← Book details Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 136

Sashe 36

Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“idan na bar wannan gidan auren Hajara ban san ina zan sake shiga ba, ban san wa zan fadawa ba, a can mi zan tarar, idan kuma na zauna zaman gaban iyaye ba dadi da shi ba ko ga budurwa balle a gurin mai yara kamar ni, bana son a fara kirga min aure Aminu ma idab ya samu labari ai zai ce gashi nan har aurena ya mutu tun ba a je ko'ina ba, zaman zawarci ba shi da dadi Hajara dan zaman da nai na iya sakin da Aminu yai min zuwa auren Abdulhamid ban jidadin ba ga natsatsin iyaye, ga lalurar yara tun da mahaifinsu babu ruwansa da su, bana son na fadawa Abdulhamid wannan abun ya sake ni saboda haka, idan ma har na samu cikin zubarwa zan yi a sirrance na cigaba da zama da mijina, ina jindadin Abdulhamid kuma ina son sa bana son shiga wata matsalar a yanzu, idan na fada masa ba lallai ne ya yarda ba, saboda ba ni da wata shaidar, wata kila ma ya zargi cewar na kasa tsare kaina ne na kasa hakuri shiyasa na aikata hakan yanzu kuma nai masa wannan karyar, tun da Allah ya rufe min asiri kara na rufewa kaina ko na samu salama”

Kai ta gyada min tana share hawayenta.

“Hakan yayi idan ma kin samu cikin ki zubar kawai mu rufe wannan sirrin, Allah ya dafa miki ya rufe mana asiri”

Jinginawa nai da kujerarta ina jin zuciyata na wani irin kona marar misaltuwa.
Hajara ta yi ta saka min maganganun na kwantar da hankali da karfafa guiwa a gareni har zuwa lokacin da Abdulhamid ya zo daukarta, ba ni kadai ba shi kansa na lura kamar baya cikin walwala sosai, ni da shi mukai shiru cikin motar kamar wasu kurame ni da abunda nake ta sakawa a zuciyata shi kuma yana ta tukinsa yana kallon titi.

Daf da za mu isa kiran Mama ya shigo wayata, ba tare da tunanin komai ba na danna picking na soma magana cikin muryar da ke karantar damuwarta ga mai saurarenta.

“Hello Mama”

“Halimatu Namra na gurin?”

“Aa tace aka kawo ta ne?”

“Aa mun dauka ko taba nan ne, Teema taje gidanki bata tararda kowa ba”

“Eh mun fita ne tun safe lafiya”

“Namra ce ba a gani ba tun jiya”

Kamar saukar aradu haka na ji maganar ban san lokacin da na ambaci sunan Ubangijina da karfi ba, wanda hakan yasa Abdulhamid kallona da sauri.

“Kamar ya ba a ganta ba? Ina ta shiga? Waya fita da ita?”

“Tare da Hafiza suka je biki wai Hafiza tace ta same ta bakin titi bata zo ba, kuma taje gidan bikin ta duba bata can sun jiya muke ta nemanta har makarantar anje bata can”

“Amman tun jiya Mama ba a fada min ba?”

Na tambaya idanuwa na kawo ruwa.

“Wallahi saboda tsoron kar hankalinki ya tashi ne yasa ba a fada ba”

Sauke wayar nai ina kuka ina jin wani irin tashin hankali na ratsa ni marar misaltuwa har gumi karyo min yake.

“Lafiya?”

“Namra ta bata”

“Subhanallahi garin ya?”

Ban iya ba shi amsa ba saboda kukan da ya ci karfina.

“Yi hakuri za a ganta In-Sha-Allah bari na sauke ki gida yanzu”

Ya fada yana miko min tissue.
7/21/21, 10:43 PM - Buhainat: *GOBE NA...*

By Khadeeja Candy

2️⃣0️⃣

DEDICATED THIS PAGE TO Mai Dambu, Allah kara miki lafiya Gwanata❤ son so Fisabilillahi💞😍

*** *** ***

Kamin mu isa gidan har wani jiri nake jin yana dibana, zuciyata kam kamar ta fashe ga wani uban zafi da kirjina ke yi, kaina sai sarawa yake.
   Ko parking din kirki be yi ba na bude motar na fita na shiga cikin gidan cikin tashin hankali kamar yadda su ma na tararda su cikin tashin hankali, gaba daya ban tarardar yan mata gidan mu ba da samarin biyun duk sun fita neman Namra Baba na tsakar gida rike da sandar damuwa kara a fuskarsa. A bakin balcony na zauna na dafe kaina. Inna na min bayanin yadda abun ya faru da guraren da aka je nemanta bata can. Mahaifinta ne ya fado min a rai.

“Ko Aminu ya dauke ta ba a sani ba?”

Na fada ina kallon Mama, a yayinda Abdulhamid ya shigo yana gaisawa da su.

“Mi zai saka Aminu ya dauke ta, mutumen da tun da ya bata baya be sake dawo ko tambayar lafiyarsu ba”

Cewar Inna sai Mama ta karba mata.

“Nima dai shi na gani, kuma a ina ma zai ganta?”

“Ko tana gidan Abdallah?”

Na fada ciki ina hawaye.

“A a bata can tun dazun da shi ake ta nemanta, shi ma yace kar a fada miki saboda kar hankalinki ya tashi, yanzu yanzu ma suka fita da Samira har.... ”

Baba ne ya tari numfashin Inna da ke maganar yana fadin.

“Ku ba Allah cigiya In-Sha-Allah za a ganta, idan ba dan sake irin na Hafiza ba taya zaka fita da yaro ka ce ya same ka titi bayan yaron be san gurin ba”

Komawa nai na zauna a gurin na fara rare musu kuka, idan ba kukan ba ban san abunda zan yi a yanzu ba.

