← Book details Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 136

Sashe 68

Gobe Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya fada yana fashewa da kuka kamar mace har zaman kujerar ya gagare shi sai da ya sauko kasa. Sai a yanzu yake jin wani irin zafi da bakincikin abunda Sadi yai ma yarsa da kuma matarsa ashe akwai zafi wani ya kusanci matarka, sai yanzu yasan zafin da uba yake ji idan aka lalata masa Y'a.

“Aminu ka fada min abunda yake faruwa mana, ka gada min hankali”

“Hajiya yau an kore ni gurin aiki... Amman bashi ya fi bata min rai kamar kama Sadi da nai da Matata Murja.... ”

Idan akwai abunda yafi sakin baki da mamaki sai da Hajiya ta yi shi.

“Kasan me kake fada kuwa Aminu?....”

A nan labarta mata komai idonsa ko gani basa yi daidai saboda hawaye. A take Hajiya ta saka kuka.

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, yanzu Sadi da matarsa da yaransa zai yi matar dan'uwansa haka?”

“Hajiya kin tuna lokacin da na saki Halimatu saboda ta fada min Sadi yai ma Namra fyade? Daga ni har ke ba mu tsaya mun yi tunani ba....”

Hajiya ta dafe zuciyarta tana hawaye.

“Indai har haka ne Sadi ba zai gama lafiya ba, wane irin da na haifa?”

A wunin ranar daga Hajiya har Aminu wuni sukai cikin jimami da damuwa, sai da Dare Sadi ya shigo gidan shi ma dan Hajiya ta kira shi ne, har lokacin ba shi da natsuwa da kwanciyar hankali, Hajiya ta rufe da fada tana kuka, amman sai kokarin kare kansa yake.

“Hajiya Wallahi Aljanunta ne suka gaso kuma tana fisge fisge shiyasa na kaita daki na kwantar da ita”

“Kaji tsiron Allah Sadi idan babu duniya akwai kiyamar Allah, wace irin lalacewa ace kana tare da matar aure mai auren ma matar yayanka? Bayan kai ma kanka kana da aure da yara? Ko ka amsa ka aikata ko kar amsa wannan maganar zata tsaya a tsakaninmu daga ni sai kai sai Aminu, ba zamu fitar da wannan sirrin ba”

Duk wani abu da Hajiya ke fada, Aminu dai be ce uffan ba, kansa n kasa har sai da Sadi zai tashi sannan ya dago ya kalleshi.

“Tun yaushe kuke tare?”

Jimmmmm yai kamar ba zai amsa ba, sai kuma ya ce.

“Tun kamin ka aureta, class mate dita ce”

“Allah yai maka yadda kai min”

Ya fada masa sannan ya mike ya fice daga dakin ya bar su daga Sadi sai Hajiya.

HALIMATU POV.

Tsawon wata uku kenan ban sake saka Abdallah a ido na ba, hakan kuma ba karamin saka ni yai a damuwa ba, na rubuta masa sakon karta kwana na bashi hakuri amman be maido min da amsa ba, na kira wayarsa several times be yi picking ba.
Ba zan iya zuwa gidansa saboda na bashi hakurin abunda ya faru ba, sai dai ban abunda zan masa da zai saka ya sauko daga fushin da yake da ni ba, a iya zamana da Abdallah be taba fushi da ni na tsawon lokaci haka ba, ko da ban bashi hakuri ba yana saukowa da kansa balle har na bashi hakuri. Da kaina na zauna ina ta tunani da tariyo abunda ya faru so nake na gane idan maganar da na fada masa mai zafi ce sosai da har zata saka ya gujeni haka.

Amman kuma ai na huta da shi, ni da nake neman maraba ma? Dan ya nesance ni a yanzu ai na huta ko? Wata zuciyar ta aika min da tambaya, a maimakon na jidadi sai na ji akasin hakan, wata kila saboda na dan saba da shi ne shiyasa na ji babu dadi a yanzu, wata kila kuma saboda abunda na fada masa ne yasa nake jin babu dadi, haka dai nake ta sake sake na ni kadai na kulla wannan na wance wacan.
   Yau ma after na shiryawa yarana sun tafi school na shirya na fito da zimmar leka gidan kawata Hajara wacce na dade ban ziyarce ba, a yau can nake son zuwa yau so nake ba bude nata cikina ina son na ji irin shawarar da zata ba ni ina son na ji yadda zata kalli abun.
Na yi kyau matuka ni kaina na san na yi kyau domin bakar abaya ce a jikina wacce take yi ma ko wace mace kyau, gashi na tsirka da jan mayafi, sam ba zaka gan ni kace Halimatu bace domin na rame sosai ni kaina ina ji a jikina domin yanzu bana jin nauyin jikin kamar da kusan dukan tufafina sun min yawa. Napep na tara na shiga na fada masa inda zai kaini ina cikin napep din ina tunani ban san mun isa unguwar ba har sai da mai napep din ya tambayi inda zai sauke ni.

