← Book details Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 136

Sashe 20

Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_na hana ki bayyana soyayyata saboda na san wannan ranar zata so wata kila na samu sauko ko akasin haka, kin ga yanzu da ban samu sauki ba babu wanda ya san mun yi soyayya da ke, da ace na samu sauki kuma da yanzu ne zan bayyana soyayyata, ki fahimce ni mana Haima Wallahi ina kaunar ki amman ba zan iya hana ki auren lafiyayyen miji ni na aureki, ba kuma zan hana ki auren kowa ki jira ni ba domin ban san lokacin samun lafiyata ba, kuma iyayenki a yanzu ma sun damu su aurar da ke, Allah ya riga ya rubuto ba zan aureki ba...._

Duk wani magana da Hajiya ke yi be ji ko daya ba saboda ya lula a duniyar tunanin abunda ya faru tsakaninsa da tsohuwar soyayyiyarsa yana murza zoben da ta saka saka mata da kansa a wani lokaci can baya.

“Hassan....”

Da sauri ya dago ya kalli Hajiya domin ya ji kiran kamar daga wata duniyar.

“Na'am Hajiya?”

“Ba ka ji abunda na ce ba ne?”

“Na ji.... Na ji.. Na ce eh ba ki ji ba ne?”

“Saboda me?”

“Haka nan kawai”

“Haka nan kawai sai ka ki zuwa aiki? Abun ya fara taba har da aikinka ne?”

Sai a lokacin ya fahimci abunda Hajiya take magana akai domin a dazun amsa mata kawai yake ba tare da yaji abunda take fada ba. Mikewa yai tsaye yana murmushi.

“Zan je aiki mana Hajiya, ban fahimta ba ne sai yanzu”

“To Allah ya tsare yai muku albarka”

“Amin Hajiya sai na dawo”

Ya fito yana jin cewar a yanzu ne ya dace ya nemi magani ko dan Halimatu, idan ma bar warke ba zai aureta a hakan matukar a yanzun zata aminta domin yana jin cewar shi kadai mutumen da zai iya yarda ya aureta da yaya a yanzu kuma ya mantar da ita komai.

HALIMATU POV.

Wani abunda ya bani mamaki rashin samun abun hawa tun daga kan babura har napep duk wanda na tara ba ya tsayawa. Abun har mamaki ya bani na rika shafa kaina ina lalabawa wai ko basa ganin nane amman sai na jini a mutum kuma ai ina ganin mutane an kallona sai dai tsayawa su dauke ni ne basa yi. Tun ina tsaye ina taro har ta kai ga na fara takawa ina bin gefen titi, da na gaji da tafiyar sai na samu guri na hutu, na sake cigaba da tafiya sai yamma lis na isa gida ban taba jin gajiya irin ta yau ba damin ban taba shan wahalar tafiya kamar yau ba. Na tararda kowa da kowa na tsakar gida kamar yadda aka saba yin shimfida a harabar gidan a zauna ana ta fira da dare dare. Suna ta min sannu da zuwa ni dai ban bi ta kansu ba na wuce zuwa falon Mama sai na samu Abdallah a zaune yana game da wayarsa Namra na gefensa tare da Aiman da Adnan sun zagaye shi Amal kuma na saman cinyarsa tana kallon wayar, tsayawa nai ina kallonsa shi ma ya dago ya kalleni fuskarsa ba yabo ba fallasa.

“Sannu da tafiya”

Sannan ya mike tsaye yana gyara rigar shaddar da ke jikinsa.

“Kin ce na dawo miki da yaranki ko? To ga su nan sai ki saka su makarantar ai”

Yana fadar hakan ya raba gefena ya wuce ni kuma na bishi da kallon takaici da mamakin karfi hali irin nasa, yara dai nawa ne kuma na zabi na saka su da kaina to ina ruwansa, tun ba yau ba Abdallah na da son shiga rayuwata tun igiyoyin aure suna kaina ina yawan nuna masa bana so amman baya fasawa. Ba wai bana son ya saka su karantar ba ne canja musu makaranta abu ne mai kyau wanda ni ma nai tunanin hakan sai dai bana son yadda yake son shige min ne da yawa, har ga Allah bana jin zan iya karbar wani tayi daga gurin Abdallah na so, taya zan so mutunen da na kaunace dan'uwansa kamar na mutu, mutumen da be san darajar aure ba kuma mutumen da be taba martaba ni saboda ina da igiyar aure ba, mutumen da a kullum fatar mutuwar aure yake min.
  Adnan na aika a shago ya siyo min suga da madara da biredi na hada tea mai sanyi na sha, domin yau ban saka komai a cikina ba sai ruwa, a lokacin da zan fita ban ci komai ba ga shi na ci tafiya a kafa kamar marar galihu. Na yi sa'a bana sallah hakan kuma ba karamin dadi yai min ba, domin yau ko ta kan Amal ban bi na hau kafita na fara sheka bachi kamar wacce ta shekara batai bachi ba.
Ban farka ba sai 11pm a lokacin wasu sisters nawa sun yi bachi su kan yara ba a maganarsu daman can abu ne mai wahala su wuce 10 ba su yu bachi ba ko lokacin da muke gida suna ganin game balle nan da babu. Wani irin ciwon kafafuwa ne ya taso min kamar wata tsohuwa da kaina na zauna ina matsa abu saboda azaba. Na yi minti talatin a haka sannan na tashi na shiga bandaki na tsaftace kaina na canja pad na fito na nufi dakin Mama.
   Na same ta tana hamma kamar dai ni da bachin be wadatar da ni ba, kusa da ita na zauna ina amsa mata cewar lafiya kalau gajiya ce kawai ta saka ni bachi.

