← Book details Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 136

Sashe 26

Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rasa nai abunda zan sake ce masa sai na bata fuska kamar mai shirin yin kuka.

“Miya hana su karatu da wuri?”

Mutumen ya tsomo min baki a magana yana kallon yarana.

“Canja musu za ayi”

Na bashi amsa kamar an min dole.

“Saboda mi za a canja musu scul din? Kuma kika kawo su a wannan makarantar”

“Ra'ayi”

Na fada ina mikewa tsaye cike da fusata sai a lokacin ya kalleni domin duk maganar da yake su yake kallo ba ni ba.

“Ya ana magana za ki tashi kuma kika sani ko a taimaka miki... ”

“Bayan ka ce babu a taimakon da zaka iya yi mana? Sai ka ce mu ba kudin za mu biya ba ai kyauta na roka ba, kuma ba wannan ce kawai makaranta ba”

Principal din ya fada, ni kuma na bashi amsa a fusace domin har ga Allah na ji haushi wato saboda ya ga alamar mu ba masu arziki ne kamar wannan ba shine zai wani ce a tainaka mana tun da ya saka ba ki bayan farko ya fada mana ba wani taimako, irin wannan makarantar ma ko yaran ka sun yi karatu aciki wulakanta ka za ayi da yaran. Har principal din ya bude baki yai magana sai mutumen ya daga masa hannu yana lasa wayar da ta zame masa dole. Ni kuma na sako yarana a gaba muka baro makarantar cike da dana sanin zuwan da nai.
7/20/21, 8:30 AM - Buhainat: *GOBE NA...*
_My Tomorrow_

By Khadeeja Candy

1️⃣5️⃣

Sai da na sauke su gida sannan na wuce gurin aikina cikin damuwa, damuwar rashin karatunsu da kuma na abunda ya faru a makarantar yau.
Na yi mamakin ganin wani a kujerarta mamakin ba dan kankane ba sai kuma tsoro ya biyo na soma rayawa a zuciyata ko sun kore ni ne kuma? Ko kuma wani abun ne? Ban cewa Emanuel komai ba balle kuma bakon mutumen kai tsaye na nufi office din oga Dahiru.
Sai na fara knocked bayan ya ba ni izinin shiga na tura na shiga. Gaisuwa na fara mika masa a maimakon ya amsa min sai ya kai hannu ya dauki wayarsa ya shiga waya da wanda na ke zaton abokinsa ne domin yanayin firar da yake ya nuna haka, ina tsaye a gurin har yai wayar ya gama sannan ya kalleni da murmushi a fuskarsa kamar zai ce wani abu sai kuma ya mike tsaye ya zago inda na ke ua miko min hannu.

“Congratulations kin hau matsayin Kabeer a yanzu kin samu karin mukami....”

A tsakanin miko min hannunsa da yai da kuma sanarwar karin girman sai na rasa wanne yafi ba ni mamaki, miyasa za a kara min girma kai tsaye bayan akwai waenda suka fini cancantar hawa kujerar Kabir? Da wata manufa yai ko kuwa dai rabo ne ya koka kamar yadda na kowa yake kokawa? Ban ankaro ba na ji na rika hannun nawa yana shaking.

“Congrats Dear”

“Kabir fa?”

Na tambaya bayan na yi saurin cire hannuna daga na shi, ina ta fargabar kar ace min ya mutu. Sai ya juya ya koma kujerarsa ya zauna ni kuma na bi shi da kallo.

“Kabir ya samu tabin hankali, abun nan ya taba shi har cikin kwakwalwarsa, a yadda suka rubuto mana ma an tafi tashi lagos yanzu haka, bayan an bar Kaduna da shi”

Tausayinsa ya kamani ni a lokacin da yake can yana rashin lafiya yana fama da kanshi a lokacin aka dauki position dinsa na aiki a aka ba ni, da ace ba ni ba ce da murna zan hau shi yayinda shi yake can hana fama da kansa.

“Ku kuka cire shi daga aikin?”

“Dole ne wannan ai Halimatu saboda kamfani ne ba aikin gobnati ba, ba za mu iya jiransa har ranar da ya warke ba, ko da ma ya warke ba za mu iya sake daukarsa aiki ba”

Babu tantana idan na sake bude bakina kuka ne zai fito, hakan yasa ban sake ce masa komai ba na juyo kamar kazar da kwai ya fashewa na fito daga office din.

“Halimatu....”

Na ji kiransa bayan an fito daga office din, juyawa nai na koma cikin office din ba tare da na amsa ba, sai ya miko miko min wata takardar da ke tabbatar da zamana a position din, karasa nai cikin rashin kwarin guiwa na karba na fito. Na sake dawowa office din mu cike da damuwa ina zaunawa a kujerar da Kabir yake sai hawaye suka ce min sallamu alaikum, babu wani dan 'adam da za ayi ma bushara da karin girma a duniyar ya ji babu dadi sai ni da tawa kaddarar ta zo a haka, ba san abunda ya hanani sukuni da farinciki ba, na kasa samun jindadi da annashuwa, tun ina hawaye kadai har na koma yin kuka mai sauti, Emanuel ne yai ta ba ni hakuri amman sai na ji kamar yana horara min wutar kukan a zuciyata, bayan ko wace dakika biyar fuskar Kabir ce take min gizo, rayuwar da mukai a baya idan zai miko min wata takardar ko ya karba ko ya min wata maganar a cikin har da yawan murmushin da yake min, ina ta jin sautin muryarsa.
Bar bar gurin aikin ba sai da na rubuta takardar resigned ba tare da neman shawarar kowa ba, a lokacin da na aje takadar a office din oga Dahiru baya ciki hakan ya bani damar ficewa ba tare da shan kai ba. Na isa gida da kumburarrin idanuwa saboda kukan da na yi a office, duk wanda ya kalleni ya san bana cikin walwala da nishadi, daga Babana har Mama ba su farinciki da aje aikin da nai ba, ba su fada min ba amman na gani a fuskarsu da kuma yanayin maganarsu. Allah yasa hakan shi ya fi alheri shine abunda suka fada min, ni kuma na amsa da min kamin na taso na baro musu dakin na dawo dakin da nake kwana cikin damuwa.