“Bari naje na duba makarantarsu...”

Cewar Abdulhamid yana kokarin juyawa sai Inna tai karaf tace.

“Ai har can Abdallah ya tafi....”

Baba ya sake saurin tarar numfashinta.

“A a be je can ba, islamiyarsu dai yaje, zaka iya zuwa can ka duba”

Sai da Abdulhamid ya fice sannan Baba ya hau yi ma Inna fada wai ta cika tsoma baki a maganar da babu ruwanta. Ni kam sam ban ga illar maganarta ba kamar yadda ita ma kanta da Mama ba su ga haka ba, wata kila kuma akwai abunda Baba ya hango.

“Mama zan je gidansu Aminu na duba ko tana can”

“To da Abdulhamid din be wuce ba ai sai ya karaki”

“A a shi yaje can din ni zan duba gidansu Aminu”

Na bawa Mama amsar ina mikewa tsaye.

“Mi zai kaita can ma”

“Nema ne ai Mama”

Ban tsaya na jira su kara kashe min jiki ba na zari jakata na fito cikin gidan kamar wata mahaukaciya. Kamin mai napep din na kai ni gidan su iyayen Aminu har na matsu abunka da wanda je cikin tashin hankali. A bakin gate ya tsaya ni kuma na shiga cikin gidan da sallama. Kana gani na kasan hankalina ba a kwance yake, ba Hajiyar Aminu ba ko kanensa sun yi mamakin ganina a cikin gidan, ban musu magana ba kamar yadda suma suka saki ido suna kallona kamar wata bakuwarsu. Har cikin falon na shiga na gaishe ta ita ta amsa min da dan mamaki sannan na tambaya ko Namra tana nan.

“Namra da kuka kekashe kasa ke da yan'uwanki kuka ce ba za ku bayar ba, bayan kun gama ikirarin an bata ta mi za mu dauko ta tai mana? Ai mun yafe miki ita ki dafa ki ci ko ki saida babu abunda za mu da ita”

Mikewa nai tsaye cikin bacin rai na ce.

“Ke kika fi kowa abun yi da ita saboda jininki ce, kuma tambaya kawai na zo saboda idan tana nan na tafi da ita saboda kula da tarbiyar”

Mikewa tai tsaye ta nuna ni da yatsa.

“Ke Halima ki shiga hankalinki karki ce za ki so har cikin gidan nan ki min rashin kunya, ki bar ganin an kyale ki Wallahi kika min iskanci sai an karbe yaran nan daga hannunki”

“Da kuwa kin bude abunda yake rufe, da kin tona asirin danki dan sai duniya ta ji abunda ya aikatawa yar dan'uwansa”

Na bata amsa a fusace sannan na juya na fice na barta tana ta surutanta, inda na bar mai Napep din a nan na same shi.

“Kai ni igala quarters”

Na fada bayan an shiga Napep din, yana tafiya ina nuna masa inda za abi har ya sauke ni a kofar gidan Aminu, bayan Hajiya ban san ko tana gidan ba neman be ba a cire tsammani wata kila ma ya ganta a wani gurin ko kuma ita ta fadi can a kai ta ba tare da mun sani ba.
  Mai gadin yai na'am da ganina yana ta washe min hakora da tambayar yaushe gamo.

“Dan Allah Malam Garba tambaya nake ko kaga Namra a gidan nan?”

“Namra dai ta wajenki?”

“Ita, ta bata tun jiya”

“Subhanallahi Wallahi ban ganta ba, amman ki tambayi Alhaji ai yana ciki, Hajiyar ma tana ciki”

Fadar Hajiya ma tana nan ciki ya tabbatar da cewar Aminu yayi sabon aure kenan.

“Aa bana bukata na gode”

“Allah ya tsananta rabo”

“Amin”

Na amsa ina hawaye, ina shiga cikin napep din kuka ya kwace min.

“Hajiya Lafiya?”

“Yata ta bata tun jiya kuma ba a ganta ba... ”

“Subhanallahi a ina?”

“A gurin biki taje ita da kanwata”

“Aiko na ji ana cigiyar wata yarinya a fm dazun, amman ban sani ba ko ita ce”

Da sauri na kalleshi.

“Yaushe? A ina? Ya sunanta?”

“Wallahi ban rike sunanta ba amman dai dazun ina sauraren fm a napep na ji ana cigiyarta”

Ya karasa yana kunna fm din.

“Dan Allah ka taimaka ka kai ni can mu binka kasan inda fm din take?”

“Eh na sani Allah yasa ita ce”

Kamar nai tsuntsuwa na tashi na isa fm din haka naji, abun ka da guri mai nisa daga igala quarters zuwa Damba sai tafiyar ta zame min kamar ta wani gari, muna isa na fita na shiga ciki na fara tambayar mutane hankalina a tashe, sai wani ya shiga ciki ya duba takardun cigiyar ya rubuto mana number wayar da aka bada sannan ya fada min sunanta. Ina jin ya ambaci Namra wani dadi marar misaltuwa ya lullube ni.

“Sai kinje Samaru ki tambaya gidan Alhaji Muhamad Gwarzo”

“Na gode”

Tun kan ya gama magana na juya da sauri na fito na shiga napep din na fada masa unguwar da zai kai ni, a hanyar mu ta tafiya kiran Aminu ya shigo wayata, na gane ne numbersa ne saboda na haddace ba dan number tana da suna ba. Har na yi kamar ba zan dauka ba sai kuma wata zuciyar ta hana ni na danna picking na kara a kunne na.

“An ga Namra?”
Chapter 36 · 0% Book details