“Ya jikin abokin aikin na ki?”

“Jiki ba dadi Mama ance ma wai jini zai iya taba kansa ni abun ya bani tsoro sosai, amman matarsa sai ci min mutunci take”

“Akan me? Miye hadinki da matarsa?”

Na jera mata komai kamar a gabanta ya faru, sosa abun ya bata mata rai har take yabon matar da rashin kunya da kuma tunani, mun dan dauki lokaci muna tattaunawa maganar kamin na soma mata shimfida da zancen Sadi.

“Wai Halimatu ba zaki share maganar nan ba? Yanzu fa aurenki ne ya mutu kin dawo cikin kenanki kin zauna su ma muna fatar rabuwa da su ke kin dawo maimakon ki fara tunanin yadda Goben ki zata kasance ki samu mijin aure shine kike neman batawa yarki da kanki suna? Ke yanzu kina ganin wani ma idan ya ji kina da yara hudu zai aure ki ne? Ai ba kowa ke son mace mai yaya ba ma, sannan wani ko ya so ki ba zai yarda ke je masa da yaya ba”

Kallo mamaki nai mata.

“Mama yaushe aurena ya mutu ma balle har ace wani ya zo nemana? Kuma ni yanzu ai ban shirya ma aure ba”

“Baki shirya ma aure ba? Kika magana kamar ba yar musulmi ba? Ke yanzu ko dan ki bawa Aminu haushi ai kyayi aure da wuri, sannan ga kanenki nan suma neman rabuwa na ke su ke kuma kin dawo har ki fara tunanin zama? Halimatu kina da tunani kuwa?”

Babu juyin duniyar nan da ban yi ba dan na fahimtar da ita irin matsalar da na fuskanta a gidan Aminu wanda ya saka aure ya fita a raina amman ta kasa fahimta, idan na dauko zancen kotu kuma sai ta tare ta nuna min ba haka har na gaji na taso na baro mata dakin. As usual na farka raina babu dadi babu walwalah daman na saba tashi a haka tun ina gida Aminu balle kuma yanzu da abubuwan suka kara min yawa.
Kudina na saka na siyo ma yarana koko da kosai na basu suka sha suka koshi, na san ba za su iya jiran na gida ba domin sun saba da cin abinci da wuri, balle kuma abincin gida na taru ba ba lallai ayi musu yadda zai wadatar da su ba. Bayan na gama da su na aika aka siyo min madara da biredi na hada tea ina sha. Wayata da ke gefena ce tai kara alamar sako tun daga saman screen din wayar na karanta da sakon tare da sunan mallakin sakin.

“Good Morning.”

Dauke kai nai ganin Abdallah na dauka ma ko zai yi zuciya ya kyaleni ashe ba shi da zuciyar ma, ina jin lokacin da wayar ta koma ringing na ki kulawa saboda bana bukatar kallon mai kiran ba, abunda ban sani ba ashe kawata ce Hajara take kirana ba Abdallah ba, ankarowa da hakan yasa nai saurin picking.

“Hello Hajara”

“Na'am Halimatu ya gida ya aiki? Ko baki kusa da wayar ne?”

“Eh ina breakfast ne ya yaran?”

“Lafiya kalau ga ni kofar gidanku ki fito mu gaisa”

Mamaki ne ya kamani.

“Kofar gida kuma? Miyasa ba za ki shigo ba?”

“Ke dai ki fito kawai”

Mamaki ne ya kamani ba dan kankane ba, taya Hajara zata so har gidanmu bata shigo ba tace wai na fito mu gaisa?
Wata kila wata maganar ce mai muhimmanci ita ce amsar da zuciyata ta bani a take na bar cin abincin da na ke na dauka hijabina na saka Amal ta biyo bayan muka fita tare. A bakin kofar gidan mu na yi arba da motar Isma'il sai dai ban kawo komai a raina ba a zatona ko tana cikin motar ne, haka ne yasa na karasa ya buga kofar gilashin motarta. Saukar gilashin motar sai yai min almara mijin Hajara ne kadai a motar ba tare da ita ba, mamaki ya hanani cewa komai sai sakar masa ido yai, shi kuma yana ta faman zuba min murmushi kamar auduga, bude motar yai ya fito yana ta kara min murmushi da haurensa na makka fari.

“Hajara tace min na fito tana kofar gida”

“Eh haka ne, amman dai ya kamata mu kamin a dora da bayani ko”

“Ba da kai ba da ita”

Na maimaita masa saboda ya fahimta amman sai ya kara dilmiyar da ni.

“Da ni zaki gaisa ba da ita ba”

Ya fada Yan mikawa Amal hannu ta zo sai tai bayana ta boya kamar wacce bata san shi ba.

“Ina fatar kina lafiya”

Nauyi baki na yi na kasa ce masa komai har ya sake jefo min wata tambayar.

“Ya gida ya yaran?”

“Lafiya Kalau”

Na juya da sauri sai ya kira ni.

“Halimatu... ”
Chapter 20 · 0% Book details