Kwana biyu da faruwar hakan Abdulhamid ya turo magabatansa aka tsayar da magana, Baba be yi komai ba sai da amincewata kamar yadda shari'a ta shar'anta. An saka lokacin auren saba ga watan Rajab wato watan azumin tsofi. A daren ranar na kasa ganin walwala a fuskar Namra, tun kan nai maganar kanenna suka fara cewa kishi take ni kuwa na san ba kishi ba ne domin har yau Namra bata san cewa mahaifinta ya sake ni ba ita dai tana ta ga ya daina zuwa kuma ba mu koma gidansa ba, tun daga wacan lokacin da ta min maganarsa bata sake min ba, Namra ma ina ta san wani saki   balle ta kawo wani abu a ranta ko da yake yaran yanzu wayo ne da su ba kamar mu ba.
  Ina daki ina fidda musu kayan bachi ta shigo ta kwanta saman katifar tana ta kallona kamar wata bakuwarta, ni kai na sai da kallon nata ya saka na tsargu duk kuwa da kasancewar karamar yarinya ce.

“Namra minene?”

Na tambaya ina dan murmushi da ban san ma ta ina ya samu hanyar fito min ba.

“Momy aure za ki yi?”

Na gyada mata kai ina karfafa ma kaina guiwa.

“Daddy fa?”

Na dan yi jimm kamin na amsa mata.

“Namra mun rabu da Daddynki shiyasa na dawo nan gidan na zauna, shiyasa Daddynku ya zo ranar yana fada yana cewa sai an ba shi ku”

“Ba za ki sake komawa gidan ba?”

Na gyada mata kai.

“Shi ma ba zai zo nan ba?”

Nan ma na gyada mata kai, sai ta ɓata fuska kan ka ce kwabo hawaye sun fara mata zuba, janyota nai a jikina na rumgumeta ina rarrashinta.

“Namra ai ba daina ganin Daddy za ku yi ba, za ku ganshi lokaci zuwa lokaci, ni kuma kuna nan tare da ni babu wata damuwa”

Kuka tai sosai kamar wacce akai wa bushara da mutuwar ubanta ko tawa mutuwar har wani shidewa take numfashinta na yin sama, ni kaina ban san lokacin da na fara hawayen ba. Daga ni har ita muka kwana kamar marasa lafiya, na kasa farinciki da auren Abdulhamid da zan yi kuma na rasa na rasa dalilin hakan.
   Washe garin ranar Abdallah ya sallamo gidanmu, a yawance ya shigo falon ya gaisa da Mama ya shiga ya gaishe da Baba sannan ya shigo dakin da na ke ya tsaya a bakin kofa yana kallona fuskarsa ba yabo ba fallasa. Ni kuma na kasa kallon inda yake ma balle har na bude baki nai masa magana.

“Am... Yaran nan ya maganar karatunsu?”

Sai a lokacin na dago na kalleshi kwarjininsa ya cika idona sai dai hakan be saka ni dauke kai ko janye idanuwa daga nasa ba.

“Na je Gwarzo ba su karbe su ba, wai sai da ubansu”

“To miyasa ba ki fada min ba? Yanzu idan ban yi magana ba haka za ki zuba musu ido karatunsu ya lalace?”

Sai na ji wani iri kamar ba ni ba, magana yake da ni kamar wanda be taba furta kalma so a gareni ba.

“Kin amince a akai su?”

Na dan kawar da idona daga kallonsa ina girgiza kai alamar ban amince ba.

“Haba Halimatu idan ba ki amince ba ya za ki yi? Ko Aminu za ki maidawa su ki ce ya saka su? Ya kamata ace idan za ki yi abu kina tunani gaskiya, ko da yake har yanzu akwai kurciya a take tare ke yaran ma ai mabiyi da mabiyi ne ba wani dogon tazara”

Sai na ji kamar magana ya fada min a cikin magana, ban yi aune ba na ji yana wata maganar da dariya a sautin muryarsa.

“Idan baki amince ba zan kai karar ki gurin Baba na ce kin hana asaka yara a makaranta”

“Abdallah zan saka su”

Na yi maganar a cikin muryar da ke karantar da mai saurarenta damuwata, sai yai min wani kallon tausayi yai min magana a hankali.

“Zan saka su Halimatu karki damu, karki min musu pls”

Ya roka kuma ya samu domin ban iya masa musun ba sai gyada masa kai da nai alamar na amince.

“Thank you”

Ya furta sannan ya fice daga dakin ni kuma na hade wani abu marar dadi da ban san ko minene ba na rumtse ido.
Chapter 26 · 0% Book details