“Idan ka dan kara gaba kadan ya isa”

Na fada masa ina kallon wata motar da nake kyautata zaton mu take bibiya, ko na nace ni domin tun daga lokacin da nai arba da wannan mutumen ba kasafai bake fita ban ga mota tana bibiyata ba, kuma ba kalar mota daya ba, wani lokacin zai sauke gilashin motar ya kalleni amman ba zai ce min uffan ba, wani lokacin kuma ta cikin motar yake bibiyata, tun abun na bani tsoro har na fara sabawa, ban san mi yake nema a gareni ba, a iya sanina ban yi ma kowa komai ba balle ace wani ya saka ni a gaba dan ya cutar da ni. Bayan na biya nai napep din na tura gate din gidan na shiga sai da muka gaisa da mai gadin sannan na nufi cikin gidan.
  Na jidadin tararda ita ba tare da kowa ba, domin ko mijinta ya fita aiki balle kuma yara da sun tafi school. Tana ganina ta washe hakora

“Yau garinmu inji maki baki”

Da dariya na zauna saman cushion muka gaisa sai ta tashi ta hado min abun karyawa, ban musa ba na karba daman da safen nan koko kawai na sha, sai da na ji na koshi sannan muka dauko labaran duniya har take min zancen komawa makaranta na cigaba da karatuna.

“Ni yanzu ba wani karatu dake gabana, karatun da nai ya isheni aikin nake son samu, na dogara da kaina iyeyena ma suna bukatar taimako na ga yara a gabana ga kanena ga ni ni kaina, kuma kin san karatu dole sai da wanda ya tsaya maka...”

Ya janyo fillon kujera ta rumgume tana kallona.

“Zan tsaya miki ki yi karatu Halimatu, ko nawa ake kashewa zan kashe miki so nake ki yi karatu ki kai matakin da ko aiki zaki samu ba karami zaki samu ba sai babba wanda zai zama na har wasu ma'aikatan a karkashinki suke, ya zamana kina iya daukar nauyin yan'uwanki da ke kanki da iyayenki da kuma yaranki”

“Thanks for the opportunity amman har ga Allah a yanzu bana sha'awar karatu bana jin ma kwakwalwata zata iya daukar wani abu a yanzu”

“To aure kike so?”

“Bana da kudirin aure a yanzu Hajara, kin fi kowa sanin irin kalubalen da nake fuskanta a rayuwar aure, kwata kwata Yanzu aure baya burgeni, aiki dai nake son samu saboda na dogara da kaina domin bana da mai taimaka min a yanzu, Abdallah da nakr ganin yana dauke min wani nauyi shima ya fara guduna”

Fuskar mamaki tai

“Kamar ya?”

Ban rage ba ban kara ba daga abunda ya faru tsakanina da shi wanda nake ganin shine silar fushin da yake da ni.

“A gaskiya baki kyauta ba, amman shi kuma ya dauka da zafi”

“Na san ban kyauta ba, tun daga lokacin abun ke ta damuna har yanzu na ta masa sako na ta kiranshi amman be daga ba be kuma maido min da amsa ba, Wallahi abun yana da damuna”

Na fada idanuwa na taf da hawaye.

“Kina son Abdallah Halimatu....”

Wani kallo na watsa mata a kaikaice.

“Ko ki yarda ko karki yarda son Abdallah kike Halimatu kuma kin yi kuskure tun farko da kika auri Abdulhamid bayan kin san Abdallah yana sonki ga kuma tarin kyautatawar da yai ta miki, yanzu gashi zaki cutar da kanki”

“No ba ki gane ba ne, ba son Abdallah nake ba”

“To miyasa kike kuka saboda ya kaurace miki?”

Na kai hannu na share hawayen da suka zubo min.

“Ai ya kyautata min da yawa ko? So ya kamata na ji babu dadi idan ya kwaurace min ko?”

“Hakan be isa ya saki a damuwa ba, akwai son Abdallah a rayuwarki wata kila ba ki sani ba, wata kila kuma kina boyewa ne kawai, so abunda nake ganin yafi kije kai tsaye ki same ni a gidansa ai ba zai kyale ki a can ba, ki bashi hakuri idan ki kai hakan kin wanke kanki”

“Kina ganin idan naje matarsa ba zata zargi wani abu ba?”

“Ke fa jininsa ce Halimatu, taya matarsa zata yanke alakarku? Ke wai ni yar a manta ma ban fada miki ba kinji Aminu ya saki matarsa?”

“Haka Asma'u makociyata take fada min a chat, ko me hada su kuma?”

Hajara ta tabe baki.

“Me zai hada su kuwa ban da bakin halinsa, wace macen ce zata dauki abunda kike dauka? Ai babu macen da zata iya zama da Aminu”

Na yi murmushi ina tuna lokacin da yake ce min wai babu namijin da zai iya zama da ni sai shi saboda bakin halina da sa'idon da nake masa.

“Wata kila shiyasa ya fara munafurci, kin ga yadda yake kula da yaran nan a yanzu kamar ya lashe su? Wallahi idan ya gan ni har wani sunsun da kai yake kamar mazuru”

“To ko so yake ya dawo dai.... ”

Na tofar da yawun bakin.

“Allah ya kiyaye haba Hajara ai dai kya min fatar kwarai ko? Wallahi ni yanzu ko a kafa aka daura min Aminu ba zam iya jansa ba, ke idan na ganshi har wani tashin zuciya nake ji”

Na fada ina yatsina fuska sai Hajara ta saka dariya.

“Balle ya ga kin yi slim kin yi kyau abunki Ma-sha-Allah”
Chapter 68 · 0% Book details