ya fice, dafe kaina nai gabana na mugun faduwa, faduwar da ba ban san ta Minenen ta fargabar kar ya zargi wani abu ko kuwa ta fargabar ganinmu ko kuma ta fargabar zoben da na gani a hannun Abdallah?

AHMAD POV.

Kansa a kasa yake sauraren Momy, idonsa sun rikide gaba daya saboda bacin rai, ta ya yanzu Momy za ta zo masa da wannan maganar? Wani irin magana ce wannan wacce hankali ba zai dauka ba, taya zata hana shi auren wannan saboda kawai ita Shuwa ce?

“Wallahi ance mallake miji suke ni sam ban yarda ka aureta ba ka nemo mata”

Dagowa yai ya kalleta cikin tsananin bacin rai da damuwa.

“Amman tun farko da na fada miki family yarinyar na fada miki wacece ita ya kamata ki hana ni ba sai yanzu da yar mutane ya kamu da so na ba, har na gaisa da mahaifita sun yi magana sun ce na turo magabata sannan ki kawo wannan maganar haba Momy wannan na reason ba ne.... ”
Chapter 33 · 0% Book details